Wasu Sana'o'in Da Zaka Iya Yinsu A Lokacin Da Kake Karatu A Jami'a:




Tabbas duk wanda ya fito daga gidan iyaye marasa karfin wadata kuma yake karatu yasan wahalar karatu koda kuwa ta furamari ce. Bare kuma ace matakin karatu na sakandari, Koleji ko Jami'a 
'Ya'yan marasa karfin arziki da dama suna kasa ci gaba da karatu bayan sun kai wani matsayi a karatun nasu saboda matsaloli irin na kudi.

Ga wasu aiyuka da sana'o'in da ɗalibai zasu iya aiwatar dasu a lokacin da suke yin karatunsu musammanma masu karatu a Jami'a. Idan aka yi sa'a Allah Ya dafa a wannan abun neman kudin, ɗalibi zai yi karatunsa cikin sauƙi ba tare da wahala ba.

#1 AIKIN KOYARWA: A lokacin da kake karatun jami'a zaka iya samun wasu ɗalibai kana koyar dasu darasin daka ƙwarai akai.
Akwai iyayen da suke so a rika koyar da yaransu a gida bayan sun dawo daga makaranta. Ana kuma samun wasu ɗaliban sakandare da suke bukatar a rika musu darusa na musamman bayan sun tashi daga makaranta saboda wani jarabawan dake gabansu. Irin waɗannan cikin sauki ɗalibi zai rika karantar dasu yana samun 'yan kuɗaɗe.

#2. TACE RUBUTU (Editing and Proofreading)
Wannan aiki ne da ƙafafen yaɗa labarai da dama suke buƙata. Wasu kuma jami'ai ne na gwamnati da suke rubuce rubucen da suke bukatar tace su kamin a gurzasu. Nan ma hanyace ta samu kuɗin shiga a lokacin da ɗalibi yake karatu.

#3; NEMAWA DALIBAI MUHALLI: zaka haɗa hannu ne da dillalan da suke dillancin bada gidajen. Ka samu na unguwar da kasan ɗaliban sunfi sha'awar zama. Duk lokacin da ɗalibai suka tashi neman wajen zama kai zasu nema ka samamusu su biyaka kamishonka.
#4. WANKI DA GUGA: shi ma aiki ne da zai tallafamaka a lokacin da kake karatu.

Zaka samomu yaran da su zasu riƙa yi maka wankin suna gogewa kai kuma kana karɓo aikin wajen masu bukatan bayarwa a musu.
#5. GYARAN JIKI: wannan aikine daya dace da mata ɗalibai.
Zaki iya yin kitso, gyaran gashi. Da kuma aikin farata da ƙafafuwa.
 Allah Ya a amfana da abunda aka karanto ko ake karanta.

#Malam Tonga
#sirrinrikemiji 

Post a Comment

0 Comments