TAƘAITACCEN TSOKACI GAME DA BATUN FALASƊIN (1)


WAIWAYE ADON TAFIYA (14)



Yahudawa al'ummace mai dogon tarihi, sabo da gudun tsawaitawa za mu farane daga abunda ya kama daga ƙarni na 19 zuwa wannan ƙarnin. Mai son samun tarihin abubuwan da suka wakana kafin nan a sauƙaƙe zai iya neman tafsirin Suratul Isara'i na Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo.

Duk da cewa ƙsashen turai sun rungumi tsarin secularism amma hakan ba tasa yahudawa sun samu saukin tsana da hantarar da suke fuskanta ba wanda hakan ya samo asali daga mugayen ɗaɓi'unsu na sharri na son kai da jin cewa sun fi kowa. sakamakon hakan ne aka samu wasu daga cikin yahudawa wanda suka fara tinanin lallai yakamata su samu ƙasarsu ta kansu da za su tattaru anan a sabo da hakane aka shiga binciken ƙasar da ta dace su.

An bijiro da ƙasashe da dama wanda ake ganin za su dace da zama ƙasar yahudawa kamar su Argentina, Uganda, Bahrain da yankin Ahsa'(gabashin Saudiya), yankin Sina dake ƙasar Masar (Egypt) wanda ƙarshe tinanin falasɗin ya fi zama mafi ƙarfi da karɓuwa.

A ƙoƙarin aiwatar da wannan ƙudurin na samarwa da yahudawa ƙasa ta kansu Theodor Herzl wanda ɗan jaridane bayahuden ƙasar Hungary ya kafa ƙungiyar Zionism a shekarar 1897 wanda aikinta shine samarwa da yahudawa matsuguni a Falasɗin . A koƙarin aiwatar da hakan har khalifa sultan Abdulhamid na biyu ya samu yana mai ta yi mai gwaɓi na maɗuɗan kudaɗe akan ya amince ya siyar musu ko ya basu hayar wani sashi na falasɗin, in da nan take Abdulhamid ɗin ya ƙi amincewa ya nuna mai cewa ƙasar ta dukkanin musulmai ce kuma yahudawa ba za su taɓa samun matsuguni ba anan matuƙar yana kan matsayinsa, kusan zamu iya cewa ba don rawar da Herzl ya taka ba da yanzu yahudawa suna gararamba a sassa na duniya.

*Ga videon haɗuwar Herzl da Sultan Abdulhamid
 https://youtu.be/01T3GHDVWtwda

Biyo bayan hawan-naƙi da Abdulhamid ya nuna ƙungiyar Zionism da kuma yan Free Mason suka ga cewa lallai sai an kawar da shi kafin nan za iya cimma manufar da ake so, hakan kuma aka yi a sanadiyyar falasɗin Abdulhamid ya rasa kujerarsa yama zama shine khalifan ƙarshe mai cikakken iko a daular Usmaniyya a shekarar 1909

Bayan kawar da sultan Abdulhamid yahudawa suka fara yo hijara zuwa Falasɗin a hankali a hankali suna kama wuri suna zama wasu kuma suna siyan wurare suna kafa kauyuka a haka lamarin ya kasance har zuwa yaƙin duniya na ɗaya a 1914

San da yaƙin duniyan na ɗaya ya kaure wanda Ingila da Faransa da Russia suka fuskanci daular Usmaniyya da
Germany da Austria, a wannan lokacin an samu yarjejeniyar yanka ƙasashen daular usmaniyya da rabesu tsakanin Faransa da Ingila wato yarjejeniyar Sykes-Picot wanda Falasɗin ta faɗo a cikin kason Ingila, birnin ƙuds kuma akace zai kasance ƙarƙashin kulawar duniya (su kenan).

A ƙoƙarin neman gudunmawa ta ƙudi da agaji a wannan yaƙi da take yi yasa Ingila ta bakin minstan harkokin wajenta Arthur Belfour ya yiwa yahudawa alƙawarin kafa musu ƙasarsu ta kansu a Falasɗin wanda hakan tasa manyan attajira da masu kuɗin yahudawa suka tallafawa ƙasar Ingila sosai domin samun nasara a ƙarshe dai hakan ta kasance a 1917 Ingila ta ci nasarar mamaye Falasɗin tare da taimakon wasu larabawa wanda Sharif Husain(Kakan sarakunan Jordan) yake jagoranta da suka haɗe da turawan a yaƙinsu da daular Usmaniyya a bisa alkawarin cewa za a kafa musu daularsu kuma shi Sharif Husain ɗin shine zai zama khalifa bayan ruguje daular Usmaniyya ɗin.

Mecece maslahar turawa wajen samarwa da yahudawa ƙasa ta ƙashin kansu? 

Dalilai biyune:

 Dalili na siyasa shine kasancewar yahudawa sun addabi turawa ɗin a can ƙashensu don haka samarmusu da ƙasarsu zai sa suma su huta da sharrinsu da fitanarsu, sannan a lokaci guda kuma sanya yahudawan a wannan yanki dake tsakiyar musulmai zai shagaltar da musulman kan batun turawan don haka a rikici da rigima da yahudawa za su ƙare ba zama su samu sukunin sake haɗewa ba harma su sake tunkarar turawar kamar yadda haka ta sha faruwa a tarihi matukar an dasa musu fitina a cikinsu.

Dalili na addini kuma shine mazahbar Protestant wanda Ingila da America take kai, suna da kyakkyawar alaƙa da yahudawa,domin a ganinnsu Annabi Isa ya zo duniyane a bayahude, kusan irin kallon da muslmai suke yiwa larabawa na girmamawa da mutuntuntawa kasancewar Annabi Saw balarabene irinsa Protestants suke yiwa yahudawa, kuma suna da aƙidar cewa Almasihunsu ba zai sakko ba dole sai yahudawa sun taru a Falasɗin a wannan lokacin ne zai sakko ya jagoranci yaƙin Armagiddon wanda daga shi sai tashin alƙiyama, wannance tasa ake kiran ƴan mazhabar Protestants da Christian Zionism, don a wurinsu tarewar yahudawa a Falasɗin aƙidace da dole a tabbatar da ita.

A rubutu na gaba insha Allah za mu ga abubuwan da suka wakana har yahudawan suka yi nasarar kafa isra'ila.

* Wannan hoton Theodor Herzl ne wanda ya assasa Zionism.

#Tarihinmu_madubinmu

Post a Comment

0 Comments