Daga Sameerah Bello Shinco.
Farkon abin da mafi yawancin matasa keyi idan sun farka daga barci shi ne daukar waya domin duba sakonnin daga masoyansu, ko kuma duba sanarwa, labarai da sauransu ta hanyar yanar gizo-gizo ko dandalin sada zumunta wato social media. Kafin mutum ya ankara ya cinye awoyi marasa adadi a Social Media.
Kafafen Sadarwa na zamani (Social Media) Sun zame mana Jiki a rayuwarmu ta yau da kullum, Kamar dai misalin Mashayi da Kayan Shaye-Shaye; Idan bai sha ba to kuwa babu nutsuwa da Zaman Lafiya. Sabbin kafafen sadarwar na zamani sun zame mana jiki a rayuwarmu ta yau da kullum: Har ma ya kasance jama’a ba su cika kallonka a matsayin wayayye wanda ya san mai ya ke yi ba idan har ya kasance ba ka amfani da daya daga cikin shafukan sadarwar na zamanin. Duba da yanda kowane rukuni na mutane su na amfani da shi(Social Media), tun daga kan maza har zuwa mata, yara, matasa, attajirai, ‘yan siyasa, malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa da sauran sassan jama’a. Kai har ma kamfanoni da ma’aikatu sun kasance suna amfani da (Social Media) wajen tallata hajojinsu ko ayukansu ga al’ummar Duniya.
Bincike ya nuna akwai abubuwa da dama wadanda (Social Media) ta haifar a cikin al’umma, amma wannan rubutu zai yi tsokaci ne kan yadda (Social Media) ta yi tasiri a rayuwar matasa, ma’ana ta ya ya (Social Media) ta taba rayuwar matasa?
AMFANIN DA SOCIAL MEDIA TA KAWO WA MATASA:
Social media ta hada duniya wuri guda ta zama wani dan karamin gari wanda ake kira global village a Turance: ko kuma a ce duniya a tafin hannunka a hausance.
Ta dalilin social media; a yau matasa suna haduwa su tattauna da juna daga bangarori daban-daban na duniya.
Ta hanyar social media matasa suna musayar ra’ayi da tafka muhawara a junansu, sannan kuma su na samun bayanai da labarai da kuma samun dumbin damammaki dabam-daban.
Social Media ta ba wa matasa damar yin sababin abokai, haka zalika ta bada damar matasa gano tsofafin abokansu wadanda a baya su ka yi gwagwarmayar karatu tare ta hanyar ganin sunayensu ko sunayen makarantar da su ka yi.
Social Media ta taimakawa matasa masu saye da sayarwa in da su ke bude shafuka na musamman domin tallata abubuwan da su ke sayarwa ko kuma su biya matasa wadanda su ka yi suna su tallata musu hajojin nasu su kuma su biya ladan tallatar da su ka yi musu.
Sannan Social Media ta na bawa matasa damar hada kai da zama jaikadu kan harkokin kasuwanci da ayyukan jama’a.
Haka zalika, Social Media tana samarwa matasa kudi ta hanyar Blogging da ayyukan watsa labarai da harkokin tallace-tallace da sauran ayyukan fasaha.
Sannan kuma (Social Media), wurare ne da matasa su ke amfani da shi wajen bayyana ra’ayinsu da sanar da duniya tunaninsu cikin sauki ba tare da wata shakka ko fargaba ba.
Haka zalika Social Media ta ba da dama ta yadda a sanadiyyarta za ka iya yin aiki a ko’ina ka ke a fadin Duniya.
ILLOLIN DA SOCIAL MEDIA TA KAWO A RAYUWAR MATASA:
LALATA TUNANIN MATASA: Babu wuraren da suka kai social media lalata tunanin matasa musamman mata. Domin zaka dinga ganin rayuwar mutane kala-kala kuma daban-daban. Mutum zai hadu da wanda suka fi shi, da wanda suke dai-dai da wanda ya fi su. A maimakon matashi yayi hakuri da yanda yake, da yawansu su kan kasa jurewa, suna ganin dole sai sun yi koyi da wane da irin rayuwarsa. Da yawan matasa suna mutukar daurawa kansu irin wannan fitinar rayuwar na cewa sai sun samu irin abun da wasu ke samu.
‘YANCIN MAGANA: matasa da yawa Suna ganin yanzu sun kai su yi kafada-da- kafaɗa da kowane mutum a cikin rubutunsu a social media. Sai ka ga matashi ya kira sunan wani mutum mai ƙkima da mutunci a al’umma, babu kunya babu tsoron Allah ya zage shi, ko ya yayi masa muguwar addu’a. A duk zage-zagen da ake yi a social media babu wanda ya fi ɗdaga hankali irin zagin Malamai. Ka ga wani jahili wanda ko karatun sallah bai iya da kyau bam, yana tsinewa ko muhawara da baban malamin da ya fisa sani a addini. Wani kuma ko brighter grammer bai taba karantawa ba yana tsinewa profesa. Kawai laifinsa shine ya rubuta abun da ya sha banban da aƙidarka kona malaminka haka nan ra’ayinka ko na malamanka.
ƘARYA DA RIYA: social media ta yi sanadiyyar lalacewar aikin matasa da yawa. Domin a halin da ake ciki duk abun da mutum yayi na ibada zaka ga sai ya saka shi a social media yana fadawa duniya cewa ai shi mai kaza ne ko yana yin kaza. Akwai wadanda ko sallan dare suka tashi sai a dauki hoton an yi posting. Da yawansu ko sadaka suka bada ko wani aikin ladan da ma ba sai duniya ta sani ba to sai sun sanar. Har ya kai ga wasu suna ganin idan suka yi wani aikin alkhairi ko na neman yardan Allah in basu yi posting ba basa jin kamar sun yi aikin.
HASSADA DA KYASHI: A social media daya daga cikin abun da yake saka matasa faďa, gaba, bincike, gulma, kiyayya, da hassada ga juna shine kwaikwayon wani a cikin abun da yake yi. Wurin kokarin son ganin ka kamo wata ko wani; sai kamayar da kan ka sauna ko sakarai. Domin idan kana kwaikwayon wani a komai nasa; hakan yana nuna tabbas baka cika mutum mai iya tsayawa da kafafuwan sa ba. Kuma baka godewa ubangiji taka baiwar daya maka ba. Saboda duk yanda kake raina kanka akwai abun da Allah Ya yi maka mai muhimmanci. Amma kallon na wani, da son kwaikwayon sa, da kokarin kamosa shi zai hana ka fahimtar irin taka baiwar. Wata kila kwata-kwata kyautar ka ba a cikin irin abun da kake ta kwaikwayon wancan bane. Amma saboda yana burge ka sai ka yi damarar kwaikwayon komai nasa. Daga Karshe idan ka kasa kamosa, ko zama kamar shi, sai abun ya koma HASSADA. Sai ka rika jin haushin sa bai maka laifin komai ba, ko digo ya rubuta sai ka zage sa.
0 Comments