MAGANIN CIWON KAI MACE KO NAMIJI



Ciwon kai yana daga cikin chutukan da ake fama dasu yau da kullum. Kuma yana da dalilai ko Musabbabai da yawa. Amma ga wasu fa'idodi masu albarka ka jarraba. In sha Allahu zaka dace :

1. SURATUL FATIHA : Malaman Musulunci sun ce lallai fatiha tana maganin kowacce irin chuta ajikin 'Dan Adam. Yadda zakayi amfani da ita domin magance matsalar ciwon kai shine: Kayi Basmalah ka sanya hannunka na dama ka rike goshinka ko kuma wajen da yafi ciwon. ka karanta Fatiha Qafa daya sannan ka saki kan naka. In sha Allahu zaka ji ya Dena.

Idan bai dena ba, ka sake rikewa sannan ka karanta Fatiha din Qafa uku. Zaka ji ya dena. Idan kuma bai dena ba, ka karanta Qafa biyar. idan bai dena ba, ka karanta Qafs bakwai. In Allah ya yarda zakaji ka warke nan take.

2. MAN HABBATUS SAUDA : Ka samu Man Habbatus Sauda ka zuba acikin Garwashi sannan ka rika shekar hayakin. In sha Allahu zakaji babu ciwon kan.

3. MAN TAFARNUWA, MAN GELO : Kowannensu idan ka shafa zaka samu waraka daga ciwon kan.

Allah ya sawwake. Allah ya yaye maka.

Post a Comment

0 Comments