LITTAFIN FIQHU DARASI NA UKU



YADDA AKE AIWATAR DA SUNNONIN FIƊRA

Abin da ake nufi da sunnar fiɗ’ra ita ce wasu abubuwa da suke jikin mutum da ake so ya cire su ko ya bar su. Misalin wanda ake so a cire kamar farce. Misalin abin da ake so a bari kamar gemu . Su ma guda goma ne:
1. Aske gashin baki ko rage masa tsawo da cika gemu da barin sa, saboda hadisai masu yawa. Daga ciki akwai hadisin da Manzon Allah ﷺ Ya ce: “Ku saɓawa mushirikai. Ku cika gemu ku aske gashin baki.” 
2. Yin aswaki, sunna ne mai karfi. Manzon Allah ﷺ Ya ce: “Aswaki yana tsarkake baki kuma yana jawo samun yarda daga Allah ﷻ. Akwai wasu muhimman lokuta da ake so mutum ya dinga yin aswaki kamar lokacin shiga gida, lokacin bacci, lokacin tashi daga bacci, lokacin alwala da lokacin sallah da karatun Al’Qur`ani mai girma.
3. Yin kurkurar baki da shaƙa ruwa da facewa a lokacin wanka da alwala da lokacin farkawa daga bacci. Yana tsaftace baki da hanci bayan kasancewarsa ibada.
4. Yanke farce (akaifa ko qumba ): Kada mutum, mace ko namiji, ya bar farcensa ya yi zaƙo-zaƙo, har ya wuce kwana arba'in ba a yanke shi ba, domin yana tara datti da ƙazanta kuma yana hana ruwa shiga tsakani a lokacin wanka da alwala, kuma hakan yana iya jawo samun lam'a.
5. Aske gashin hammata: Kada mutum ya bar hammatarsa ta tara gashi. Hakan ya saɓawa sunnah, kuma ga shi ƙazanta ne, kuma yana iya hana ruwa shiga a lokacin wankan ibada kamar janaba ko jinin al'ada.
6. Aske gashin gaba. Kada mutum ya bar gashin gaba ya yi yawa ba tare da askewa ba, domin haka ya saɓawa karantarwa Annabi ﷺ. Kuma barin nasa ƙazanta ne, kuma za a iya ɗaukan cututtuka da jin rauni a lokacin mu'amalar aure. Kuma idan ya yi kauri da yawa zai hana ruwa shiga a lokacin wanka a sami lam'a. 
7. Yin amfani da ruwa a lokacin tsarki da wanke najasa, domin ruwa ya fi komai tsaftacewa, wajen wanke fitsari da kashi.
8. Wanke hannu musamman kafin cin abinci da bayan an ci abinci da lokacin shiga banɗaki da fitowa, lokacin kwanciya da bayan an farka daga bacci da lokacin yin alwala da wanka da duk lokacin da aka bukaci a wanke hannu domin tsafta da ibada da kiwon lafiya da dai sauran su.
9. Yin kaciya ga maza sunnah ce wajiba, amma ga mata sai idan ana buƙatar yi sai a yi, idan ba a buƙata sai a bar shi, domin ga mata ba dole ba ne.
10. Barin furfura idan ta fito. Kada a cire ta ko a shafa bakin abu, yadda za ta ɓuya, amma babu laifi a yiwa furfura ƙunshi da lalle ko wani kala amma ban da baqi.
11. Idan mutum zai bar gashi a kansa babu laifi, amma ya kula da shi wajen wankewa da tajewa da gyarawa, kuma kada ya aske wani wuri ya bar wani wuri. Yin haka ya saɓawa Shari'ah. Ya kula da gashin kansa wajen tsafta, kamar yadda Manzon Allah ﷺ yake yiwa gashin kansa da kuma umarni da ya yi ga dukkan wanda ya tara gashi ya dinga kula da shi.
Allah ya ƙara ganar da mu gaskiya da bin ta.

Post a Comment

0 Comments