JININ AL’ADA.
Abin da ake kira da jinin al’ada shi ne wani jini ne na ɗabi’a wanda yake fita daga cikin gaban mace a wasu lokuta sanannu kuma Annabi ﷺ ya ce, “Wani abu ne da Allah ﷻ Ya rubutawa mata ‘yan Adam.” Don haka ba ciwo ba ne, ba tawaya ba ne, ba naqasa ba ne, ba kasawa ba ne, haka Allah ﷻ Ya qaddara wannan jini ya dinga fita, wanda kuma shi ne alama da ake gane mace za ta iya ɗaukar ciki, za ta iya haihuwa cikin hikimomin da Allah ﷻ Ya tsara.
HUKUNCE-HUKUNCEN JININ AL’ADA (HAILA)
Menene jinin al’ada?
Yaya iyakar jinin al’ada yake? Ma’ana, yaushe mace take fara jinin al’ada kuma yaushe take gamawa?
Kwanaki nawa mai ala’da take yi?
Tsakanin ɗaukewar jinin da zuwa wani jinin, gwargwadon kwana nawa ne ta yadda idan jini na biyu ya zo za a kira shi sabon jini?
Menene mafi yawan kwanakin da mace za ta yi tana tsarki?
Shin mace mai ciki tana yin haila ko ba ta yi?
Idan mace ta sami tsarki kafin ala’darta ta cika, me ya kamata ta yi?
Idan lokacin al’adar mace ya sauya, da can tana yi a farkon wata sai ya koma ƙarshe, ko tana yi a ƙarshe sai ya koma farko, ko tana yi a farko sai ya dawo kwanakin tsakiya, yaya za ta yi?
Idan mace ta sami ƙarin lokaci, da tana kwana shida ya koma goma, ko kuma da tana yin kwana goma ya koma shida, yaya za ta yi?
Idan jini ya yankewa mace tana cikin al’ada, sai ya yi kwana ɗaya ya ɗauke sai ya yi kwana ɗaya sai ya dawo, yaya za ta yi?
1. As-Suf’ratu wal Qud’ratu. Wani yanayi ne na sauyawar jini, ya koma fatsi-fatsi, ko ya koma hanta-hanta, yaya mace za ta yi a wannan yanayi, idan ya faru kafin haila ko tana tsaka da haila ko ta gama haila?
2. Yaya ake gane cewa jinin al’ada ya xauke da alamomin zuwansa?
3. Sannan menene ya haramta ga macen da take cikin al’ada? Kuma menene ba za ta yi ba? Sannan menene za ta iya yi?
Menene hukuncin wanda ya sadu da matarsa tana cikin al’ada? Ya zai yi ya kankarewa kansa wannan laifi?
Matar da jini ya rikice mata ya sauya daga ala’da ya koma jinin ciwo, ya za ta yi?
Menene bambance-bambancen da ke tsakanin hukuncin jinin da mace take yi na cuta da kuma jinin da take yi na al’ada?
Waɗannan su ne mafi yawan tambayoyi da mata suke yi game da jinin haila wanda za mu ji amsa a wannan waje.
Insha Allah.
0 Comments