Domin Ma'aurata Kawai.
Kamar yadda maza suke da hanyoyin Motsawa mata sha'awa ba tare da sun kusance su ba, haka ma suma matan suke da nasu hanyoyin.
Ina matukar mamaki idan naji mace na ƙorafin cewa suna kwana su tashi da miji a gida daya kuma gado daya amma sai ya dauki lokaci bai yi jima'i da ita kuma ita tana so. Hakan yana faruwa ne saboda sanin yadda zata yi amfani da halittun ta domin cusawa mijinta wannan sha'awar bama sai ta ce masa komai ba.
Sai dai mata da dama sun kasa sani ko amfani da wannan baiwar da Allah Ya musu.
Ga wasu hanyoyin da mata zasu iya amfani dasu domin motsawa mazansu sha'awa.
1: Sakonnin Tex: Macen da take son matsawa mijinta sha'awa tun kamin ya kusanceta tana iya somawa ne sakonnin text.
Sakonnin batsa suna da sauri da sauƙin tayarwa maza sha'awa muddin mace ta iya tsara su.
2: Abinci: Akwai wasu abinci da abin sha da suke motsawa maza sha'awa muddin suka ci ko suka sha su. Irin Waɗannan abinci dana sha mata da damar gaske basu ma sansu ba bare suyi amfani dasu. Yanada kyau ki sansu kuma ki shiryawa maigida su kamin ya gama ci ko sha zaki ga cewa yana cike da bukatar ki ba tare da kin kusance shi ba.
3: Gyaran Makwanci. Shi dakin da ake shirin yin jima'i da ciki yana bambamta ne da dakin da ake shirin kwanciyar barci a ciki.
Dakin kwanciyar jima'i baya bukatar haske kuma bai kamata a barshi cikin duhu ba.
Haka shi kansa gadon da za ayi jima'i akai yana bukatar kwalliya na musamman na zanin gadon dake dauke da wasu alami na soyayya ko kuma na jima'i.
Ba a barin dakin jima'i da wari ko kuma karni ba tare da an tura rashi da kayan kamshi ba.
Duk namijin da zai shigo yaga an shirya masa daki da irin wannan kwalliyar babu abunda zai zo masa a rai irin jima'i. Daga bisani kuma sai sha'awar sa ya soma motsawa ba tare da matarsa ta kusance shi ba.
4: Kiɗa Mai Ratsa Zuciya: Duk mace tasan irin wakar soyayya da mijinta yake son ya saurara. Da wannan wakar kawai kina iya motsawa mijinki Sha'awa sa.
Da zaran miji ya shigo daki yaji turare na tashi ga kuma an yiwa gado kwalliya ga kida mara sauti na tashi. Kawai zuciyarsa zata kamu ne da sha'awar matarsa. Mata nawa ne suka san hakan kuma suke amfani da hakan.
5: Tsafta Ce Jiki. Muddin mace ta tsafa ta ce jikin ta, tayi wanka ta soko gashin ta ko ta yi kitso mai kyau. Ga lalle ko kun shi a kafata da faratanta hakan yana motsawa maza sha'awa ba tare da sun kusanci mazan ba.
6: Kwalliya Da Ado : hanya ce mafi sauki da mace zata motsawa mijinta sha'awa.
Akwai mazan da suna ganin mace ta saka jan baki ko kuma ta yiwa fuskanta kwalliya nan take suke jin sha'awa. Sai dai ki kula da irin kwalliyar da mijinki yafi sha'awa sai ki masa tarko dashi.
Ado shi ne hanya mafi sauki wajen yiwa namiji tarkon da zaki motsawa mijinki sha'awa. Shi kwalliyar motsawa sha'awa ya bambamta da sauran kwalliya.
Ki tabbatar kwalliyarki a wannan manufar kinyi ne da kayan da zasu bayyana tsiraicinsa. Kayan da zasu riƙa motsa miki jikinki. Kayan da idan zasu rika fito da kan nonuwanki da kuma shatin gabanki. Hakan zai yi saurin motsawa miji sha'awarsa bayan kin turara jikinki.
7: Hira: da mai gida idan ana so a motsawa miji sha'awa daban yake da sauran hira na tsakanin miji da mata.
Dole ne ya zama kin tautausa muryar ki idan kina son motsawa miji sha'awa ta hanyar hira dashi. Kalaman ki zasu bambamta da kalaman da bana hira motsa sha'awa bane. Zaki shigo da hira ne na soyayya da ya ba halittar sa tare da tuna masa yadda ya jiyar dake dadi a jima'in ku na karshe da ire iren hira na motsa sha'awa.
8: Kwanciya Ko Zama: akwai kwanciya da zama na musamman da mata zasu iya yi domin motsa mazansu sha'awa. Zama ne da zaki yi cinyoyinki a bude. Ko kuma kiyi kwanciyar da zaki fito da rabin jikinki a waje. Haka shi ma kwanciya da akwai yadda ake yi domin motsawa namiji sha'awar sa ba tare da kince masa kala ba.
9: Tafiya : Idan kina son motsawa mijinki Sha'awar da ba sai kin taba shi ba kawai ki yi tafiyar da za ki rika juya duwaiwukanki. Kina girgiza nonuwanki nan take miji zai bukace ki.
10: Kallon Fim Din Soyayya: Ki samu wata tasha ko ki saka masa fim din da ake buga Soayya a cikinsa wanda kika san zai iya motsawa mijinki Sha'awa ba tare da kin kusance shi ba.
Wadannan wasu hanyoyi ne da mata zasu iya amfani da su domin su ribaci mazansu ta hanyar motsa musu sha'awa. Sai dai kuma duk macen data san waɗannan hanyoyi ya saba da akidar ta, al'adar ta ko addinin ta suna iya watsi dasu.
0 Comments