AMFANIN MAN KADANYA 7:



Man kadanya na da matukar amfani a fata domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin bitamin A da E. Wannan man na magance kurajen fuska da gautsin fata da kodewar fuska da kuma kyasbi. Amfani da wannan man na sanya sulbin fata. Ga kadan daga cikin amfanin man kadanya.

MATAKAN HADIN

1)- Hadin magance kyasbi:
A samu man sandal da man ‘labender’ a zuba a cikin man kadanya sannan a kwaba sosai sannan a samu murta a zuba hadin. A mayar da wannan man ya zama tamkar man shafawa a kullum. A yi amfani da shi na tsawon watanni shida za a ga canji.

2)- Gautsin fata:                                 
A samu man kwakwa da man zaitun da kuma man ‘almond’ sannan sai a zuba a murta a zuba man kadanyan a ciki sannan sai a kwaba da cokali ya kwabu sosai sannan sai a rika shafawa a jiki. A mayar da man, man shafawa bayan an yi wanka.

3)- Domin magance bushewar laba:
A samu zuma da man zaitun sannan sai a zuba a kan man kadanya a kwaba sosai. Sannan a sa a wuri mai sanyi . Sai a rika shafawa a labban baki a kullum za a samu sauki.

4)- Domin magance kurajen aski ga maza:
A samu man ‘rosemary’ da man kwakwa sannan a zuba a kan man kadanya a kwaba. A rika shafawa a kulum bayan an aske gemu. Yana warkar da kurajen da ke fesowa a gemu bayan an yi aski.

5)- Makero:
A samu man kadanya a hada shi da man zaitun sannan a rika shafawa a inda makeron yake a kullum domin samun biyan bukata.

6)- Kitso:
Kitso da man kadanya na magance fatar kai daga makero sannan yana sanya gashi laushi da tsayi da kuma sulbi.

7)- Sulbin fata:
Yawaita shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka na sanya sulbin fata sannan yana hana fesowar wadansu cuttukan fata.

Post a Comment

0 Comments