Wasu Abubuwan Da Suke Jawo Zafi Ko Jin Ciwo A Lokacin Jima'i:




Ba mata kadai ba, har maza sukan yi kukan jin zafi ko ciwo a lokacin da suke saduwa da iyalansu. Sai dai wannan kukan yafi yawaita ne ga mata. Hakan yasa zan soma kawo wasu dalilan da suke jawowa mata jin zafi a lokacin saduwa kamin na kawo na maza.


Duk wacce take son taji dadin Jima'i to dole ne sai ta saka sha'awar abun a ranta, muddin babu sha'awar shi koda bata jin zafi idan ana saduwa da ita, baza kuma taji dadinsa ba. Don haka ba abun kunya bane mace ta nunawa mijinta tana bukatarsa tun ma kamin ya shigo gidan. 

Muddin za a samu kyaunkyawan sadarwa tun kamin lokacin da za a gudanar da Jima'i to tabbas za a samu warakar jin ciwo ko zafi a lokacin saduwa. Saboda mace ta shiryawa hakan kuma ta saka abun arai tun kamin lokacin tana tsume kuma a shirye.

Duk macen da bata son namiji yana wahalar gaske taji dadin kwanciyar Jima'i da shi. A irin wannan lokacin idan tana saduwa da shi gabanta yana bushe batada sha'awa. Hakan kuma zai sata jin zafi kuma tana iya jin ciwu.

Rashin iyawa mace wasannin motsa sha'awa shima yana iya sata jin ciwo ko zafi idan aka yi Jima'i da ita. 


Wasu mazan babu ruwan su da yiwa mace wasanni, wasu kuwa basa tsaiwaita wasannin nasu sai kawai su afkawa matansu. Hakan dole ne ya cutar dasu.

Yana da kyau namiji ya dauki mintuna 20 zuwa 30 yana wasa da matarsa ko lokacinda ita da kanta ta bukaci shi. A irin wannan yanayin ta riga ta kamu kuma ta jike sharaf yadda bazata ji ciwo ko zafi ba.

Wasu mazan masu girman azzakari basa saka hankali ko natsuwa a lokacin da suka zo saduwa da matansu. Musamman matan sabbin aure da basu gama sabawa da halittar namijin ba.

Dole ne kabi matarka a hankali a wajen shiganta da saduwa da ita musaman idan kana da girman halittan gaba. Zaka bita a sannu a hankali har lokacin da ta saba da kai. Rashin yin hakan zai sa ta rika gudunka a duk lokacin da ta fahimci kana son saduwa da ita. Saboda maimakon ka sata jin dadi, wahala, zafi da ciwo kake jiyar da ita.

Tilastawa mace yin Jima'i a lokacin da bata da sha'awar yi zai iya sa taji zafi ko ciwo. Shi yasa masana ke bada shawara na yadda ma'aurata zasu yiwa junansu inkiya idan suna bukatar junansu domin shiryawa hakan kamin lokacin. Ko kuma nuna rashin sha'awar hakan kamin lokacin.

Akwai wasu cututtuka na mata da idan ba maganinsu aka yi ba mace ta daina jin dadin Jima'i kenan.

Cutuka irin su,Fibroids, Bacterial vaginosis, Vagina yeast, ovarian cyst a turance. Cutuka ne da suke sa mace ta rika jin ciwo ko zafi a gabanta. Don haka idan ma'aurata sun gwada duk abunda muka ambata a sama basu daina jin zafi ko ciwo ba, to su garzaya wajen likita domin neman magani.
Tabbas rashin iya wasannin motsa sha'awa ga wasu mazan shine asalin cutar da matan nasu a yayin Jima'i. Don haka maza magidanta sai a daure, a cire girman kai da kunya a nemi wannnan Illimin.

A darasi na gaba idan Allah Ya nuna mana bayan azumi zamu kawo dalilan da suma maza sukan ji ciwo ko zafi a yayin Jima'i da matansu.

Post a Comment

0 Comments