Sau da yawa kuma in ji masanan karancin abinci da cutar kasa, da cutar koda, ko kuma doguwar jinya kan haifar da bubuwa 12 da ake bukatar sha a lokacin tsananin zafi
Yanzu lokaci ne da ake fuskantar tsananin zafin rana a wasu yankuna na Kudu da Hamadar Sahara da suka hada da garuruwan da ke Arewacin Nijeriya da kuma Jamhuriyyar Nijar.
Wannan ma shi yasa ya sa aka tuntubi masana harkar lafiyar abinci don su bayar da shawarawari kan irin abubuwan da suka kamata a rinka ci da sha lokacin da ake fuskantar tsananin zafin rana.
Zafi yana sa gajiyadda kishirwa, yana kuma kona ruwan jiki. Don haka jiki yana bukatar abincin sha mai sanyi wanda zai sa a mayar da ruwan da yake konewa a kuma sami yanayi wanda yake mai sanyi
Jiki kan rasa kusan lita biyu zuwa biyu da rabi na ruwa a duk rana ta hanyar yin gumi da shan numfashi da fitsari da kuma bahaya.
Don haka a kalla ana bukatar a sha kofi shida zuwa takwas na ruwa a kowacce rana ko sauran abubuwa masu dauke da ruwa a cikinsu.
Malama Maijidda Badamasi Shu’aibu Burji wata kwarariyar Likita ce kan fannin abinci kuma malama a makarantar sakandaren ‘yan mata da ke Darmanawa a Kano, kuma ta bayyana jerin abubuwan da suka kamata a rika ci a wannan yanayi.
Gurji – Gurji kayan lambu ne da yake kunshe da saindarai daban-daban masu amfani da kare lafiyar jiki da fata.
Mangwaro – Yana kare konewar ruwan jiki.
Manyan lemun tsami – Yana kunshe da sinadaran bitamin C da B da sindaran Mineral kamar Calcium da Phosporous da Magnesium.
Ana iya sarrafa lemon tsami ta hanyar matse shi da kara masa ruwa da sanya sikari daidai idan ana bukata.
Kankana – Kashi 95 cikin 100 na kankana ruwa ne kuma shanta na kawar da kishi ruwa sosai.
Tsamiya – Ita ma tana daga cikin ‘ya’yan itacen da suke taimakawa wajen inganta jiki lokacin zafi.
Ana iya dafa ta tare da masoro da na’ana a tace ruwan a sanya dan sikari idan ana bukata a dinga sha.
Ruwan Rake – Ya kunshi sinadarai kamar Potatssium da Glucose da Calcium da Magnesium, sannan yana da amfani wajen kara wa jiki ruwa.
Ruwan Kwakwa – Shi ma ruwan da ke cikin kwakwa yana da muhimmanci a dinga sha lokacin yanayin zafi.
Gwaiba – Malam Maijidda ta bayyana cewa gwaiba ma wani muhimmin kayan marmari ne da jiki ke bukata miusamman a lokacin zafi, saboda sinadaran da take dauke da su kan masu inganta yanayin jiki ne.
Abarba – Ita ma tana da sinadari masu saurin sa abinci ya narke da kuma ruwa sosai a cikinta.
Tumatur – Kashi 94 na tumatari ruwa ne. Za a iya cin sa hakanan ko a markadawa ko a sa shi cikin abinci.
Korayen ganyayayaki – Kusan kashi 80 zuwa casa’in nasu ruwa ne, wanda yake sawa su narke nan da nan idan an ci su. Hakan na sawa su sanyaya jiki. Ganyaryaki sun hada da kamar su zogale da latas da lamsur. Masana sun bayyana cewa miyar kuka na kara wa mata ni’ima da karfin mazakunta ga maza.
Kuka
Kuka wata bishiya ce mai asali da ake samu a nahiyar Afirka da kuma wani yanki na kasashen Larabawa.
A al’adance bishiyar kuka tana da matsayi da muhimmanci ga abinci da kuma magungunan mutanen Afirka.
Kuka tana kunshe da muhimman sinadarai masu gina jikin dan Adam kuma masu inganta lafiya, kamar yadda mujallar lafiya ta Healthline ta bayyana a wani bincikenta game da amfanin ita kuka ga lafiyar dan Adam.
Tun daga ganyen kuka, da bawon da kuma’ya’yan Kuka dukkaninsu suna da sinadarai masu amfani sosai a jikin mutum.
Mujallar ta bayyana cewa Kuka tana ƙunshe da kusan dukkanin sinadaran da jikin mutum yake bukata – Kuka na da sinadarin Calcium da suke taimakawa wajen kwarin kashi da Hakori da sinadarin magnesium wanda yake daidaita jini.
Kuka tana kuma da sinadarin iron wanda yake kare jiki daga kamuwa da cutar rashin jini, hakanan kuma Kuka tana da sinadarin potasium da ya ke sasaita jini.
Sannan kuma wani babban sinadarin Vitamin C ya fi yawa a Kuka wanda yake yaki da cututtuka.
Sauran sinadaran da suke cikin Kuka sun hada da sinadarin Cabonhydate da Protien da bitamin D da kuma sinadarin fibre da ke sa abinci saurin narkewa a jikin dan Adam.
0 Comments