TURAKUN ALQUR’ANI (DARASI NA 9)




Abu Hurairah رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Mutane ba su haɗu a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah ﷻ suna karanta littafin Allah ﷻ suna yin darasinsa ba, sai Allah ﷻ ya saukar musu da nutsuwa, rahama ta lulluɓesu, Mala'iku sun kewayesu, sannan Allah ﷻ ya ambacesu a wajen waɗanda suke tare da shi.” 
Waɗannan su ne manyan darajojin da ake samu a wuraren da ake karanta Alqur’ani. 
Daraja ta farko: Samun nutsuwa. 
Daraja ta biyu: Rahama za ta lulluɓe masu yin. 
Daraja ta uku: Mala'iku za su kewayesu.
Daraja ta huɗu: Allah ﷻ zai ambacesu a wurin manyan mala'kunSa.
Babu shakka wannan muhimmiyar daraja ce Allah ﷻ Ya ambace ka a cikin manyan Mala'ikunSa masu girman daraja, ya sanar da su cewa kana da daraja da ƙima a wajenSa.

Wannan Alqur’ani yana da juz’i talatin (30), yana da izu (60), yana da rub'i (240), yana da sumuni 480.yana da sura (114), sannan yana da ayoyi (6,236) , yana da kalmomi 77437.da huruffa 323617.
1.Sahabbai sun mai da karatun sa ibada, wato kodayaushe suna cikin karanta shi dare da rana, wannan kuma shi ya jawo musu albarka da daraja da mutunci da ƙima a wajen Allah ﷻ a rayuwarsu. 
2. Idan watan Ramadan ya zo sukan ba da ƙoƙari da himma wajen karanta shi iya bakin ƙoƙarin su. 
3. Malam Ibn rajab ya ce, sashin magabata sun kasance wani yakan sauke Alqur’ani a duk kwana uku,
4. Wani kuma yakan sauke Alqur’ani a duk kwana bakwai, kamar malam Ƙatada,
5. Haka kuma wani yakan sauke Alqur’ani a duk bayan kwana goma, kamar malam Abu Raja'in,
6. Daga cikin su akwai wanda yake karance Alqur’ani kaf a watan Ramadan a cikin sallah, kamar malam Aswad yana karanta Alqur’ani izu (30) a kowane dare, wato kenan a duk kwana biyu yake sauke Alqur’ani. 
7. Haka nan malam Ibrahim Annakha'i ya kasance a goman ƙarshe na Ramadan a duk kwana uku yana sauke Alqur’ani. 
8. Haka nan malam Qatada ya kasance a duk kwana bakwai yana sauke Alqur’ani, amma idan watan Ramadan ya zo a duk kwana uku yana sauke Alqur’ani, idan kuma goman ƙarshe ta zo a kullum yana saukar Alqur’ani sau ɗaya. 
9. Haka nan ImamusShafi'i a cikin watan Ramadan yana yin sauka (60) ta Alqur’ani, wato kenan a kullum yana saukar Alqur’ani sau biyu. 
10. Haka nan an ruwaito Imamu Abu Hanifa shi ma yana yin sauka (60) a cikin watan Ramadan, wato shi ma kullum yana yin sauka biyu kenan. 
11. Imamuz Zuhri ya kasance idan watan Ramadan ya kama yana cewa wannan wata ne na tilawar Alqur’ani da ciyar da mutane. () 
12. Ya zo cewa Imamul Bukhari ya kasance yakan yi suka (40) a cikin watan Ramadan. 13.Imamu Zahbi ya ce malam Musabbin Bin Sa’id ya ce, Muhammad Bin Isma'ila (Bukhari) ya kasance yana sauke Alqur’ani da rana a cikin watan Ramadan, sannan yakan sauke Alqur’ani a cikin sallar tarawihinsa a kwana uku. Kamar yadda ya zo a cikin Siyaru A'alamin Nubala'i. 
14. Haka nan Imamu Ibn Hajar Al-Asƙalani ya ce, malam Muƙsim Ɗan Sa'ad ya ce, Muhammadu Ibn Isma'ila (Bukhari) ya kasance idan daren farko ya zo na watan Ramadan ya kasance yana tara abokanansa suna yin sallah yana karanta aya (20) a kowacce raka'a. 
15.Haka kuma Imamu Ibn Rajab yana cewa, Ibn Abdil Hakam ya ce, Imamu Malik ya ce, idan watan Ramadan ya shigo yakan rufe majalisin hadisi da na koyar da ilimi sai ya shagala da tilawar Alqur’ani, yana dubawa da Mus'haf (ƙur’ani). 
16.Malam Abdurrazaƙ ya ce, Imamu Sufyanus Assauri ya kasance idan watan Ramadan ya shigo sai ya daina kowacce irin ibada, sai kawai ya shagala da karatun Alqur’ani. 
Ummina A’ishah رضي الله عنها ta kasance tana da rubutaccen Alqur’ani sai ta ɗauko shi ta yi karatu da rana a cikin watan Ramadan har zuwa lokacin da rana za ta hudo, sai ta ajiye ta yi barci don ta huta.

WAƊANDA SUKE SAUKE ALQUR’ANI A KULLUM KO A RAKA’A ƊAYA

Daga cikin magabata da suke sauke Alqur’ani a kullum ko a cikin raka'a ɗaya akwai sayyidina Usman Bin Affan رضي الله عنه, akwai Tamimud Bn Aus Addariy رضي الله عنه, akwai Sa'idu Bn Jubair. Sannan akwai ma su yin sauka a sati, daga cikin su akwai sayyadina Usman Ɗan Affan رضي الله عنه, Sa'idu Bn Zaid رضي الله عنه, Zaidu Bn Sabit رضي الله عنه, Ubayyu Bn Ka'ab رضي الله عنه, da wasu jama'a daga tabi'ai, kamar Abdurrahman Bn Yazid, da Alƙamatu Bn Waƙƙas, kamar yadda ya zo a cikin littafin Attibyan fi adabi hamalatul ƙur'an shafi na (46).
 Malamai sun ce, magabata na ƙwarai sun kasance idan watan Ramadan ya gabato sukan yi addu'a ta tsawon wata shida suna roƙon Allah ﷻ ya kai su watan Ramadan, idan kuma watan azumin ya wuce sukan yi wata shida suna yin addu'ar Allah ﷻ ya sake maimaita musu su sake ganin wata Shekarar, kuma Allah ﷻ ya sa abin da suka yi karɓabbe ne. kamar yadda ya zo a cikin littafin Laɗa'iful Ma'arif shafi na (376). 
* * * *

Post a Comment

0 Comments