MANYA-MANYAN LARURORINMU A YAU
Ƙarzuwa (scabies) larura ce ta fata mai matuƙar saurin yaɗuwa, da ke faruwa sakamakon rayuwar waɗansu ƙananun ƙwari (dangin gizo-gizo) da ake kira 'Sarcoptes scabiei' - a kai da cikin fata. Waɗannan ƙwari ba'a iya ganin su da ido kai tsaye saboda ƙanƙanta. Larurar takan bayyana a salo na ƙananun ƙuraje, borin fata, ɗaɗewa haɗe da kuma ƙaiƙayi da sauran su.
Waɗancan ƙananun ƙwari sukan rayu akan fata ne, bayan kamuwa kafin daga bisani macen ta kutsa kai cikin fata domin yin ƙwai da kuma ƙyanƙyasar ƙwayayen Daga baya, suma ƴaƴan sukan fito waje domin cigaba da yaɗuwa i zuwa sauran sassan jiki domin haddasa wannan larura da ake kira ƙarzuwa
Kamar yanda muka gani, ƙarzuwa ba larura bace ta ƙwayoyin cututtuka kamar bakteriya, fungai ko bairos da sauran su, kamar yanda muka saba gani a sauran cututtuka masu yaɗuwa; domin waɗancan ƙwari dake haddasa larurar ba sa daga cikin misalan ƙwayoyin cututtuka. Hasali ma, ƙarzuwa yana faruwa ne sakamakon artabun jiki da su ƙwarin, ƙwayayensu da kuma kashin su.
Duk da saurin yaɗuwar wannan larura, ana iya magance ta cikin ɗan lokaci kasancewar magunguna kan yi matuƙar tasiri akan waɗancan ƙwarin da ke haddasa ta, to sai dai wani hanzari ba gudu ba shine, magance ta na buƙatar yin maganin ga mai larurar da kuma ɗaukacin makusantan sa/masu mu'amullar haɗa fata dashi da kuma muhallinsa.
ABINDA KE HADDASA ƘARZUWA DA KUMA YAƊUWAR SA
Kamar yanda muka ambata a sama, kamuwa da waɗancan ƙwari ƙanana da ake kira 'Sarcoptes scabiei' shi ke haddasa wannan larurar. Waɗannan ƙwari na da dangogi daban-daban, wasunsu kan sanya larurar a mutane, wasunsu kuma ga dabbobi.
Kaitsaye, karzuwa yana yaɗuwa:
1. Daga mutum zuwa mutum: ta hanyar haɗakar tufafi, cuɗanyar fata ta kaitsaye; dalilin gaisuwa, taɓawa, saduwa da sauran su.
2. Daga muhalli zuwa mutum: ta hanyar amfani da bargo, katifa, ko dukkanin wani abin taɓawa na mai larurar.
Ƙarzuwa yana da saurin yaɗuwa a makarantu, gidajen kurkuku, wajen raino da gidan jinyar tsofaffi.
ALAMOMIN ƘARZUWA
Alamomin wannan larurar sukan bayyana da wuri ga waɗanda suka taɓa yinta. Ga waɗanda basu taba yinta ba kuwa, sukan jikirta har sama da wata ɗaya bayan kamuwa.
Alamomin suna faruwa ne sakamakon artabun jiki da su ƙwari masu haddasa ƙarzuwa. Suna faruwa a fatar kai, wuya, ƙirji, hannu, al'aura, ƙafafu da sauran su. Sun ƙunshi:
* Ƙaiƙayi
* Tashi/kumburin shashin fata
* Rurewar fata mai kama da kuraje
HAƊARIN KAMUWA DA ƘARZUWA
Ƙarzuwa na iya shafar kowa-da-kowa, ba tare da la'akari da yanayin tsafta, wanka ko matsayi na mutum ba. Illa iyaka, wasu abubuwan kan ƙara yiwuwar samunsa, misali:
- Haɗakar suttura
- Amfani da wajen canja tufafi; ga yan kwallo da sauransu
- Kasancewa yaro (ƙarami)
- Faruwar wasu larurorin kamar ƙanjamau da sankarar ƙashi
- Amfani da wasu magungunan
- Cuɗanya da mai larurar
ILLOLIN LARURAR ƘYAZBI
- Tsanantar ƙaiƙayi da daddare, wanda kan iya jawo ƙarancin barci/nutsuwa
- Tsanantar ƙaiƙayi na tilasta susa, wadda kan iya haifar da rauni da ke bude kofa ga shigar ƙwayoyin cututtuka cikin jiki
- Rashin sukuni cikin jama'a
SHAWARWARI A TAƘAICE
Yana da kyau mu sani cewar, wadancan kwarin dake haddasa ƙarzuwa suna rayuwa ne bisa fata da cikin ta, tare da shan jininmu kamar dai su kuɗin cizo da ƙwarƙwata. Sa'annan, magance ƙarzuwa ya haɗa magance shi a mutane da kuma muhallansu.
1. Hattara da cuɗanyar fata da mai larurar.
2. Hattara da tufafi da ba'a wanke ba.
3. Kasancewar ƙwarin dake haddasa ƙarzuwa sukan iya kwanaki hudu a raye bayan faɗuwa daga jikin mai larurar, yana da kyau wanke tufafinsa da ruwa mai zafi, da kuma busar dasu a wuri mai zafi; so samu a haɗa da guga.
4. Magunguna na matuƙar tasiri akan larurar, a don haka ayi hanzari tuntuɓar ƙwararru da zarar an fuskanci larurar.
5. Guji amfani da magunguna ba tare da izini ko shawarar ƙwararru ba!
Allah sa mu dace, aamiiiiin.
©M.A.B.
0 Comments