By Olusegun Mustapha |
Ni idan na yi sahur na kwanta sai cikina ya kumbura ko kuma na yi gudawa. Mene ne maganin wannan?
Daga Mudassir Ningi da Musa K.
Amsa: Ba wani abu za ku canza ba da ya wuce saurin kwanciya bayan sahur. A ka’idar kiwon lafiya bayan cin abinci yakan dauki awoyi 2 zuwa 4 bai shige cikin hanji ba. Wannan kuma ya danganta ne da abin da aka ci. Akwai wanda zai wuce cikin awa biyun an ma tsotse shi, akwai wanda kuma sai ya zauna awa hudu din nan.
To, idan mutum ya ci abinci ya kwanta bayan Sallah, lokacin abincin ko awa guda bai yi ba to tabbas zai samu matsala irin wadda kuke samu. Don haka dole ne a dan jinkirta kwanciya da akalla wata awa gudar bayan sallar domin abincin ya wuce kafin ku daina jin wadannan alamu.
Da gaske ne shan ruwan kanwa bayan sahur yana danne gyatsa da magwas? Ko hakan na iya jawo illa ga lafiya?
Daga Muhammad Salisu
Amsa: E, kanwa na iya sa abinci narkewa da sauri saboda tana rage yawan acid da ke ciki. To amma tana da illa idan aka lazimci shanta a kullum, domin tana da sinadaran ma’adinai na gishiri da yawa wadanda za su iya jawo matsaloli kamar na hawan jini da ciwon koda idan ana yawan sha. Irin maganin nan na minti kamar gelosil masu rage kwarnafi, za su fi kanwa amfani.
Ni kuma sai na tashi da safe ne nake jin alamun tashin zuciya, kai wani lokaci har da amai da jin juwa. Ko kuma ina gama cin abincin. Mece ce mafita?
Daga Ibrahim Usman Zaria da Amina Sakkwato da Saiful Islam
Amsa: To su kuma irin wadannan alamu ba na abinci ba ne. Su kuma sun fi nuni da shigar kwayoyin cuta ciki da hanji, musamman ma kwayar typhoid, duk tana sa irin wadannan alamu. Don haka ke nan sai kun je an auna an gani ko hakan ne.
A lokacin yin sahur ni ba na iya shan ruwa, domin ko na sha tashin amai zan rika ji, sai dai kamar fura ita ce ba zan yi amai ba. Ko matsala ce wannan?
Daga Aliyu B.
Amsa: A’a, ba wata matsala tunda kana shan abu mai ruwa-ruwa. Ba dole sai ruwa ba. Ya kamata dama kowa ya lura mene ne cikinsa ba ya so a irin wannan lokaci na sahur.
Lebbana ne suka yi bawo-bawo, da na bare sai wurin ya dade ya yi ja, amma ba sa ciwo. Me ke janyo haka kuma me ya kamata na yi? Me ke kawo bushewar bakin da cikin makogaro?
Daga Malama Jameel da Bala, Legas
Amsa: Alamun rashin ruwa a jiki ne lebba da baki da makoshi su rika bushewa. Don haka idan mutum yana yawan samun haka lokacin azumi to ya rage shiga rana, duk da cewa yanzu lokacin damina ne. Amma a wuraren da ba ta fadi sosai ba dole sai an rage shiga rana. Idan an sha ruwa kuma a rika yawan shan abu mai ruwa-ruwa, wanda ciki zai iya karba.
Ni kuma sai na kwana biyu ban sha ruwa ba, ko hakan ba matsala ga lafiyata?
Daga Adam Abbatuwa, Legas
Amsa: E, duk da yake masu yawan shan ruwa sun fi marasa yawan sha koshin lafiya, in dai kana yawan shan koma wane irin abu ne mai ruwa-ruwa ai da sauki, musamman ma da yake ku kasar Legas iskar da ke cikinta ba zafi kuma mai danshi ce sosai. Za ka ji da za ka zo Arewa ai dole sai ka sha ruwa za ka ji dadi.
Ina yawan shan kankana, domin a rana sai na sha kusan uku. Ko hakan matsala ce, kuma za ta iya yi mini illa?
Daga Boska Kwasara
Amsa: Amma dai ka san cewa an ce ko abu na da kyau yawansa ba zai haifar da da mai ido ba. Don haka yana da kyau ka saisaita yawan shan.
Wai shin ’ya’yan kankana da wasu kan hadiye suna da illa ne ko babu?
Daga dan Bashir
Amsa: Wasu masana cimakar abinci sun ce idan aka tara kwallayen kankana aka soya ko gasa, kafin a ci, akwai sinadarin protein da jiki zai iya amfana da shi. A danyensa dai ba mu da masaniyar amfaninsa.
Na kan dauki kwanaki da dama a yanzu ban je bayan gida ba. Kuma ni lafiyata kalau. Ina mafita?
Daga Bilkisu S.
Amsa: Yawan shan lemon bawo da abin da ke ciki na bezar, da ganyaye musamman bayan shan ruwa ko sahur da tafiyar kafa za su rage miki wannan matsala.
Wai me ya sa cikina wasu lokuta kan rika kugi har da zawo ne, ko da ban ci abin da zai batan ciki ba? Na fi jin irin wannan idan na ci Indomie ko na sha madara.
Daga Alh. Jinjiri, Legas
Amsa: Kai kuma da yake ka ware wasu nau’in abinci da ka lura su ne ke bata maka ciki ka ga ke nan ba za a alakanta abin da kwayoyin cuta ba, sai dai wadannan abincin. Dama akwai mutane da dama da wadannan abincin suke wa haka. Don haka sai ka guje su. Madara ka nemi ta waken soya, wato soy-milk. Maimakon Indomie kuma ka nemi wata taliyar
Me ke sa rashin jin dadi a baki idan mutum ya tashi daga barci?
Daga Hassan Gashuwa
Amsa: Shi kuma wannan ya ta’allaka ne a kan taruwar da kwayoyin cuta kan yi idan muka ci abu muka kwanta bamu goge bakin ba. Don haka ko da kai ba ka jure yin burushi bayan abincin dare ko sahur, to dole sai kana yin aswaki kafin kwanciyar kafin ka ji dadin bakin idan ka tashi daga barci.
Idan na ci dabino sai na ji hakorana sun fara ciwo. Me ke kawo hakan?
Daga 2-effect dan Gada
Amsa: Alamar kwayoyin cuta sun ci hakorinka ke nan. Idan ba ka ga wurin ba in ka duba da mudubi to mikin na can kasa ke nan. Don haka ba laifin dabino ba ne, hakoranka ne da suka riga suka fara ci. Ya kamata ka nemi asibitin hakori a duba. Idan an gyara kuma duk bayan cin zaki dole ka goge baki, musamman kafin kwanciya.
Me ke kawo farfashewar hakori ne wanda za ka ga yana bantarewa da kadan- kadan?
Daga Garba Gashua, Yobe
Amsa: Shi kuma wannan rashin kwarin hakorin ke kawo shi. Abinci masu sinadarin calcium irinsu madara, su suke kara karfin hakori da ma kashi.
Ko shin yawan shan zuma na da illa ga jiki?
Daga Adam Usman
Amsa: Zuma na da amfani da dama ga jiki, amma kamar yadda muka fada a sama ne, komai dole a ci shi daidai gwargwado, idan ya yi yawa kuma ai sai a fara tambayar ko kalau kake.
0 Comments