HUKUNCIN I’ITIKAFI A WATAN RAMADAN(DARASI NA 10):




Daga cikin manyan ibadu da aka fi yin su a cikin watan Ramadan ita ce, ibadar Iitikafi. 

  1. Mene ne I’itikafi a harshen Larabci da kuma ma'anarsa a Shari'a? 
  2. Mene ne hukuncin yin I’itikafi? 
  3. Waye ya kamata ya shiga I’itikafi? 
  4. Mene ne rukunan I’itikafi? 
  5. A ina ake yin I’itikafi? 
  6. Mene ne manufar yin I’itikafi? 
  7. Mene ne sharuɗɗann yin I’itikafi? 
  8. A wane zamani ake yin I’itikafi? 
 9. Mene ne yake ɓata I’itikafi? 
 10. Wane amfani ake samu a cikin yin I’itikafi? 
 11. Abubuwan da suka halatta ga mai yin I’itikafi. 
 12. Shin za a iya yin I’itikafi a wajen watan Ramadan? 
 13. Shin za a iya yin I’itikafi babu azumi? 
 14. Wacce irin ibada mai yin I’itikafi zai mayar da hankali wajen yin ta? 
 15.Mene ne ya halatta mai I’itikafi ya aikata? 
 16.Da yaushe ake shiga I’itikafi? 
17. Da yaushe ake fita daga I’itikafi? 
 18. Mutum yana iya fasa I’itikafi bayan ya fara? 
 19.Shiga I’itikafi da guzuri da sauran kayan buƙata.
Ma'anar I’itikafi: Ma'anar I’itikafi a harshen Larabci shi ne zama wuri ɗaya, ko kuma lazimtar aikata wani abin kirki ko na banza. 
Amma I’itikafi a Shari'an ce shi ne, mutum ya zauna a masallaci ko ya kawwame kansa a masallaci yana aikata wasu ayyukan ɗa'a, domin neman yardar Allah ﷻ ko neman ƙarin kusanci da Allah ﷻ maɗaukakin sarki. 
Hukuncin yin I’itikafi: Shi dai I’itikafi tabbatacce ne a cikin Alqur’ani da sunnar Ma’aiki ﷺ da kuma ijma'in malamai. 
Hujjar yin sa a cikin Alqur’ani ita ce faɗin Allah ﷻ, inda yake cewa:
﴿وَلاَتُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ﴾ ()
Ma’ana: “Kada ku rungume su (mata) alhali kuna I’itikafi a masallatai.” Hujjar yin sa daga hadisi ita ce hadisin Ummina A’ishah رضي الله عنها inda take cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yin I’itikafin kwana goman ƙarshe, na watan Ramadan, haka ya ci gaba da yi har Allah ﷻ yakarɓi ransa. () 
Malaman musulunci gaba ɗaya sun tafi a kan Shar'ancin yin I’itikafi a watan Ramadan. 
Matsayin I’itikafi: Hikimar da ta sa aka Shar'anta yin I’itikafi ita ce, domin mutane su koma ga Allah ﷻ, saboda gafalar da suka yi a tsawon Shekara da tarin zunuban da suka aikata a tsawon Shekara, to sai ake so su kawwame kansu a wani muhimmin wuri mai ƙima da daraja a wajen Allah ﷻ wato masallaci, don yawaita zikiri da karatun Alqur’ani, yawaita sallar nafila, yawaita istigfari, salati ga Annabi ﷺ da yawaita tunanin makoma da kuma lissafin yadda rayuwa za ta kasance nan gaba. 
Daga cikin wasu malamai masana suna cewa hikimar I’itikafi shi ne ka yanke alaƙarka da kowa ka jingina kanka ga Allah ﷻ, wato ka duƙufa wajen neman ƙara kusanta kanka ga Allah ﷻ.
Kashe-kashen I’itikafi: I’itikafi ya kasu kashi daban-daban, akwai lokacin da I’itikafi yake zama wajibi, akwai lokacin da yake zama sunnah, abin da ake cewa wajibi shi ne abin da ya zama dole mutum ya yi, sannan kuma abin da ake cewa sunnah shi ne abin da idan mutum ya yi shi zai samu lada idan bai yi ba babu zunubi. 
Inda I’itikafi yake zama wajibi shi ne, inda mutum ya wajabtawa kansa, ta hanyar bakance ko rantsuwa, kamar ya ce na yi alƙawari zan yi I’itikafi na wata guda, ko kwana ashirin, ko na kwana goma, to ya zama wajibi ya cika wannan alƙawarin ko bakancen da ya ɗaukarwa kansa, ko kuma kamar ya ce na rantse da Allah ﷻ sai na yi I’itikafi, ko idan ban yi I’itikafi ba kaza ya hau kaina, ko idan matata ta haihu lafiya zan yi I’itikafin kwana kaza, ko idan na auri wance zan yi I’itikafi na kwana kaza. 
To idan Allah ﷻ ya sa matar tasa ta haihu lafiya ko ya aure ta ko mahaifan nasa suka warke, wajibi ne ya cika wannan alƙawarin da ya ɗaukarwa kansa na yin I’itikafin, saboda hadisin da aka ruwaito wanda Ma’aiki ﷺ yake cewa, “Wanda ya yi bakance zai bi Allah ﷻ to ya bi shi, wanda kuma ya yi bakance zai saɓe shi to kada (ya kuskura) ya saɓe shin.” () 
Mafi ƙarancin I’itikafi shi ne gwargwadon abin da mutum ya ɗauka na niyya, domin mutum zai iya yin I’itikafi na kwana ɗaya, zai iya yin na kwana biyu ko biyar, ko na kwana goma. 
Mafi tsawonsa shi ne wata guda, mafi ƙarancinsa shi ne kwana ɗaya a mazhabar Imamu Malik. 
Wasu malamai ma suna ganin za ka iya yin I’itikafi na awanni, kamar ka ce zan yi I’itikafi daga azahar zuwa la'asar, ko daga la'asar zuwa magariba, ko daga magriba zuwa ishsha, ko daga ishsha zuwa sallar asuba, ko daga asubahi zuwa azahar. 
Wato mutum ya zauna a masallaci iya waɗanann awannin da niyyar I’itikafi da niyyar kara kusanci da Allah ﷻ, shi ma zai iya zama I’itikafi a bisa ra'ayin wasu malamai. 
Wannan kuma shi ne ra'ayin malaman Hanafawa, Shafi'awa, da Hambalawa.” ()
Rukunan I’itikafi: Shi I’itikafi yana da rukunai guda biyu, rukuni na farko: shi ne zama a cikin masallaci gwargwadon abin da mutum ya niyyata na adadin kwanaki ko awannin ko lokaci, amma fa tare da niyyah a mazhabar Imamu Malik kuma sun ƙara har da azumi, wato lallai ne sharaɗin yin I’itikafi ya zamo ana yin azumi.
Sharuɗɗan I’itikafi: Akwai sharuɗɗa guda bakwai da aka sharɗanta wa mai son ya yi I’itikafi: 
Ya zamo Musulmi, wanda ba Musulmi ba, ba zai shiga I’itikafi ba. 
Ya zamo mai hankali, mahaukaci ba zai shiga I’itikafi ba. 
Ya shiga I’itikafin da niyyar yin I’itikafin. 
Ya zamo ya tsarkaka ga barin janaba, jinin haila ko na haihuwa a lokacin shiga I’itikafin.
Ya kame ga barin saduwa da iyali da makamancin hakan, kamar runguma, sumba, ko shafar juna da rana ko da daddare. 
Idan namiji ne mai yin I’itikafin ya yi shi a masallacin da ake yin sallar Juma'a, idan I’itikafin nasa zai haɗa da ranar Juma'a. 
Sannan kuma idan yana da iko ya yi I’itikafin nasa a masallacin Ka’aba, ko masallacin Ma’aiki ﷺ, ko Masallacin Baitil Maƙdis, ko Masallacin Ƙuba, 
Domin waɗannan su ne manyan Masallatan da suka fi kowane Masallaci daraja da ƙima a wajen Allah ﷻ, idan kuma bai sami ikon zuwa waɗancan Masallatan ba, sai ya yi a kowane Masallacin da ya tabbata Masallaci ne wanda Jama’a suke haɗuwa su yi jam’in sallah biyar da kuma sallar Juma’a, idan I’itikafin nasa zai haɗa da ranar Juma'a.
Idan mace ce za ta shiga I’itikafi za ta shiga ne da sharaɗi guda uku. 
a) Idan tana da miji ko waliyyi sai ta nemi izininsa. 
b) Ya zamo wurin da zata yi I’itikafin wuri ne keɓantacce wanda ba za ta cakuɗu da maza ba. 
c) Za ta tanadi duk wani abin da ake tanada idan za a shiga I’tikafin. 
Sannan shi I’itikafi ana so a yi shi a cikin watan azumi. 
Haka nan mai I’itikafi ba zai fita dubiyar mara lafiya ko halartar sallar jana’iza ko rakiyar mamacin zuwa maƙabarta ba, sai dai in jana’izar da ta zamo dole a kansa, kuma ba zai shafa jikin matarsa ba, ba zai rungume ta ba, ba kuma zai sumbance ta ba. 
Haka nan ba a yin I’itikafi sai da azumi, Kuma ba a yin I’itikafi sai a Masallaci. ()
Abin da ya halatta ga mai I’tikafi: Ya halatta ga mai I’itikafi ya tsaftace jikinsa. Ma'ana ya goge bakinsa da asuwaki ko da man goge baki na bature.
Sannan zai iya fita ya je ya yi wanka zai iya taje kansa, zai iya yin alwala, za a iya ɗaura masa aure, amma sai dai matar ba za ta tare ba, zai iya siye ko siyarwa, ammafa ba wai ya shiga harkar kasuwanci gadan-gadan kamar yadda yake yi a kasuwarsa ba, zai iya yin rakiya ga wanda ya kawo masa ziyara, amma kada rakiyar ta yi nisa. 
Haka nan matarsa za ta iya ziyartarsa, yana masallacin zai iya rakata har bakin harabar masallacin, kamar yadda Ummina Safiyya رضي الله عنه matar Ma’aiki ﷺ ta ziyarce shi lokacin da yake yin I’itikafi a masallaci. 
Kuma ba zai shiga gidansa ba, koda masallacin da yake yin I’itikafin a kusa da gidan yake, sai dai idan da wata larura ta Shari’a. 
Sannan zai iya ajiye kayan buƙatunsa a masallacin amma akula da tsaftace masallacin ta wajen share shi, da ƙamsasa shi. 
Abdullahi Ɗan Abbas رضي الله عنه ya ce, wanda ya shiga I’tikafi kuma sai ya sadu da matarsa to I’itikafinsa ya warware, sai ya sake sabuwar niyya. ()
Wajibi mai I’itikafi ya shagala da abubuwa guda uku:
Na farko: Ya kula da karatun Alqur’ani mai Girma, ya dage a kan karanta shi sosai. Babu laifi ma ya ɗauki wani adadi na sauka da zai yi kafin ya ƙare I’itikafin. Misali, kamar sauka ɗaya, ko biyu, ko uku, idan zai iya. Amma sai dai kada ya ɗorawa kansa abin da ya san ba zai iya ba, ko kuma zai iya amma sai ya sha wahalar gaske, an fi so ya yi ibadarsa a cikin nishaɗi gwargwadon ikonsa.
Na biyu: Ya shagala da yawan zikiri kamar hailala, tasbihi, takbiri, tahmidi, istigfari ko kuma salati ga Annabi ﷺ da sauran ayyukan ibada.
Na uku: Ya mai da zuciyarsa zuwa ga Allah ﷻ, wato ya riƙa tunanin shi wane ne? Wane ne ya yi shi? Me ya sa ya yi shi? A ina yake? Me yake yi? Ina za shi? Kuma mai zai faru? Sannan ya riƙa tunani a kan mutuwa da abin da zai biyo bayanta na tambaya a cikin Ƙabari, wanda Mala’iku za su yi masa cewa, wane ne Allanka? Wane ne Annabinka ﷺ? Mene ne addininka? Kuma ya riƙa tunanin ya zai tashi a gaban Allah ﷻ a ranar ƙiyama? Sannan ya riƙa tunanin Ƙabari, kuncinsa, duhunsa, micizansa, kunamun cikinsa, zafin cikinsa, kaɗaitar kwanciya a cikinsa, firgicin tambayar cikinsa, daɗewar da za ai a cikinsa kafin ya fito daga cikinsa, da tsayuwa gaban Allah ﷻ da tsoron tambayar da zai yi masa da firgicin rashin sanin amsar da zai bayar, da daɗewar da zai yi a tsaye a gaban Allah ﷻ kafin a sallami kowa, da auna ayyukansa a kan sikelin nan mai adalci, da firgicin rashin tabbacin a wane hannu zai karɓi takardun ayyukansa, a dama ne ko a hagu? da tsoron haɗuwa da waɗanda ya cuta ko ya ɗanne haƙƙinsu, ko waɗanda ya ha’inta, da firgicin hawa kan siraɗi, da tunanin yana daga cikin waɗanda za su iya tsallakewa lafiya, ko yana cikin waɗanda miyagun ayyukansu za su afka su cikin wuta? sannan da tunanin yana daga cikin waɗanda za a bari su shiga cikin tafkin Al-Kausara, ko yana cikin waɗanda za a kora a hana su shiga, da dai sauran makamantan waɗannan. 
Ya Allah ﷻ ka iya mana.

 Fa'idodin da suke ƙunshe a cikin I’itikafi:
Akwai tarbiyya da mutum zai samu ta hanyar tattara kansa da zuciyarsa zuwa ga Allah ﷻ baki ɗaya ya karkaɗe zuciyarsa ga barin hargowar duniya da ruɗinta da kawace-kawacenta. 
Mutum zai iya ta ra hankalin sa wuri ɗaya domin ya dace da samun daren lailatil ƙadari.
Mutum zai sabawa kansa haƙuri da zaman masallaci wanda zama ne mai albarka. 
Mutum ya ciru daga wasu miyagun al’adu na cutarwa kamar zaman gulma, yi da mutane, annamimanci, yaɗa jita-jita da ɓata lokaci cikin abubuwan da ba su da amfani, kamar sauraron kaɗe-kaɗe da raye-raye, ka ga zaman I’itikafin ya hana shi faɗawa cikinsu.
Mai zaman I’itikafi zai koyi wasu abubuwa masu amfani na samun nutsuwa da ƙarin yaƙini a zuciyarsa a tsakaninsa da mahaliccinsa, waɗanda za su sashi ya ƙara ayyukan ƙwarai ya guji munanan ayyuka. 
Ya san cewa, ba ya fita daga I’itikafi sai da wani dalili, kamar dai ya sa kansa ne a cikin wani kurkuku domin ya yiwa kansa wata tarbiyya ta musamman wacce za ta sa ya sabada zama domin ƙarin kusanci da Allah ﷻ. 
Mai zaman I’itikafi zai ƙudurce a zuciyarsa cewa, zaman ibada yake yi a masallacin, domin neman yardar Allah ﷻ da neman ƙarin kusanci da shi, sannan ya san wannan zaman wata jarrabawace da horo wacce ya koye ta yadda idan ya fito daga I’itikafin zai ci gaba da ita, domin ya riga ya sabada ita. 
Zai samu nutsuwa a cikin zuciyarsa da kwanciyar hankali. 
Mutum zai iya sauka mai yawa ta Alqur’ani. 
Mutum zai iya tuba daga zunubansa ƙanana da manya waɗanda ya san yana yi, ya kuma nemi gafarar Allah ﷻ a kansa don ya yafe masa. 
Mutum zai sabada tsayuwar dare wacce da take yi masa wuya, to yanzu za ta zame masa jiki saboda yawan sallah da zikiri da zai yi. 
Mutum zai raya lokutansa a kan bin Allah ﷻ. Waɗannan duka suna cikin irin amfanin da mutum zai sa mu idan ya shiga I’itikafi.
Lokacin da ya kamata mai I’tiƙafi ya ɗauka yana ittiƙafi: Ibn Hajar a cikin Fatahul Bariy juz'i na (4) shafi na (342), ya ce, malamai sun haɗu a kan cewa shi I’itikafi ba shi da iyakar yawa, ba shi da iyakar ƙaranci, sai dai idan mutum ya riga ya sharɗantawa kansa cewa zai yi I’itikafin kwana kaza, to ya lazimce shi ya cika wannan adadin da ya ɗaukarwa kansa.

Wanda kuma ya sharɗanta cewa zai yi shi da azumi amma iyakarsa kwana ɗaya, wato awa ashirin da huɗu, to wurin da ake yin I’itikafi dai kamar yadda muka faɗa shi ne masallaci. 
Yaushe ya kamata mai I’itikafi ya shiga I’itikafi: Imamul Bukhari ya ruwaito hadisi daga Ummina A’ishah رضي الله عنها ta ce, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yin I’itikafi a goman ƙarshe na Ramadan, kuma ni ce nake kafa masa hemar da zai shiga ya yi I’itikafin bayan ya yi sallar asuba, sai kawai ya shiga wurin I’itikafin nasa. 
Wannan ya nuna mana cewa ana shiga wurin da za a yi I’itikafi ne bayan sallar asuba.
Da yaushe mutum zai fito daga I’itikafi? Abu Sa’idi Al-Khudriy رضي الله عنه ya ce, mun yi I’itikafi tare da Ma’aikin Allah ﷺ a goman tsakiya na Ramadan, lokacin da muka wayi gari a kwana na ashirin da ɗaya, sai muka kwaso kayanmu da nufin za mu fita daga I’itikafin. 
Imamu Ibn Hajar ya ce, wannan ana ɗaukarsa ga wanda yake yin I’itikafin da daddare ne ba da rana ba. 
Wanda kuma yake son ya shiga I’itikafi da rana, sai ya fito bayan Alfijir ya keto, wanda kuma yake son ya yi na kwanaki, sai ya shiga bayan ketowar Alfijir, ya fito bayan rana ta faɗi. 
Wanda kuma yake son ya yi na dare da rana, sai ya shiga kafin rana ta faɗi ya fito bayan rana ta faɗi a kwana na gaba.
Ladubban I’itikafi: an so ga mai I’itikafi ya shagala da tsantsar ɗa'a, kuma ya nesanci abin da ba zai amfane shi ba, domin bai kamata ya shiga I’itikafi da taba ko abin karta ko ya shiga I’itikafi yana buge-bugen waya ko ya tsaya yana (chatting) ko ya shagala da shiga (facebook, da instgram, da twiitter) ko duk wani wasa da zai shagaltar da shi ga barin ibadar da ta kai shi masallacin, ko kuma a buɗe dandalin hira a mayar da wajen I’itikafi wurin hira da tattauna labaran duniya da harkokin siyasa, kasuwanci, labaran wasan ƙwallon ƙafa, da sauransu.
Ko a mayar da wurin I’itikafi ya zama dandalin musun addini ko na qwallo, duk waɗannan ba su kamata mai I’itikafi ya shagala da su ba.

Mutum ba zai fita daga I’itikafinsa ba, sai dai in akwai wata larura ta Shari'a, Ummina A’ishah رضي الله عنه ta ce, Manzon Allah ﷺ yakan zuro min kansa alhali yana cikin Masallaci, ni kuma ina ɗakina sai in wanke masa, saboda ba ya shigowa gida sai da wata buƙata idan dai yana I’itikafi. 
A wata ruwayar ta ce, sunnah ga mai I’itikafi kada ya je dubiyar mara lafiya, kada ya bi rakiyar kai mamaci Maƙabarta, kada ya shafa mace, kada ya rungumeta, kada ya fita sai idan da wata larura a lokacin da yake I’itikafi.

Yakamata jama’ar da za su yi I’itikafi a wani masallaci, ko kuma hukumar da take kula da masallacin da aka san za a yi I’itikafi a cikinsa, su tabbatar da sun kula da abubuwa muhimmai kamar guda shida, domin ɗorewar I’itikafin da kuma gamsar da masu ibadar da za su haɗu a masallacin kamar haka: 
1. A kafa wani kwamiti na musamman wanda zai tsara yadda I’itikafin zai gudana wajen tantance adadin mutanen da za su yi I’itikafi a wannan masallacin a wannan Shekarar. 
2. Ya kamata a samar da wani (form) da za a ba wa duk mutumin da yake son yin I’itikafi a wannan masallacin, ya cike shi ta hanyar rubuta sunansa, sunan wakilinsa, sunan unguwarsu, sunan sana’arsa, sunan layinsu, lambar wayarsa in yana da ita, da ta wakilinsa, 3. A kuma tantance lafiyarsa, domin kada ya zamo yana ɗauke da wata cutar da za a iya ɗaukarta a cikin jama’a. 
4. A tabbatar mai I’itikafi ya tanadi duk wani abin guzuri da zai yi amfani da shi a cikin I’itikafinsa, wanda ya haɗa da abincinsa, abin shansa, sabulunsa na wanka da na wanki, da ‘yar tabarmarsa, ko dardumarsa, da zai kwanta a kai da abin goge bakinsa, da makamantansu. 
5. Samar da cikakken tsaro mai ƙarfi ta hanyar samar da masu gadinsu dare da rana ta yadda za a raba masu gadin biyu, wato masu aikin dare da masu aikin rana su kuma sa ido sosai. 
6. Tanadar abubuwan da za su sanyaya masallacin, kamar fankoki, da kuma tanadar man da za a zuba a inji idan babu wutar lantarki a dare da rana saboda samar da wadataccen haske. 
7. Kula da tsaftace masallacin ta hanyar share shi, da goge shi, da kuma sanya turare da abubuwan sa ƙamshi, Allah ﷻ shi ne masani.
Allah ya sa mu dace. 
* * * *

Post a Comment

0 Comments