GYARAN FUSKA DA FATA,CIKIN SAUKI.
☏+2348037538596 or ☏+2348066627317
MUNA DA SABULUN GYARAN JIKI ( SKIN CARE ).
■ gyaran fata.
■ haske fata.
■ maganin kuraje.
a yau zamuyi bayani game da gyarna fata, musamman masu fama da yawan kananan kuaraje da yawan gumin fuska da maiko na fuska.
Ga duk mai son rabuwa da wandan nan matsalolo ga hanya ingantacciya,wacce bata da wata illa,kuma ba tare da kashe wasu kudade ba,domin wasu masu son gyaran fuska da fata suna amfani da mayukan da suke dade fata wadan kuma suna da illoli sosai ga lafiyar fata.
Ga wasu hanyoyi Guda 3 wadda kowacce idan akai amfani da ita za'a samu Nasara.
HANYA TA FAFKO.
ZA'A NEMI.
1. Lemon tsami
2. Zuma
Da farko za'a matse lemon tsamin a cikin wani abu kamar roba,sai a zuba Zumar a ciki a cakuda sosai sai a shafe fuska da shi na tsawon minti 15 kafain wanka,sannan a wanke da ruwan dumi a shafa man Zaitun a fuskar.
HANYA TA BIYU.
ZA'A NEMI.
1. Danyen kwai
2. Zuma
Da farko zaa fasa kwan amma iya farin ruwan kwan banda kwandowar,sai a kawo Zuma a zuba a cakuda sosai a shafe fuska na tsawon minti 15 kafain wanka sai a wanke da ruwan dumi.
HANYA TA UKU.
ZA'A NEMI.
1. Tumatur(Tomato)
2. Lemon tsami
3. Zuma.
Da farko zaa matse lemon tsamin a runa, sannan a matse Tumatur shima a ciki sai a kawo Zuma azuba a ciki a huya sosai sannan a shafe fuska da shi na na tsawon minti 10 kafun wanka sanan a wanke da ruwan duni.
Dukkan kowacce hanya da zaka gwada zakayi na tsawon sati daya ko biyu gwargwadon yadda kake son fatar taka tayi kyau.
🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼
✨ WASU HANYOYIN GYARAN FUSKA✨🧼
⇒ _Za a iya hadin ruwan lemun tsami da na zuma sannan a shafa a fuska ko jiki, domin inganta hasken fata da karfafa fatar jiki da kuma hana fesowar kuraje._
⇒ _Akwai hadin ayaba da kwaiduwar cikin kwai da man zaitun. Idan aka yi wannan hadin, sai a shafa a fuska na tsawon minti ashirin sannan a wanke, shi ma wannan hadin domin gyaran fatar jiki da kuma na fuska ne._
⇒ _Hadin ruwan lemun zaki da ruwan kwai da kuma kurkum na da matukar muhimmanci sosai domin yana taimakawa wajen gyaran fata, musamman ma ga amare._
⇒ _Garin bawon lemu wanda sai an busar sannan a daka a tankade sannan a hada da ‘baking soda’ shi ma yana magance cututtukan fata sosai._
⇒ _Akwai hadin ruwan kwakwa da garin bawon lemun zaki da kuma madara. Wannan irin hadin na sanya fata sulbi sosai._
🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼
SABULUN WANKA NA GYARAN JIKINKI AMARYA:
☏+2348037538596 or ☏+2348066627317
Kaduna- Nigeria
_domin samun naki sabulu
Za ku iyayin wannan ma:
1. Kur-kur
2. Dilka
3. Zuma kwai
4. Lemon tsami
Za ku hade su a guri guda ku samu ruwan ku kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ku shafe fuskanku, idan kuma har da jiki kuke so, sai ku shafa harada jiki bayan awa daya sai ku shiga wanka za k ga yadda jikinku zai goge. Das da izinin Allah. Domin wannna hadin shi ake kira Dalleliya.
Ga kuma wani hadin har wayan na gyaran fatan jiki zaku tanadi:
1. Lalle
2. Kwaiduwar kwai 3
3. Manja cokali 3
4. Kur-kur
Sai ku kwaba su guri guda ku shafe jikinku zuwa awa guda, sai ku yi wanka da ruwa zalla sai ku jika duka da ruwan dumi ku shafe jikin da ita sai ku kuma yin wanka.
Allah ya taimake mu.
☏+2348037538596 or ☏+2348066627317
Sɪʀʀɪɴ ʀɪᴋᴇ ᴍɪᴊɪ
0 Comments