MENENE AZUMI


An haramta ma Musulmai ci da sha da jima'i tun daga bullowar rana wato Fajr har zuwa faduwar rana maghrib. Musulmi na da damar yin dukkan abubuwan da aka haramta masa da rana tun daga faduwar rana har zuwa lokacin fitowar Al'fijir. Azumi na taimaka ma musulmi wajen kara kusanci da Allah da kuma tsoron Allah. Sannan musulmai na kara gane kyautar Allah a gare su sakamakon abubuwan da suka sabayi na Al'ada kuma na dole kamar ci da sha da kusantar iyali amma sakamakon azumi dukkan wadanan an haramta masu su. Anan ne musulmai kan farga da irin halin da wadanda basu da wadata kan shiga na rashin ci da sha.

Ma'anar azumi ba wai kawai hana bukatun dan'adam na al'ada bane ba kadai a'a harma da yana taimakama dan'adam wajen yin ainahin biyayya ga Allah da kara tsoron Allah da biyayya ga manzon Allah (s.a.w) da kuma kara lafiyar jiki da tattalin arziki da kara sada zumunci.

 Azumin Wajabci na Watan Ramadana Gyara
Akwai abubuwan da ayar Kur'ani ta [2:187] ta baiyana a kaurace masu yayin azumi kamar: Abinci, abin sha, da kuma kusantar iyali. Sannan akwai kari kan haka wanda Shari'a ta baiyana a kaurace masu kamar (Girman kai, mummunan kalami, fada, gulma, da sauran su). Idam musulmi ya kasance yana aikata koda daya daga cikib wadannan ne to azumin sa ka iya lalacewa. Musulmai an umarce su ne da yin sadaka da taimako ga mabukata a cikin watan Ramadana ko kuma yayin azumi. Daga Kur'ani da Sunnah dukkannin wanda yanayi na rashin lafiya ya kaishi ga bazai iya azumi ba ko matafiyi wanda yake yin tafiyar da shari'a ta amince kuma halin tafiya yasa bazai iya azumi ba, to wadannan zasu yi kokarin su rama azumin da ya kubuce masu. Amma kuma wanda wata cuta wadda an kasa shawo kanta ke damunsa to wannan zai nemi shawarar masana lafiya ne idan har sun bashi tabbacin zai iya yin azumi to lallai azumi ya wajaba a kansa, amma kuma idan likitan ya fada masa cewa hin azumin ka iya zama sila ta karuwar larurar tasa to wannan hukuncin sa shine ya ciyar da mutane na ko kuma wani mutun guda na tsawon kwana talatin ko kuma ashirin da tara gwargwadon dai yadda watan yayi.

Shiri'ar Musulunci ta haramta azumi ga matar da take jinin al'ada har sai lokacin da jinin ya dauke to sai ta yi wanka kuma taci gaba da azumi. Sannan wannan azumin daya kubuce mata to zata rama shi kafin dawowar wani ramadanan. Wani malamin Musulunci a kasar Amurika Nouman Ali Khan yace "hanin yin azumi ga mata masu al'ada yana da nasaba ne ga lafiyar su domin musulunci ne kadai ke kare lafiyar mabiyansa". Amma kuma matan masu al'ada ka iya cigaba da yin zikirori da adduo'in su.

Azumi ya wajanta ga wanda ya hada wadannan abubuwa guda biyar din

Musulmi ko Musulma
Baligi ko Baliga
Zai iya ko zata iya azumin (wato babu wata larura wadda shari'a ta amince zata sa a dakatar da azumi).
Mazaunin gida (wand ba matafiyi ba)
Wanda baya daga cikin wadannan Mai tsohon ciki, Mara lafiya, Mai babban rauni, Mai shayarwa.
Karya azumi Gyara
Idan mutum cikin halin mantuwa yaci ko yasha ko ya kusanci iyali yayin kuma da yake azumi to hukuncin sa shine zai rike wannan azumin wato ya karasa wannan ranar ba tare da aikata dukwani abinda zai karya azumi ba kuma zai rama shi bayan watan azumi. Amma kuma mutumin da yakasance yana sane ya ci ko yasha ko ya kusanci iyalin sa to wanna ga abinda shariar musulunci ta ce a kansa,

Zai yanta bawa, idan ba hali to
Zai azumci wata biyu, shima idan ba hali to
Zai ciyar ko ya tufatar da mutun sittin.

Jerin Abubuwan dake karya azumi

Cin abinci da gangan
Shan abin sha da gangan.
Saduwa da mace da gangan.
Kakaro amai da gangan
Fasa niyar azumi.
Rashin dauko niyya tun dare ga mai azumin farilla.
Zuwan jinin Al’ada ko na haihuwa ana cikin azumi.
Shafar gaba da sha’awa, Ko kallo, Da shaawa, Ko tunanin mace da sha’awa, Har maniyyi ya fito.
Yin ridda da fita musulunci.
Yin Allurar Abinci.

Post a Comment

0 Comments