Daga Umar Idris Bin Jauro, Jos
Mata da dama sukan fuskanci ƙalubale a farkon lokacin fara al'adar su, saboda rashin samun ilimi ko wayewa ga sabon yanayin da suka samu kansu a ciki, musamman matan mu na Hausawa.
Da yawa daga cikin ƴan uwa mata lokacin da suka fara al'ada basu san mecece ita Al'adar ba, balle su san sharuɗɗanta, dokoki da kuma hukunce-hukuncenta ta fuskar addini.
Domin iyayen mu mata basa zaunar da su su nusar da su hakan, duk da kasancewa hakkin ƴaƴan a kansu yake. Da yawa daga cikin irin waɗannan iyaye suna alaƙanta rashin sauke wannan haƙƙin nasu na yaran su mata da jin KUNYA.
Wata daga cikin irin waɗannan yaran mata da na samu zantawa da ita a kan wannan matsalar ta shaida min cewa, a lokacin da ta fara ganin jini a jikin ta bata ɓata lokaci ba ta sanar da mahaifiyarta, amma abin mamaki mahaifiyar tata ta ce da ita ba komai, ba wani matsala ba ne.
Sai dai kash, daga nan bata sake ce mata komai ba. Ballantana ta zaunar da ita ta fahimtar da ita cewar yanzu ta balaga, kuma ga yadda ya kamata ta kula da tsaftar jikin ta, da kuma kiyaye hukunce hukuncen addini game da wannan sabon yanayi da ta shiga. Duk wai saboda KUNYA.
Haƙiƙa kunya tana daga cikin Imani, amma ya kamata iyaye mata su san da cewa, sanar da ƴaƴan su mata abin da ya shafe su, da matsayinsu na mata haƙƙi ne a kan su. Wanda ya zama wajibi su sauke idan ba za su iya ba, za su iya tura su wajen wata malamar unguwar su ko wata ƴar uwarta ko ƙawar ta, ko makusanciyarta, domin a wayar da kan ƴar tata.
Kamar yadda na baku labarin wannan baiwar Allah, haka mahaifiyarta ta kasa sanar da ita. Ƙarshenta wata ƙawar ta ce ta sanar da ita a makaranta, alhalin kuwa a irin shekarun ta, ba lallai ne ta iya wayar mata da kai ɗari bisa ɗari ba kamar in da a ce mahaifiyar ta ce za ta yi, wanda ita ce ta san zafin ta fiye da kowa a faɗin duniya.
Da fatan iyayen mu mata za su gyara, Allah kuma Ya datar da mu da alkhairi.
*Malam Umar Idris bn Jauro, marubuci ne dake zaune a garin Ɓukur, kuma shi ne shugaban reshen Ƙungiyar Arewa Media Writers a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, da ke Jihar Filato
💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
Shirin Bada Ƙanƙarar Ruwa domin masu Azumi
Ku bada Sadaƙar Naira Ɗari biyar ₦500 kachal domin taimaka wa Bayin Allah yayin Buda Baki.
Za'a riƙa sayen a ƙallah Ƙanƙara ta Naira Dubu Biyu ƙosai na Naira Dubu Ɗaya kowace rana a rabama Mabukata domin rage radadin wannan zafin rana da muke ciki.
Ku bada taku Gudummuwar ta Lambar Asusun ajiya kamar haka:
Account number: 7810335410, Bank name: WEMA BANK, Account name: Sirrin rike miji
Allah yasa mudace ya Karbi Adduo'in mu da Ibadun mu yasa mudace da Alkhairan dake ciki wannan watan Mai Alfarma Amin.
Share ma sadaka ce 💧💧💧💧💧💧
0 Comments