Daga Rabi Ahmad Mu'azu, Jos
Na yi tunanin yin wannan rubutu ne domin faɗakar da 'yan uwana mata, musamman 'yan mata da zawarawa, game da wata sabuwar fitina da ta kunno kai da sunan yayi. A daidai lokacin da al'ummar Musulmi ke fafutukar neman abin da za su ci da iyalan su, cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, da abin da za a yi wa iyali ɗinkin Sallah.
Ga duk mai bibiyar abubuwan da ake tattaunawa a kafafen sadarwa na zamani wato zaurukan sada zumunta na Soshiyal Midiya, zai lura da yadda matasa suka shagala da batun sabuwar suturar yayi ta mata da ake sa ran yayin ta a lokacin ƙaramar sallah mai zuwa, wato Abaya. Masu nuna kwaɗayin su ga samun wannan riga, da masu ganin bai dace mata su ɗaga hankalinsu kan lallai sai sun mallaki Abaya, don kece raini a sallah ba.
Babban abin tambaya a nan shi ne menene manufar ƙirƙirar wanann sabon salon ado na yayi? Mai ya sa kuma ya ja hankalin musamman mu mata?
Abaya fa ba wata baƙuwar sutura ba ce da aka fara ta yau, mata sun jima suna sanya Abaya tun ma lokacin ba ta zama gama gari ba. Idan za mu iya tunawa a baya can daga wasu ƙasashen Musulmi na duniya ake shigo da ita, don haka ta zama sai wance da wance. Ina iya tunawa lokacin akwai Dubai Abaya ko Turkey Abaya da sauran su, waɗanda sai kin yi oda kin biya webil na jirgi kafin ta iso miki. Ba kamar yanzu da ta zama gwanjon Kano ba, inda ake samun teloli na gida suna satar fasahar na waje suna dinkawa ba.
An fara maganar Abaya ɗin nan cikin wannan wata na Ramadan ne, inda mata suka fara ɗaga hankalin su a kan irin shigar kece raini da za a yi da sallar nan, abin da ya kawo batun yayin Abaya da za su yi.
Wai mai ya sa komai idan za a yi wanda ake so shaiɗan ya samu nasarar kaɗa gangar shi sai dai a saka mata a sahun gaba, saboda mune tunanin mu ragagge? Don mu ne za mu iya yaɗa abu kamar wutar daji ko? A gefe guda kuma sai aka samu wasu mazan da suke ƙara ingiza su, suna zolayarsu.
Ni dai ban ga wata wayewa a kan batun saka Abaya ba. Idan kin sa kin burge wasu wallahi wasu ba za ki burge su ba, don su sun daɗe da daina yayin ta. Kowa da inda Allah ya ajiye shi, kada fa mu takura sai mun kai kan mu inda Allah bai kai mu ba. 'Yar uwa, a yadda rayuwar nan take wasu ma lafiya suke nema ba su samu ba, wasu abincin ma da za su yi buɗa baki gagarar su yake yi!
Mutuncin ki da darajarki ya fi Abaya ɗari wallahi, idan har ya zube a kan maula da wayo to, tabbas ya tafi tafiya ta har abada, a lokacin da Abayar ta daɗe da zama tsumma!
A wannan lokaci da ƙasar mu ke fama da ƙalubalen tsaro da na tattalin arziƙi, maimakon mu mayar da hankali wajen dagewa da addu'a da neman gafarar Allah sai faman shirme muke yi, muna kashe lokacin mu da kuɗaɗen mu wajen yin muhawarar da ba za ta amfane mu ba.
Ba wai ina nufin kar a yi raha ba ne, amma mu taƙaita don Allah. Wallahi wasu matan sun ɗauki maganar Abayar nan kamar abin nan na ko a mutu ko a yi rai, sun sa shi a ransu kamar wani abin dole. Wai har wata na yi wa wasu gori da cewa, duk wacce ba ta sa Abaya a sallar bana ba, 'yar ƙauye ce!
To, ke da ki ke cewa wata 'yar kauye ce ke kuma Babbar Yarinya kin saka Abayar Dubu 22 to, akwai wata mai less ko shaddar Dubu 30 ko fiye da haka amma ba ta fariya.
Ya kamata 'yan uwa mata mu dinga yi wa kan mu faɗa tun kafin a yi mana. Wallahi masu zuga mu ma sai dai su mayar da mu sakarai su koma suna yi mana dariya. Don na tabbata wata garin neman kuɗin sayen Abaya sai ta sayar da mutuncin ta, a wurin da ba ta da sauran martaba da mutunci.
Ba a kan ki za a fara sa Abaya ba, kuma ba a kan ki za a daina saka wa ba! Idan kunne ya ji, gangar jiki ta tsira!!
*Rabi Ahmad Mu'azu ta yi wannan rubutu ne daga Jos, kuma ita ce Editan reshen ƙungiyar Arewa Media Writers na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato
0 Comments