ALAMOMIN CIWON SANYI DA MAGUNGUNA SU:
Waɗansu daga cikin alamomin ciwon sanyin mata da ake samu ta hanyar saduwa da namiji ko mace mai ɗauke da ciwon : (STD/STI):
1. Fitar ruwa daga farji, ruwa mai kauri ko silili, kalar madara ko koren ruwa daga farji.
2. Kuraje masu ɗurar ruwa da fashewa a farji , musamman wurinda pant ya rufe.
3. Feshin ƙananan ƙuraje a farji ko cikin farji
4. Raɗaɗin zafi a lokacin yin fitsari
5. Jin zafi cikin farji lokacin jima'i
6. Zubar jinin al'ada mai yawa ko zuwan jinin al'ada mai wasa, wato akan lokacinda ya saba zuwa ba
7. Ciwon mara
8. Zazzaɓi
9 . Ciwon kai
10. Murar maƙoshi/maƙogwaro
11. Kasala/raunin jiki
12. Zubar jini lokacin saduwa
13. Dakushewar sha'awa, ko rashin sha'awa ko ɗaukewar ni'ima
14. Bushewar farji
15. Ƙaiƙayin farji
16. Warin farji (ɗoyi) mai ƙarfi
17. Kumburin farji da yin jawur
18. Gudawa
18. Ko rashin ganin wata alama daga cikin wadannan alamomin da muka bayyana a sama.
Ki nemi wadannan
- Garin Lalle cokali 2.
- Garin ganyen Magarya cokali 2.
- Garin Raihan (rai-dore) cokali 2.
- Garin ganyen gasaya cokali 2. Optional (shi ba dole bane).
Za ki tafasa su baki dya da ruwa kofi biyu ko uku mai kyau. Idan ya tafasa kin sauke sai ki surka kwatankwacin yadda zaki iya zama ciki da dumi sannan ki rika shiga kina zama tsawon Minti 15.
Idan kin gama kin fito daga ruwan ki samo garin ganyen lalle cokali daya ki hadashi da Man Kadanya ki kwaba, ki rika shafawa a farjinki kuma kina yin matsi dashi.
In sha Allahu zaki dena jin wannan Qaikayin, kuma ruwan zai dena fito miki.
Sannan kuma ki rika dafa hulba tare da kustul Hindi kina sha. In sha Allahu sanyin zai bar jikinki baki daya har abada. Idan har kinyi wannan baiyi ba to gaskia akwai yiyuwar junnu ne....
Allah yasa mu dace.
0 Comments