Bawon ayaba yana kunshe da arziki na sunadaran gina jiki (nutrients) da kuma masu sanya karfin jiki (carbohydrates). Akwai ire-iren sunadaran vitamin B6, vitamin B12, magnesium da kuma Potassium wadanda suke da alfanu daban-daban ga lafiyar jikin dan Adam.
Ga jerin hanyoyi 10 da bawon ayaba ke inganta lafiyar jikin dan Adam:
1. Hasken hakori:
Goga bawon ayaba ga hakora sau daya a kullum har na tsawon sati guda ko da kuwa na minti guda ne, yana matukar kalkale hakora su fita tar kamar haksen walkiya.
2. Fitar da tusar jaki:
Mulka bawon ayaba yana taimakawa wajen ficewar tusar jaki da kuma hana bayyanar wat sabuwa a jikin dan Adam
Amfani 9 na bawon ayaba ga rayuwar Dan Adam
Amfani 9 na bawon ayaba ga rayuwar Dan Adam
3. A matsayin ci ma:
Ana amfani da bawon ayaba a matsayin abin ci, domin kuwa mutanen kasar Indiya sun gano cewar sanyawa dahuwar kaza bawon ayaba yana kara laushin tsokar ta kaza.
4. Waraka ga kurajen fuska:
Goga bawon ayaba ga kurajen fuska cikin minti 5 har na tsawon mako guda za a sha mamaki.
5. Rage yakunewar fata:
Hada bawon ayaba tare da kwanduwar kwai kuma a shafa ga fuska sannan a wanke da ruwa, ya na matukar warware fata ta yi luwai-luwai.
6. Sauki ga buguwa a jiki:
Shafa bawon ayaba ga wata buguwa ko wani ciwo na jiki yana taimakawa wajen rage radadin ciwon cikin gaggawa.
7. Waraka ga cutar makero:
Bawon ayaba ya na taimakawa wajen kawar da cutar makero wadda turawa suke kiranta da Psoriasis. Ya na kuma taimakawa wajen rage radadin kaikayi na makeron
8. Cizon kwaruka:
Shafa bawon ayaba akan cizo kamar na sauro yana dauke kaikayin zafin cizon
9. Kyalkyali:
Goga bawon ayaba ga fatar takalmi, jakar leda ko azurfa yana sanya su zamto cikin kyalkyali a koda yaushe.
0 Comments