Lada Da Sakamakon Yin Salati Ga Annabi ‎ﷺ




Yin salati ga Annabi ﷺ wajibi ne akan dukkan musulmai baki daya. Kuma hakkin Annabi ﷺ akan dukkan al'umarsa su yi masa salati, musammama idan an ambaci sunansa da ranar Juma'a da daren Juma'a da bayan kiran sallah, da dukkan lokacin da kasami lokaci.

Yin salati ga Annabi ﷺ yana da falala da lada mai yawa, babban ladar sa shine samun ceton Annabi ﷺ da samun kusanci da shi a ranar alqiyama da kuma sanin sunka a wajansa duk lokacin da ka yi masa salati.

KADAN DAGA CIKIN LADA DA SAKAMAKON SALATI GA ANNABI ﷺ

1-Wanda yayi masa salati guda daya Allah zai yi masa guda goma.
@[صحيح : رواه مسلم].

2-Manzon Allah ﷺ zai mayar da sallama da salati ga dukkan wanda ya yi masa.
@[حسن : رواه أحمد (٢٥٧/٢) ، وأبو داود(٢٠٤١) ، وحسنه الألباني في " صحيح الترغيب" ( ١٦٦٦)]

3-Allah yana sanyawa a isar da salatinka zuwa ga Manzon Allah ﷺ.*
@[صحيح : رواه رواه النسائي في " عمل اليوم والليلة"(٦٦) ، وابن حبان في " الصحيح" (٩١٤) ، وصححه الألباني في "صحيح الترغيب"(١٦٦٤)].

4-Ana bujirowa Annabi ﷺ salatin dukkan wanda yayi salati a gare shi.
@[صحيح : رواه أحمد(٤/٧) ، وأبو داود(١٠٤٧) ، وابن ماجه (١٠٨٥) ، وابن حبان (٩٠٧) ، والحاكم (٢٧٨/١) وصححه].

5-Wanda ya yawaita salati ga Manzon Allah ﷺ, Allah yana yaye masa bakin ciki kuma ya gafarta masa zunubansa*.
@ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ : ﺣَﺪِﻳﺚٌ ﺣَﺴَﻦٌ ﺻَﺤِﻴﺢٌ . ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻟﻤﻨﺬﺭﻱ ﻓﻲ ‏( ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ ‏) ، ﻭﻛﺬﺍ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﻓﻲ " ﺍﻟﻔﺘﺢ " ‏( 11/168 ‏) ، ﻭﺃﺷﺎﺭ ﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﻓﻲ " ﺍﻟﺸﻌﺐ " ‏( 2/215 ‏) ﺇﻟﻰ ﺗﻘﻮﻳﺘﻪ ، ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ " ‏( 1670 ‏) ﻭﻏﻴﺮﻩ

6-Wanda ya yawaita salati ga Annabi ﷺ,yana samun ceton Annabi ﷺ, a gobe alqiyama*. 
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﻗﺎﻝ : ﺣﺪﻳﺚ ﺣﺴﻦ ‏)

7-Mai yawaita salati ga Annabi ﷺ, yana samun lada mai yawa domin za a rubuta masa lada goma kuma a kankare masa zunubai guda goma kuma a daukaka darajarsa sau goma*.
@صحيح الجامع

Wannan kadan kenan daga cikin romon lada da ake samu cikin yiwa Manzon Allah ﷺ salati.

Allah ya bamu ikon yi masa salati ko kuma koyi da shi a cikin dukkan ibadar mu.

Post a Comment

0 Comments