FALALAR YIN AZUMI DA FA'IDODINSADARASI NA 6:




  Shi dai azumi yana da falala yana da darajoji masu girma a wajen Allah ﷻ ga wanda ya yi shi don Allah ﷻ. Azumi yana daga cikin manyan ibadu masu girma da Allah ﷻ ya tanadarwa masu yin sa a gobe qiyama, yana da fa'idoji muhimmai da suke riskar mai yin sa tun a nan duniya. 
Haka nan shi azumi yana daga cikin manya-manyan ibadu na ɗa'a ga Allah ﷻ waɗanda ake samun qarin kusanci ga Allah ﷻ da shi, domin yana samar wa mumini gagarumar ladar da shi kaɗai ya san iyakar lissafinta. 
Sannan ana samun kankarar zunubai saboda yin sa, kuma ana nesanta fuskar mutum ga barin shiga wuta. Kuma mai yin azumi yana samun wata alfarma da cancantar shiga Aljanna ta wata qofa ta musamman wadda ake kiranta RAYYAN, za a yi masa tanadinta. 
Sannan azumi yana faranta ran mai yin sa a ranar da zai gamu da Ubangijinsa ﷻ. Yabon da Allah ﷻ ya yi wa jerin wasu nagartattun mutane ciki har da masu azumi, inda yake cewa:
﴿ إِنَّ ٱلْمُسْلِمِينَ وَٱلْمُسْلِمَٰتِ وَٱلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَٰتِ وَٱلْقَٰنِتِينَ وَٱلْقَٰنِتَٰتِ وَٱلصَّٰدِقِينَ وَٱلصَّٰدِقَٰتِ وَٱلصَّٰبِرِينَ وَٱلصَّٰبِرَٰتِ وَٱلْخَٰشِعِينَ وَٱلْخَٰشِعَٰتِ وَٱلْمُتَصَدِّقِينَ وَٱلْمُتَصَدِّقَٰتِ وَٱلصَّٰٓئِمِينَ وَٱلصَّٰٓئِمَٰتِ وَٱلْحَٰفِظِينَ فُرُوجَهُمْ وَٱلْحَٰفِظَٰتِ وَٱلذَّٰكِرِينَ ٱللَّهَ كَثِيرًا وَٱلذَّٰكِرَٰتِ أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا۝﴾ () 
Ma’ana: “Haƙiƙa musulmai maza da musulmai mata; da muminai maza da muminai mata; da masu biyayya maza da masu biyayya mata; da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata; da masu haquri maza da masu haquri mata; da masu qasqantar da kai maza da masu qasqantar da kai mata; da masu sadaka maza da masu sadaka mata; da masu azumi maza da masu azumi mata; da maza masu kiyaye farjinsu da mata masu kiyaye farjinsu; da maza masu ambaton Allah da yawa da mata masu ambaton Allah da yawa; dukkaninsu Allah ﷻ ya tanadar musu gafara da lada mai yawa.” 
A wannan ayar, sai Allah maɗaukaki ya ambaci masu azumi a cikin jerin mutanen qwarai, don haka wannan kuwa falala ce mai girma. 
Azumi alkhairi ne ga mai yin sa. Allah ﷻ yana cewa:
﴿ وَأَن تَصُومُوا۟ خَيْرٌ لَّكُمْۖ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ۝﴾ ()
Ma’ana: “ku yi azumi shi ya fi alkhairi a gare ku idan da kun sani.” 
Mai yin azumi yana samun taqawa, wato zuzzurfan tsoron Allah ﷻ. Kamar yadda Allah ﷻ Yake faxa: 
﴿ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ كُتِبَ عَلَيْكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ ۝﴾ () 
Ma’ana: “Ya ku waɗanda kuka ba da gaskiya, an wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta a kan waɗanda suka gabace ku, (an yi muku haka ne) don ku kasance masu taqawa.”
Ashe mai yin azumi zai iya gamdakatar da samun tsantsar tsoron Allah ﷻ, wannan ma falala ce mai girma. 
Sannan azumi garkuwa ne ga mai yin sa. Wato azumin zai zame masa garkuwa, ta hanyar kare shi daga kamuwa da cututtukan zuciya da na gangar jiki. 
Sannan zai yi masa garkuwa ga barin shiga wuta a gobe qiyama. Saboda hadisin Jabir Bn Abdullah رضي الله عنه da Ma’aiki ﷺ yake faxar cewa, Allah ﷻ Ya ce: “Azumi garkuwa ne ga bawa da yake katange kansa da shi ga barin shiga wuta.” 
A hadisin Abu Hurairahh رضي الله عنه kuma Ma’aiki ﷺ ya ce, “Shi azumi garkuwa ne.” A wani lafazin kuma yana cewa, “Azumi nawa ne, ni nake yin sakayya ga wanda ya yi shi don ni.” 
A wani hadisin da zai ƙarfafi wannan, shi ne hadisin sayyidina Usman Bn Abil As رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Shi azumi garkuwa ne da bawa yake qoqarin kare kansa daga shiga wuta.”
Shi azumi ganuwa ce, ko wani kadarko ne da yake tsare mutum daga shiga wuta. Saboda hadisin Abu Hurairah رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Shi azumi wata katanga ce ko wata ganuwa ce da take tsare mai yinsa ga barin shiga wuta.”
Azumi yana zamewa mutum kariya daga rinjayar sha'awar varna, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Mas'ud رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ya ku taron matasa duk wanda ya sami ikon yin aure daga cikinku to ya yi, domin shi ya fi kaiwa matuqa wajen rintse ido da kiyaye farji, amma wanda duk bai sami ikon yin aure ba, to na hore shi da ya riqa yin azumi, domin azumin zai zame masa garkuwa da kariya.” () 
A ruwayar Abu Sa’id Al-khudri رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Duk wanda ya yi azumi saboda Allah ﷻ, to Allah ﷻ zai nisanta fuskarsa daga shiga wuta tsawon tafiyar Shekara saba'in (70).” () 
Haka nan yin azumi saboda Allah ﷻ yana nesanta mutum daga shiga wuta kwatankwacin nisan sama da qasa. 
Haka kuma, a wasiyyar da Ma’aiki ﷺ ya bari babu kamar azumi, kamar yadda yazo daga Abu Umamah Al-Bahili رضي الله عنه ya ce, ya Ma’aikin Allah ﷺ ka umarce ni da abin da idan na aikata shi Allah ﷻ zai amfane ni da shi. Sai Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ka riqa yin azumi, domin babu kwatankwacinsa. A wata ruwayar kuma ya ce, ka umarce ni da wani abu, sai ya ce, “ka riqa yin azumi, domin babu kamar azumi.” 
Wannan ya nuna mana irin falala da darajar da azumi yake da shi.
Azumi yana shigar da mai yin sa Aljannah ta wata qofa da ake ce mata, qofar Rayyan. Saboda hadisin Sahlu Ɗan Sa'ad رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Lallai haƙiƙa a cikin qofofin Aljannah akwai wata qofa da ake ce mata Arrayyan, babu mai shiga Aljannah ta cikinta sai masu yin azumi, da farko za a ce ina masu yin azumi? Sai su miqe sai a nuna musu ita, sai su shiga ta cikinta, babu wanda zai shiga aljanna ta wannan qofar sai su, to da zarar sun gama shiga sai a kulle ta, daga nan babu wanda zai shiga ta cikinta bayan su." () 
A wata ruwayar ta Imamul Bukhari a cikin babin siffar 'yan Aljannah ya ce, Ma’aiki ﷺ ya ce, “A cikin Aljanna akwai qofofi guda takwas, a cikinsu akwai wata qofa da ake kiranta Rayyanu, babu mai shiga ta wannan qofa sai mai azumi.” 
Abu Hurairah رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda ya ciyar da abubuwa guda biyu mabambanta saboda Allah ﷻ, to za a kira shi daga qofofin Aljannah ya shiga, sai a ce, ya kai bawan Allah ﷻ ga alkhairi nan. 
Haka kuma duk wanda ya zamo ya fi yawan yin sAllah, sai a kira shi ta qofar sallah, wanda ya fi yin jihadi sai a kira shi ta qofar jihadi.” () 
Wanda ya fi yawan yin azumi sai a kira shi ta qofar Rayyan, wanda ya fi yawan yin sadaka, sai a kira shi ta qofar sadaka.” 
Sai sayyidina Abubakar رضي الله عنه ya ce, na ba da Uwata da Ubana don su zama fansarka ya Ma’aikin Allah ﷺ lallai tabbas babu sauran wata damuwa ga wanda aka kira shi ta waɗannan qofofi. Shin za a iya samun wanda za a kira shi ta dukkanin qofofin nan gabaɗayansu? Sai Manzon Allah ﷺ ya ce, “Eh haka ne, ina fata kai ma kana daga cikinsu.” ()
Azumi yana da wasu Xabi'o'i, wanda ya haɗa su zai shiga Aljannah. Manzon Allah ﷺ ya tambayi Sahabbai رضي الله عنهم ya ce, “A cikinku waye ya wayi gari yana azumi?” Sai sayyidina Abubakar رضي الله عنه ya ce, ni ne. Sai ya ce, “Waye a cikinku ya ciyar da wani mabuqaci a yau? Sai sayyidina Abubakar رضي الله عنه ya ce, ni ne. Sai ya ce, “Waye a cikinku ya je dubo mara lafiya a yau?” Sai sayyidina Abubakar رضي الله عنه ya ce, ni ne. Sai Manzon Allah ﷺ ya ce, “Duk wanda waɗannan ɗabi'o'i suka haɗu a gare shi zai shiga Aljannah.” () 
Don haka wanda duk ya haɗa waɗannan ɗabi'u gabaɗayansu, lallai tabbas zai shiga Aljannah.”
Azumi kaffara ne ga zunubai. Huzaifatu Bn Yaman رضي الله عنه ya ruwaito cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce: “Jarrabawar mutum da ake yi masa a cikin iyalansa da dukiyarsa da ‘ya‘yansa da maƙwafcinsa, da kuma sallarsa da ya yi da azumin da ya yi da umarni da kyakkyawa da ya yi, da hani da mummuna da ya yi, dukkansu za su zamo dalilin kankarar zunubai a gare shi, da samun wani gwaggwaɓan lada mara iyaka ga duk mai azumi, saboda kasancewar shi mai azumi yana yin haƙuri da juriya na rashin ci da sha, shi ya sa Allah ﷻ zai ba shi lada mara iyaka saboda haƙuri da juriyar da yake yi a halin azumin. Saboda Allah ﷻ yana cewa:
﴿إِنَّمَا يُوَفَّى ٱلصَّٰبِرُونَ أَجْرَهُم بِغَيْرِ حِسَابٍ ۝﴾ ()
Ma’ana: “lallai (haƙiƙa tabbas) Allah ﷻ yana cika wa masu haƙuri ladansu ba tare da lissafi ba.”
Mai azumi yana da farin ciki guda biyu, na farko: farin cikinsa a duniya yayin da zai yi buɗabaki zai ji yana farin ciki. Na biyu: sai a ranar da zai gamu da Ubangijinsa ﷻ wato zai ga kyakkyawan sakamakon da zai faranta masa rai ita ce darajar shiga Aljannah. Warin bakin mai azumi ya fi turaren Almiski ƙamshi a wurin Allah ﷻ.
Kamar yadda Allah ﷻ Yake faɗa a cikin hadisil ƙudusi, inda yake cewa: “Duk wani aiki da Ɗan Adam zai aikata nasa ne, sai dai azumi shi wannan nawa ne, kuma ni zan ba da sakamakonsa.” 
Sannan azumi garkuwa ne, idan dai wani wuni ya zo da ɗayanku yake azumi a cikinsa, to kada ya yi kwarkwasa kada ya yi zolaya, idan kuma wani ya zage shi sai ya ce masa ni ina azumi, sai Ma’aiki ﷺ ya ce, wAllahi warin bakin mai azumi ya fi ƙamshin turaren Almiski.” ()
Azumi zai ceci mai yin sa a gobe ƙiyama. 
Haka nan Alqur’ani zai ceci wanda ya shagala da karanta shi a ranar ƙiyama. 
Saboda hadisin Abdullahi Ɗan Amru رضي الله عنه wanda Manzon Allah ﷺ yake cewa, “Da azumi da Alqur’ani za su yi ceto ranar Alƙiyama, shi azumi zai ce ya Allah ﷻ na hana shi ci da sha da sha'awar jima'i da rana, ka ba ni ceton sa, shi kuma Alqur’ani zai ce, na hana shi barci da daddare, ka ba ni ceton sa, sai Allah ﷻ Ya karɓi ceton su.” Wato sai Allah ﷻ Ya ba wa azumi da Alqur’ani ceton nasu.
Azumi yana kawar da nunkufurci, da gaba, da ƙiyayya, da waswasi daga cikin ƙirjin mutane. Kamar yadda hadisin mazaunin ƙauyen nan da ya zo daga ƙauye.
Da kuma hadisin Abdullahi Ɗan Abbas رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ka yi azumin watan haƙuri, shi ne azumin watan Ramadan, kuma ka riƙa yin azumin kwana uku a kowane wata domin shi azumi yana tafiyar da mummunan ƙulli daga cikin zuciya.” ()
Azumi ƙofa ce daga cikin ƙofofin alkhairi, kamar yadda ya zo a hadisin Mu'az Bn Jabal wanda Ma’aiki ﷺ yake cewa da shi, “Yanzu ba na nuna maka wata ƙofa daga cikin ƙofofin alkhairi ba?” Sai na ce, gaya min ya Ma’aikin Allah ﷺ, sai ya ce, “Azumi garkuwa ne, sadaƙa kuma tana gusar da saɓo kamar yadda ruwa yake kashe wuta.
Wanda ya mutu da azumi a bakinsa, ana sa ran zai shiga Aljannah kamar yadda ya zo a Hadisin Huzaifata Binil Yaman رضي الله عنه yake cewa, “Wanda ƙarshen kalmarsa ta zamo la'ilaha illAllahu, zai shiga Aljannah.”
Haka nan wanda ya yi azumi a wata rana domin neman yardar Allah ﷻ sai ya mutu yana wannan azumin, to shi ma zai shiga Aljannah. 
Haka kuma wanda ya mutu yana cikin ba da sadaka bayan ya gama bayar da sadakar sai ya mutu, kuma ya bayar da sadakar ne domin neman yardar Allah ﷻ, shi ma zai shiga Aljannah.
Allah ﷻ ya tanadi wasu tangama-tangaman gidaje masu benaye a cikin Aljannah, ya kuma tanade su ne ga masu yin azumi, suke kuma ciyarwa, suke tausasa magana, suke yaɗa sallama ga waɗanda suka sani da waɗanda ba su sani ba, suke yin sallah da daddare a lokacin da mutane suke barci. 
Saboda hadisin Abu Malik Al’Ashja’i رضي الله عنه inda yake cewa, a cikin Aljannah akwai wasu ɗakuna ana gano cikinsu ta bayansu, kuma ana gano bayansu ta cikinsu. 
Wato ana gano mutanen cikinsu ta baya, su kuma na ciki suna gano waɗanda suke wajen ɗakin, ma’ana dai kamar gidan gilashi. Allah ﷻ ya tanade su ne ga wanda yake ciyar da mutane abinci, yake kuma tausasawa a wajen yin magana, yake yawaita azumi, yake yaɗa sallama, da kuma yin sAllah da daddare a lokacin da mutane suke barci. 
Ana amsa addu'ar mai azumi wato idan mutum yana azumi Allah ﷻ ba ya mayar da addu'arsa baya, ma’ana ya ƙi karɓa. 
Saboda hadisin Abu Hurairah رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Mutane uku ba a mayar da addua'rsu shugaba mai adalci, mai azumi har sai ya sha ruwa, da kuma wanda aka zalunta. Allah ﷻ yana ɗaga waɗannan addu'o'in ana ɗaukar su a kan girgije, kuma za a buɗe musu ƙofofin sama. Allah ﷻ Yana cewa: “Na rantse da girmana, da buwayata, sai na taimake ki (ita wannan addu’ar, ko shi wanda aka zalunta) ko bayan wani lokaci ne.” () 
A daidai lokacin da mai azumi zai yi buɗabaki a nan ma ana karɓar addu'a, kamar yadda ya zo a hadisin Abdullahi Ɗan Amru Ɗan As رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Lallai shi mai azumi a sanda zai sha ruwa yana da wata addu'a wacce ba a dawo da ita.”
Idan ka ba wa mai azumi abin da zai yi buɗabaki ko ya yi sahur da shi, daidai yake da kamar kai ma ka yi azumin. Manzon Allah ﷺ ne ya faɗi hakan a hadisin Zaidu Bn Khalid Al-Juhani رضي الله عنه inda yake cewa, “Wanda ya ba wa mai azumi abin buɗabaki ko abin sahur, Allah ﷺ zai ba shi lada kwatankwacin azumin wanda ya ciyar ɗin.” () 
Wato idan ya ciyar da mutum goma za a ba shi ladan azumi goma, idan ɗari ya ciyar a ba shi ladan azumi ɗari.
Misali, kamar mai aikin hajji an hana shi ya aske gashin kansa matuƙar dai yana cikin harama, sai dai idan wata larura ce ta same shi a kan, sai ya aske kan sannan ya yi kaffara da yin azumi kamar yadda Allah ﷻ ya ce:
﴿فَإِنْ أُحْصِرْتُمْ فَمَا ٱسْتَيْسَرَ مِنَ ٱلْهَدْىِۖ وَلَا تَحْلِقُوا۟ رُءُوسَكُمْ حَتَّىٰ يَبْلُغَ ٱلْهَدْىُ مَحِلَّهُۥۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ بِهِۦٓ أَذًى مِّن رَّأْسِهِۦ فَفِدْيَةٌ مِّن صِيَامٍ أَوْ صَدَقَةٍ أَوْ نُسُكٍۚ فَإِذَآ أَمِنتُمْ فَمَن تَمَتَّعَ بِٱلْعُمْرَةِ إِلَى ٱلْحَجِّ فَمَا ٱسْتَيْسَرَ مِنَ ٱلْهَدْىِۚ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٍ فِى ٱلْحَجِّ وَسَبْعَةٍ إِذَا رَجَعْتُمْۗ تِلْكَ عَشَرَةٌ كَامِلَةٌۗ ذَٰلِكَ لِمَن لَّمْ يَكُنْ أَهْلُهُۥ حَاضِرِى ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِۚ﴾ ()
Ma’ana: “Idan aka tsare ku, sai ku yanka abin da ya sawwaƙa na hadaya, kada ku aske kawunanku har sai hadayar ta isa wurin yankanta. Wanda ya kasance mara lafiya daga cikinku, ko kuma yana da wani ciwo a kansa da zai sa shi yin aski to sai ya fanshi kansa da yin azumi ko sadaka, ko kuma yanka. Idan kuma kuka aminta cewa ba za a tsare ku ba, to wanda ya yi Tamattu'i da yin umara a cikin watannin aikin hajji, sai ya yanka abin da ya sawwaƙa na hadaya, wanda kuwa bai sami abin yankan ba, sai ya yi azumin kwana uku daga cikin kwanakin aikin hajji, sai ya yi bakwai idan kun komo gida, ya zama goma daidai kenan. Wancan shi ne hukuncin wanda iyalinsa ba su kasance mazauna harami ba.” 
Haka nan kuma azumi yana zama kaffara ga wanda ya yi kisan kai bisa kuskure, kamar yadda Allah ﷻ yake cewa:
﴿فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ تَوْبَةً مِّنَ ٱللَّهِۗ﴾ ()
Ma’ana: “Wanda bai sami ikon yin hakan ba, sai ya yi azumin wata biyu a 
jere a jere, don neman yafewar Allah ﷻ .”
    Azumi yana zamowa kaffarar farauta ga wanda ya yi harama da hajji ko umara, kamar yadda Allah ﷻ yake cewa:
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَقْتُلُوا۟ ٱلصَّيْدَ وَأَنتُمْ حُرُمٌۚ وَمَن قَتَلَهُۥ مِنكُم مُّتَعَمِّدًا فَجَزَآءٌ مِّثْلُ مَا قَتَلَ مِنَ ٱلنَّعَمِ يَحْكُمُ بِهِۦ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ هَدْيًۢا بَٰلِغَ ٱلْكَعْبَةِ أَوْ كَفَّٰرَةٌ طَعَامُ مَسَٰكِينَ أَوْ عَدْلُ ذَٰلِكَ صِيَامًا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمْرِهِۦۗ عَفَا ٱللَّهُ عَمَّا سَلَفَۚ وَمَنْ عَادَ فَيَنتَقِمُ ٱللَّهُ مِنْهُۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ ذُو ٱنتِقَامٍ۝﴾ ()
    Ma’ana: “Ya ku waɗanda kuka ba da gaskiya, kada ku kashe abin farauta alhalin kuna cikin harami, duk wanda ya kashe shi daga cikinku da gangan, (zai biya) ramuwar gwargwadon abin da ya kashe na daga dabbobin gida, mutum biyu ne adalai daga cikinku za su yi masa hukunci, ya zamanto hadaya ce mai isa ka'aba, ko kuma ya yi kaffarar ciyar da miskinai, ko kuma ya yi azumi daidai da yawan wuɗannan abin ciyarwar, (an yi masa haka ne) domin ya ɗanɗani sakamakon aikinsa, Allah ﷻ kuma ya yi afuwa ga abin da ya shige, wanda kuma ya sake aikata hakan to Allah ﷻ zai yi masa uquba, Allah ﷻ mabuwayi ne ma'abocin uquba ga wanda ya saɓa masa
Allah ya bamu dacewa.

Post a Comment

0 Comments