KU KUNSAN AMFANIN AZUMI GA LAFIYAR JIKIN DAN ADAM KUWA?



ANFANIN AZUMI GUDA 5 WANDA YA KAMATA KU SANI.

Idan ka karanta ka tura zuwa sauran yan uwa domin su amfana bakali daya

Azumi kamar yadda muka sani na da amfani ga kiwon lafiya da dama, duk da cewan wadannan alfanu kan karawa mutane karfin guiwan yin azumi, mabiya addinin Islama na azumta wata daya da wasu na sunna bisa ga umurnin Allah da sunnan manzonsa ﷺ .

Malaman kimiyya wadanda bas u da alaka da addinin Musulunci sun binciko amfanin azumi ga lafiyar jikin dan Adam akalla guda biyar kamar yadda zamu zayyanasu a kasa:

1. Azumi kan hana mutum samun ciwon siga

Azumi kan zama wani kafa na rage takuran sinadarin ‘Calorie’ wanda kuma zan rage yiwuwan samu ciwon siga. (Barnosky et al., 2014)

2. Azumi kan taimaka wajen rage kiban jiki

Azumi kan taimaka wajen rage kiba kuma ya kan kara konewan abinci da kasha 3.6% zuwa 14%. (Mansell, 1990).

3.Azumi kan hana tsufa da wuri

Azumi kan rage tsufar jiki kuma ya kan sa mutum ya dade a duniya cikin cikakken koshin lafiya (Mattson and Wan, 2005)

4.Azumi na kara kaifin kwakwalwa

Azumi kan kara girman sinadarin jiki wanda zai taimaka wajen kara kaifin kwakwalwa. (Lee et al., 2000)

5.Azumi kan kara girman na’urar jiki wanda akafi sani da ‘Hormone’

Wallahu a'alamu



LIKE AND SHARE ➡️

Post a Comment

0 Comments