Idan Namiji Yana Miki Wadannan Abubuwan Dagaske Yake Sonki:




Ga wasu alamun da mata zasu iya fahimtar masu cewa suna son su da aure, da gaske suke yi ba yaudaran su suke yi ba.

Sai dai wannan bazai hana mayaudari yin amfani da wadannan Alamomin ba domin cika burinsa na yaudara. Don haka sai a rika lura ana cire son rai a soyayyar aure ana hadawa kuma da addu'ar neman tsarin daga mayaudaran maza.

1: Rashin yin nesa da kai. Na mijin dake sonki da gaskiya ba zai taba yin nesa dake ba ta yadda za a iya yin kwana biyu ba tare da jin duroyar sa ba.
Koda kuwa Bako gari daya zai rika samun lokacin a kullum yana kokarin ji da kuma sanin lafiyar ki.

2: Zai kare ki: Ba ma kawai kare ki daga abunda zai iya cutar dake ba na zahiri. Namiji mai son ki na gaskiya a duk inda yaji ana neman taba mutuncin ki ba zai iya hakurin juriyar saurareba ba tare da ya tare miki ba.

Haka kuwa muddin wani ya nemi cutar dake a zahiri kuma a gaban sa muddin na miji mai son ki ne sai fa inda karfin sa ya kare.

3:Yana ajiye hidimarsa saboda taki: Namijin dake tare da soyayarki yakan iya hakura da wani hidimar dake gaban sa ya zo ya saurari kiranki ba tare da ya baki wani uzuri ba.

4: Kice Tuninsa: Idan har namiji na sonki to a kullum da kuma kowani lokaci kece a ransa. Hakan zai iya sa ya sadaukar da wani abun domin ya saka ki farin ciki.

5: Zai rika shawara dake: Idan Namiji na sonki akwai wasu shawarwarin da tare zaku yi dashi.
Namijin dake sonki bazai taba yin wani abunda yasan zaki ji a wajen wasuba ba tare da ya fadamiki ko yayi shawara dake ba.

6: Cika Miki Burin ki :Idan Namiji Yana sonki da gaske zai rika yi miki yadda yake son nan gaba ko kuma a yanzu rayuwar ki ya kasance.

Zai rika yin duk wani kokari domin ganin ya tallafa miki akan abunda kike yi ko kike son yi domin kyautata rayuwar ki nan gaba.

7: Bai manta abunda ya shafeki: Muddin ba ciwon mantuwa bane da shi. Idan Namiji na sonki ba ya manta duk wani abunda ya shafe ki ko kuka yi magana akansa komai kankantar abun yana ransa bazai ce miki ya manta ba.

8: Yana Son Kasancewa Tare Dake: A kullum namij mai sonki burinsa yaga cewa baki masa nisa ba. Bazai so a kwana a wuni bai nemi ganin ki ba.

9: Yabonki : Shi namij mai son ki duk dan kankantar abunda kika masa ya rika Yabonki kenan.

10: Hakuri Dake: Idan namiji yana sonki zai rika hakuri da wasu kurakurenki.

11: Saki Farin Ciki: A kullum burin namij mai son budurwa sa shine yayi duk abunda zai yi wajen faranta mata rai a koda yaushe.

12:Yana Kishin ki: Namiji mai sonki a kullum tattare yake da kishin ki a zuciyar sa na rashin son ganin ki da wani ko zullumin kada ya rasa ki ta hanyar wani Saurayin. Don haka a kullum yana kokarin saka miki ido domin magana akan abunda bai gane ba. 


Post a Comment

0 Comments