HAKKOKIN MIJINKI AKAN KI



💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐

Hakkin miji abune me girman gaske, kisani miji ba abun wasa bane. Bayan ubangiji inda da akwai wanda za aima sujjada toh da macece za'a nemi taiwa mijinta

■ Wajibine ki girmama mahaifan mijinki, domin su suka haifa har kema kika samesa amatsayin miji ayau.

■ Wajibine ki girmamashi komi talaucinsa. Domin bashi ya za6i ya zauna haka ba ubangiji ne ya tsara masa. Haka karkiga yana da hakuri kice zakike fadamasa maganganu na raini da wulakanci ko yar wacece ke kuwa

■ Kar ganin yana da hakuri ko yaushe kike aikata masa kuskure da gangan abisa ganin ai inkikace ya hakura yana hakura... kisani duk randa kika kaisa bango zai dena hakurin zakuma ki dena jin dadinsa, bazaki kuma samun kanshi ba

■ Kada ki kuskura kisa aranki ko kuma wata Qawa ta fadamiki ki dauka cewa ba'a sirri da miji.... kul dinki baki da abokin sirri irin mijinki inde kika cire mahaifiyarki... inkuwa kikaqi to zaki qaraci nuqu-nuqunki kuma yana kallonki bazai nuna yasan me kike ba... tunda kin nuna kina da wayau ahaka zai barki... 

Amma kiji tsoron randa zai amayar miki da abunda ke cikinsa daga ranar kuma daga lokacin kin koma tsoronsa kenan kuma kin nesa da farin ciki kenan

■ Banda kauracemasa a shimfida. Akwai matan da inba alkawari ko cin hancin wani abu mijinsu ya basu ba basa ta6a yadda dashi a shimfida saboda wulakanci irin nasu da rashin sanin menene auren ma... kisani ba wasa bane hakika akwai tsinuwar ubangiji akan dukkan matan dake kauracewa shimfidar miji... matukar neman da yake miki ba wanda Allah ya haramta bane

Wato kamar yadda wasu kan korafin miji na cewa saide a sadu ta dubura; ko saduwa alhalin mace na cikin jini... A irin wnn hali tabbas bazaki masa biyayya ba domin shima bai yiwa Allah da manzonsa biyayya ba. Kuma duk namijin dake haka tsinuwar Allah ta hau kansa koda kuwa matar kace ta sunnah kuma koda ka tursasata. 

■ kada mace take bayar da izinin shiga gidansa ga wanda baya son shigarsu gidan. kamar wadanda ba yan uwa na jini ba, wadanda tasan komi wuya ba aure tsakanin su, koma wadanda ya nuna bayason shigarsu koda yan uwa na jinin ne, haka ma cikin kawayenki inyace baiso toh adena kurum

■ Haramun ne mace take ta yad'aa sirrin mijinta domin tozartashi

■ Ba abune me kyau ba ga mace takema mijinta barnar dukiya don ganin kurum yana da wadata. Kota rika daukar kayansa musamman na abinci ta rika kyauta dasu batare da izininsa ba... 

■ Haramun ne dibar kayan miji kina sayarwa, musamman kayan abinci su shinkafa, dawa, masara da sauransu 

■ Wajibinkine kula da yaransa da kuma ayyukansa na gida da suka shafesa, Haka yaran nan nasa koda kuwa wadanda bake kika haifa masa su bane.

■ Haramun ne ki cuci mijinki ta hanyar yiwa abokiyar zamanki sharri kisa ya saketa don kurum kina kishi da ita. Allah ya tsinema mai irin aikinki

■ Kada kike kausasa masa harshe, kina daga masa murya.... wato ya zamto kina fada masa magana mai zafi, tare da daga murya har wanda ke nesa koma amkota ace suna jiyowa koda kuwa ke ya zalunta. Hakan haramun ne a musulunci babu kyau....

■ Wajibine kike yin kokarin faranta masa rai. Sannan ki rika bashi uzuri akan wasu al'amuran koda kuwa kinfishi gaskiya.

■ Kada kiyi abinda zaisa shi yaji baya son zama dake a gida ko abunda zai sanya shi nisantar hira dake ko kaurace miki a shimfida. 
Musamman yawan kawo masa bukatu, karancin tsafta da yawan korafi ko kawo masa hirar gidan wasu.

🏡🏡
Haka wasu ruwayoyi sun kawo karin hakkokin miji kan matarsa kamar haka:

~ Yayin da wani sahabi ya bawa Manzon Allah (S.A.W) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki saita yaye masa shi, idan kuwa baya nan tana kare shimfidarsa bata ha'intarsa, kuma tana kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar 'ya'yansa. 

Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya bashi amsa da cewa: "Allah yana da ma'aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidai". 

🏡
Hakanan wata ruwaya ta nuna cewa: "Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah"

■ Sannan dole ne kiyi biyayya agare shi, domin shi shugaba ne agidan... babu yadda mutane biyu zasu hadu a wuri ba tare da shugaba ba, ki sani rashin biyayya a gare shi yana rusa masa ruhinsa da karya masa zuciya, Har ya fara tunanin daukar fansa...

■ Banda nunawa miji bai isaba kurum don kina taimaka masa ta wata fuska kice zakike goronta masa, hakan na tsyawa aranmu bama mancewa koda kinga muna dariya mun nuna bamu damu ba... Hakan nasa zamanmu daku na gurbacewa, kuma wannan fushin yakan iya turamu ga miyagun halaye da kuma yawan fusata da fada.

■ Ki girmama iyayensa da yan uwansa, kuma kike tunasar dashi yake musu alkhairi aduk sanda ya sami budi.

■ Kada mace ta rika gasa da wasu matan tace: An sayawa kawarta kaza kaima sai kayi min
kaza wannan ko kadan bashi da
kyau. Yana da kyau mata su dauki samfurin rayuwar zamantakewa daga Imam Ali (A.S) da sayyida Zahara (A.S), ga wani misali daga irin wannan; 

Wata rana Imam Ali (AS) ya shiga wajan Fadima (AS) matarsa.. sai ya tambayeta ko tana da wani abu sai tace: 
"Wallahi kwana uku kenan ya d'an Ammina bamu da komai". Sai yace: "Me yasa baki gaya min ba?" 

Sai tace: "Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi
Dan Amminki (Imam Ali) komai idan ya kawo shikenan, inba haka ba kada ki tambaye shi".

Duba kiga irin wannan rayuwa ta
gidan Ahlul Bait (AS) wacce hatta abin da yake wajibi akan miji bata tambayarsa sai idan ya kawo, 

Saboda haka ke zaki iya tambaya ba haramun bane toh amma yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado, kamar yadda maza su kuma su kiyaye ba kwauro ba 6arna..

■Uwa uba akarshe ki tsare masa farjinki da mutuncinki banda cin amana, inbakya gamsuwa dashi fadamasa karara yaje ya nemi magani ko ke ki taimaka ki nemo masa maganin ba faduwa kikai ba, 
Amma kwanciya da wani namiji wanda ba mijinki ba haramun ne kuma randa Allah ya tashi kamaki baki da uzuri, domin wutar da Allah zai saki ko fir'auna shugaban kafirai akasanshi kike matukar baki tuba ba... sai mutum ya raina kansa.

Allah yasa mu zamo masu rike amanar juna amin, fatan mun amfana da wannan tunasarwar.

Post a Comment

0 Comments