■ sirrin ・rike ・miji ■
・islamic medical center ・
▽・GYARAN JIKI A LOKACIN AL'ADA・▽
■ Facebook ■ twitter ■ Instagram ■ whatsApp
✿⇢+2348037538596
☻⇢www.sirrinrikemijinki@yahoo.com
☻⇢www.Sirrinrikemiji@gmail.com
✎◦ ✆ D3C13938
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
▽・GYARAN JIKI A LOKACIN AL'ADA・▽
Lokacin al'ada, lokaci ne da mace zata tsaya ta kula ta ga cewa bata sakin jikinta kamar lokacin da bata al'ada, musamman ma ・BUDURWA ・ wacce bata taba aure ba, har itama matar auren wacce ta san ciwon kanta , kuma ba ta son ta ga miji yayi watsi da ita da wuri ko yana tunanin Karin aure da wuri, to sai ki tsaya ki maida hankali wajen kulawa da jikinki a lokacin al'ada da kuma haihuwa, saboda ita mace a duk lokacin da take cikin al'ada to a wannan lokacin jikinta budewa yake yi, shi yasa idan mace na cikin al'ada idan akwai iyaye a kusa, sai su rinka hanata daukan Abu mai nauyi.
⇨ BOKITI.
⇨ TSALLE-TSALLE.
⇨ KAZAR-KAZAR.
saboda a wanna lokacin jikinta a bude yake.
Idan ko tana wannan kazar-kazar din to dukkanin jikinta budewa yake yi.
Don haka idan budurwa tayi aure kuma ta kasance mai irin wannan dabi'a shine sai ki ga an sami matsala da mijinta yana zarginta da ko tana yawon banza tunda bai sameta a matsayin wacce bata taba aure ba.
Nan kuwa ba haka bane, yawan TSALLE-TSALLE ne ya jawo a yayin al'ada.
Idan kuma matar aure ce to sai ka ga jikinta ya sake budewa, idan ta gama al'ada ta koma turaka sai ki samu maigida bai damu da ya rinka waiwayarta ba saboda a madadin jikinta ya matse, a a sai ma Kara budewa da yayi.
DON haka idan har kina cikin al'ada ya kamata ki kula da irin zaman da Zaki da tafiya ki kuma kiyaye da daukan Abu mai nauyi.
■ IYAYE ■
yana da kyau idan yarinya ta Kai lokacin al'ada ki zauna ki Mata bayani sosai.
⇨ wanka janaba.
⇨ da sauran bayani ibada saboda gaskiya wanna yana ma iyaye wuya sai kaga yarinya ta Kai 20 Amma bata san yadda zata gyara kan ta ba bare ma ta san yadda zata yi wanka janaba da na jinin al'ada sai a daure a dinga bayani a cire kunya domin wanna yana da muhimmanci ga ibada da zaman aure sai kaga yarinya farjinta yana wari duk saboda wanna matsala ce.
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
・YADDA ZAKI GYARAN JIKI ・
❀ +2348037538596
@sirrinrikemiji
Ya zama dole ki kula da wanka mafi karanci a Rana sau biyu, wato safe da yamma.
Sannan wanka da sabulu mai kamshi da kuma ruwan dumi, sai kuma ki shafa mai mai kamshi ki saka turare mai kamshi ki saka turare mai kamshi sannan a koda yaushe ki rinka yawan canja ( pad ) din da ke jikinki saboda shi jini ya danganta,
▼ wani yana karni.
▼ wani babu.
▼ wani ma wari yake.
To idan ya kasance ba kulawa shine Zaki ji daka do so mace tana doyi ko karni.
❀ sannan ki dinga kokari kina shan zuma safe da yamma zata dai-dai kimi al'adar ki.
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
♜ YADDA ZAKI GYARA JIKI NA MUSAMMAN ♜
✿ +2348037538596
@sirrinrikemiji
KAMAR yadda muka sani ne, yana da matukar muhimmanci ga kowacce mace data kula da aske gashin da ke (farjinta/matanci) da reza ko kuma da hodar aski, duk dai Wanda kike da halin yi, saboda shi wanna gyaran, gyara ne na musamman Wanda ake so ya zama duk sati ga mace gargasa, wacce kuma ba gargasa ba to duk sati biyu.
( gargasa itace mai yawan gashin gaba yana fito wa da wuri)
Yan'uwa Mata ayi kokari a kula da wannan gyara na musamman.
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
■ GYARAN ( NONO /MAMA ) ■
kamar yadda kika sani kowacce mace akwai yanda tsarin halittarta na ( NONO /MAMA ) yake:
⇨ AKWAI MACE MAI CIKAR MAMA.
⇨AKWAI MACE WADDA BATA DA CIKAR MAMA.
Yadda ya danganta da irin tsarin da halittar jikinta yake:
✰ misali ✰
✿ mace mai girman jiki (kiba) Zaki same ta da manya ( nono/mama).
✿ mace mai siranta Zaki sameta da karamin (nono/mama).
■ amma akwai Wanda zaka sameta bata da ( kiba ) tana da manya nono
■ akwai kuma mai kiba Wanda bata da manya nono.
Sai ta Duba ya gidansu yake tana iya gado.
Idan ya kasance yan 'uwan mahaifinta Mata suna da manyan nono to itama zata iya kasance mai manyan nono.
To idan kika kasance mai daya Daga cikin wadannan kina kuma bukatar gyaran nono ga hanyar da Zaki bi.
To Daga lokacin da (nono/mama) yake lalacewar Daga lokacin da mace ta haihu.
Musamman haihuwa farko.
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
☜・MAI MANYAN NONO・☞
idan kina da manyan nono kuma kina so ki rage girmanshi, sai ki samu Riga mama wacce bata Kai girman wacce kike sakawa ba Amma ( gardle )
Sannan ki daina cin wadannan abubuwa kamar haka,
◇ GYADA.
◇ LIPTON.
◇ KITSE.
◇ KI RAGE SHAN MAN GYADA.
◇ BOTA.
◇ MAN SHANU.
Idan kika rage ci da shan wadannan abubuwa ko ma ki dauki lokacin ba kya ci, to hakika girman nono zai ragu.
Haka Zaki ci gaba da yi har sai yayi dai-dai ( size ) din da kike so.
Sannan koda Zaki ci sai ki ci kadan yadda ba zai sa Maman ya Kara girma ba.
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
▽・MAI KARANCIN NONO TANA SO YA KARA GIRMA・▽
zata nemi wadannan
✯ gyada.
✯ bota
✯ romon kaza
Kamar kayan marmari.
■ CIKOWAR NONO ■
⇢man shanu.
■ kwai.
⇢ madarar shanu.
Zaki fasa kwai ki zuba mishi madarar shanu sai ki soya da man shanu Kici kullum da daddare.
■□ CIKOWAR NONO □■
⇨ bota
⇨ kwai
Ki fasa kwai ki soyashi da bota kici kullum da daddare ki sha madara ( peak milk )
Idan kina haka Zaki ga koda yaushe nononki a cike babu wani yakunewa ko ya zama kamar silifas.
■⇢■⇢■⇢■⇢■⇢■⇢■⇢■⇢■⇢■
Da fatan uwargida/amarya da duk wata mace zaku maida hankali wajen amfanin da wanna.
✿ www.sirrinrikemijinki@yahoo.com
✿ www.Sirrinrikemiji@gmail.com
☻ +2348037538596
■ Instagram
@sirrin-rike-miji
■ twitter
@sirrinrikemiji
■ SIRRIN ✿ RIKE ✿ MIJI ■
0 Comments