Sau da yawa idan mutum ya ce "ina fama da ciwon baya", sai ka ji wani ya ce "ba ka motsa jiki ne", ko kuma ya ce "ka riƙa motsa jiki" akai-akai. Amma abin tambaya a nan shi ne: wanne irin atisaye ko motsa jiki ne ke temaka wa mai ciwon baya?
Da farko dai, ya kamata mu bambance tsakanin "motsa jiki" da kuma "atisaye".
Motsa jiki na nufin duk wani motsin jiki ko gaɓɓai saɓanin hutu – wato hutu shi ne lokacin da mutum ke kwance ko zaune ba tare da yana yin wani aiki ba. Misalan motsa jiki sun haɗar da: ayyukan gida, aikin gona/lambu, tafiya, sassarfa, gudu, ayyukan sana'o'i da sauran ayyukan yau da kullum.
Amma atisaye, kamar yadda Bahaushe ya aro kalmar daga kalmar turanci wato "exercise", sannan ya mai da ita zuwa "atisaye". Atisaye na nufin tsararre, aunanne, ƙayyadajje, kuma keɓaɓɓen motsa jiki domin magance matsala ko bunƙasa aikin sashin jiki ko gaɓa.
Saboda haka, kamar yadda nau'o'in ƙwayar magani ke da yawa, kuma kowacce ƙwaya ke da keɓaɓɓen aiki domin ciwuka daban-daban, haka ma atisaye ke da nau'o'i daban-daban kuma domin ciwukan jiki ko gaɓɓai daban-daban. Har ila yau, nau'in atisayen mai ciwon gwiwa ba zai zama iri ɗaya da na mai ciwon baya ko wuya ba.
Bugu da ƙari, shi kansa ciwon bayan na da nau'o'i daban-daban. Wani ciwon bayan ya faru ne sakamakon tsinkewa/cirar naman baya, fashewa ko zaizayewar faifan da ke tsakankanin ƙasusuwan gadon baya, gocewa ko karayar ƙashin gadon baya da dai sauransu. Saboda haka, kamar yadda dalilan ciwon baya suka bambanta, tilas ma nau'o'in atisayen da za su magance nau'o'in ciwukan bayan su bambanta.
Abu mafi ban tsoro a kasadar fara atisaye ga masu ciwon baya ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba shi ne; sau da yawa ma ire-iren motsa jiki ko atisayen da mutane ke yi sune ke ta'azzara ciwon bayan. Ko kuma a shafe tsawon lokaci ana yi amma babu sauƙi.
Daga ƙarshe, ya zama wajibi ga duk mai wani nau'in ciwo: ciwon baya, ciwon wuya, ciwon ƙafaɗa, ko ciwon baya da ya guji fara yin duk wani irin motsa jiki ko atisaye da zimmar magance wani ciwo ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba.
Saboda kafin a samar da wani nau'in atisaye ga mai wani nau'o'in ciwon baya sai an nazarci dalilin ciwo, an kuma gane wanne iri ne kafin a ɗora mutum a kan ƙeɓaɓɓen atisaye da shawarwarin da za su temaka wa mai ciwon.
Har wa yau, akwai kayan aiki da nau'rori na musamman da likitocin fisiyo ke amfani da su wajen rage raɗaɗin ciwon baya. Wannan hanya ce da ake magance ciwo ba tare da dogaro da shan ƙwayar maganin rage ciwo kullum ba.
Don haka, yin atisaye ko motsa jiki ga mai ciwon baya, ciwon gwiwa da sauransu, ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba tamkar shan magani ne ba tare da tuntuɓar likita ba.
0 Comments