๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Sama da mutum milyan 264 a fadin duniya ke fama da cutar damuwa da ake kira "๐ซ๐๐๐๐๐๐๐๐๐" ciki hadda Nijeriya.
Mutane Bila'adadin na fama da wannan larurar ta matsananciyar damuwa ne sakamakon kuncin rayuwa ta fuskoki daban-daban da suka samu kansu aciki.
Wannan tsananin damuwar ๐๐๐ฉ๐ซ๐๐ฌ๐ฌ๐ข๐จ๐ง ciwo ne kwakwalwa dake shafar zubin yanayi na mutum wato ๐๐จ๐จ๐.
Babban abun tsoron shine; Mutane masu wannan larura galibi basa iya furtawa cewa suna fama da matsala cikin rayuwa saboda su kanji kamar ba wanda zai yarda dasu, sannan su kansu suka gaza ta ina zasu fara bayanin abun har a iya fahimtarsu! domin galibi suna da juriya zaku zauna suima hira harda dariya amma fa cikin ransu suna da dumbin damuwar da ko kuka basa iyayi saboda tsananin nauyin damuwar dake cinsu.
๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐
A hankali a hankali matsalar ke hauhawa daga kadan ta bunkasa ajika har takai ga manyan alamomin ciwon sun fara bayyana ta yadda za'a fara ganin:
1▪︎Mutum ya fara kasa kula da kansa bangaren tsaftar jiki da tsakar gida kota yaransa musamman a Mata mace me tsafta amma aga ta fara zama a sukurkuce ba kamar yadda suka saba ko aka sansu ba.
2▪︎Canzawar yanayin bacci, ya zamto ba'a iya yinsa isashshe ko kuma ayi da yawa aji baya isa duk da haka.
3▪︎ Kasa warware wasu yan kananun matsaloli, dan karamin abu saide yabi ya cudewa mutum ya kasa warwaresa,
4▪︎Rashin sha'awar komi, mutum ya dena jin dadin abunda ada inyai yake jin nishadi,
5▪︎Rika zargin kai akan wasu abubuwa dake faruwa, mutum yaga kamar duk laifinsa ne,
6▪︎ Rashin kuzari da kasala akomi, Mace kila take qin mai gida ya kusanceta sai yai fama, ko Miji yaji sam baida sha'awar kusantar matar, ko kuma
7▪︎Tabarbarewar abubuwa da fusakantar koma baya akan abubuwan da mutum kila ada ya iya amma yanzu komi ya ta6ar6are masa, ko kin maida hankali akan abunda yake hanyar nemansa ne na yau da kullum.
๐๐๐ข ๐ฆ๐๐๐ข ๐ก๐๐ญ๐ฌ๐๐ซ๐ข
Daga wandancan idan ba'a fargaba ko kuwa mutum yai tunanin kai abun nan ya dace naga likita ba sai mutum yakai ga fara tunanin ๐ฆ๐ฎ๐ญ๐ฎ๐ฐ๐ ๐ญ๐๐๐ข ๐ฆ๐๐ฌ๐ ๐๐๐ฒ๐ฎ๐ฐ๐. Wato zai fara yanke shawarar gwammacewa gara mutuwarsa da rayuwarsa.
Ana haka idan kwakwalwarsa ta gama lamince mutuwar sai mutum ya fara yunkurin hanyar da zaibi ya kashe kan nasa wato ๐๐ฎ๐ข๐๐ข๐๐ ๐ข๐๐๐๐ญ๐ข๐จ๐ง domin kamar yadda nace bashine akaran kansan keson kashe kansan ba domin yasan mahimmancin rayuwar amma kwakwalwarsa ce zata rika ingizasa kurum ya kashe kansa shine magani/mafita. Toh in ba'a ankara ba saide a wayi gari mutum ya aikata successfully ya kashe kansa labari ya famtsama madu tsinuwa nayi, masu tunani na jimami, masu muggan addu'oi kansa ma nayi.
๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐
Kowanne da yadda kwakwalwarsa ke fadamasa hanyar da ya dace yabi wajen kashe kan nasa; wani yasha maganin kwari, wani allurar guba, wani ya rataye kansa, wani kwakwalwarsa cewa zatai ya bari sai jirgin kasa ya taho ya afka gabansa ya takesa, wani motace zaije high way ya haike mata, wani bindiga zai harbawa kansa, wani ta hanyar rataye kansa...
Mafi ban tsoron da hatsarin yunkurin kashe kai shine wanda kwakwalwa kesa mutum ya 6oye inda mutane bazasu gansa ba.
Wato suicide a inda babu wanda zai gansa ballantana ya kawo dauki. Shiyasa a asibiti muna musu abunda ake kira SUICIDE RISK ASSESSMENT... muna da score da muke baiwa kowacce amsa da zasu bamu inda akarshe in muka gama lissafawa kai tsaye muke rike mutum mu basa gado, bazamu yadda mu sakesa ya koma gida ba domin zai aikata abunda yai niyya.
Mata sunfi Maza yawan yunkurin kashe kansu amma saide Maza sunfi aikatawa yanke take bada jira ba, Maza nada successful suicide completion rate.
Duk mutanen da zakuji sun kashe kansu kaso 99% suna da ta6uwar kwakwalwa wato hankalinsu ya jirkita, suna da ciwon kwakwalwar wanda da yawa ya samo asali daga cutar damuwa.
Kashe kan shine outcomes na psychotics symptoms din da sukai fama dashi tsawon watanni ko shekaru, wanda dama abunda ake gudu kenan.
Don haka kada kai saurin yanke hukunci inkaji wani ya kashe kansa, musamman cikin musulmai wallahi abun bana wasa bane, ya wuce duk yadda kuke zato, hasali ma kunji na fadamuku kwakwalwarsu ke shawarar bawai hankalinsu bane.
๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ???
Depression baida takamaiman abunda ke jawosa guda daya, saide abune da ya kunso abubuwa mabanbanta kama daga zubin halitta, muhalli ko yanayin da mutum ya taso da kuma wasu larurorin da dama jikinsa ke fuskanta, kowa da yadda abubuwan ke tasiri akansa.
๐๐ฆ๐ฆ๐ ๐ฐ๐๐ฌ๐ฎ ๐๐๐ ๐ ๐๐๐ฎ๐๐ฎ๐ฐ๐๐ง ๐๐๐ค๐ ๐๐ฌ๐ฌ๐๐ฌ๐ ๐ก๐๐ค๐๐ง ๐ฌ๐ฎ๐ง ๐ก๐๐๐:
■ Mutuwar wani na kusa da mutum walau Mata, Miji, uwa, uba ko wani dan uwa dake hidimtawa mutum ko yar uwa... hakan na iyasa mutum cikin depression ko in mijin mace ya mutu ya barta da รฝaรฝa...,
■ Haka ma ganin wani abu na firgici da mutum bai ta6a ba kamar ganin gawar mutum babu kai, ko mummunan hatsari ya ritsa da mutum kansa ya juye yaita mafarkai, ko ganin mutum kansa ya tsage kwanya ta zazzago amma bai mutu ba, da sauransu..
■ Haka a mutanen da suja fuskanci cin zarafi ya zamto tun mutum na karami ya hadu da azzalumar kishiyar uwa wacce ke azabtar dashi ta kowacce irin hanya, ko kuwa wani shaidanin cikin yan uwan ko cousin in a Mace ne ya zamto yana wasa da farjinta ko yana mata fyade tare da tsoratar da ita cewa kada ta fada inba haka ba zai kasheta, ko kuma ma har yan aiki Mata da ake kawowa gida suma sukan rika lalata yarinya mace ta gidan ta hanyar rika mata kwakule suna tsotsar farjinta batare da iyaye sun sani ba harde yarinyar ta saba kan ta gama zama budurwa sosai.
■ Ko kuma sakamakon wani ciwo da mutum ya hadu dashi musamman wanda ake ganin baxa a warke ba irinsu kanjamau, ciwon zuciya ko cancer da sauransu wanda hakan ke tsayawa mutum arai kullum cikin tunani.
■ Ko kuma dalilin harkar karatu kamar yawan faduwa jarabawa ko kuma in ankori mutum daga wajen aikinsa ko wajen neman abincinsa
■ Ko halin talauci ya zamto ga iyali amma ba cin yau bana gobe ga babu abun yi, anrasa taimako
■ Haka haduwa da matsalolin auratayya tsakanin mata da miji, wani yake kuntatawa wani koma saki baki daya inya biyo baya ta yadda macen tasan laifinta ne yanzu ta dawo tana nadama.
■ Ko sanadiyyar tafka asara a kasuwa dalilin damfara, gobara ko wani abu.
■ Ko kuma rasa wata wacce mutum yaso da aure bayan hidimta mata da de sauransu duk abubuwa dake sa damuwa baibaye mutum
๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ???
Eh' kwarai da gaske kuwa! yana sa kisa. Domin abune da galibi masu fama dashi ba furta abunda ke damunsu suke ba. Wasu kuma na iya bayyanawa amma aki daukar mataki ko ake ganin bakomi bane, watsi da korafinsu ma karin takaici ne, su kadai ke hadiyar takaicin su, tunda ya zama ciwon kwakwalwa sukan rasa control da zasu gwammace mutuwa itace kurum maganin damuwar.
๐๐๐๐๐๐๐
Duk wanda yake fuskantar damuwa tare da abu 3 zuwa 5 na alamomin can da masu depression kan fuskanta asama toh ya hanzarta kai kansa ga likitan halayya wato psychiatricians da ake samun UNIT dinsun a dukkan babban asibiti ko kuma yaje asibitin da ake lura da masu rangwamen hankali me zaman kansa wato psychiatric hospital a dubasa a dorasa akan magani da shawarwari. Kar kuji nace psychiatric hospital ku dauka sai mahaukata ake kaiwa can sam ba haka bane.
Sannan kada ku kuskura kui wasa da maganar wanda ya iya furta cewa zai kashe kansa.. koda wasa kukaji haka ku daukesa zuwa asibiti.
Mutane mu daure in mutum ya koka mana matsala muke kallonta da fadi kada muke watsi da mutum, ko bazamu iya komi akai ba mui masa magana me dadi ko murmushi hakan na iya canza duniyarsa. Mu daure mu jasu ajika.
Depression na bukatar shan magani batare da daga kafa ba na tsawon watanni koma shekara da doriya shyasa dole sai manyan likitoci.
A kasashen da sukaci gaba akwai kungiyoyi musamman na rehabilitation dake taimakawa masu wannan yunkuri na yanke rayuwa.
[๐๐๐ซ๐๐ก๐ข๐ฆ ๐. ๐๐ฎ๐ฌ๐ฎ๐]
0 Comments