𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐇𝐀𝐊𝐎𝐑𝐈 𝐖𝐀𝐓𝐎 𝐓𝐎𝐎𝐓𝐇𝐀𝐂𝐄 & 𝐓𝐎𝐎𝐓𝐇 𝐀𝐁𝐒𝐂𝐄𝐒𝐒:



~~~~~~~~•••●●■●●•••~~~~~~~~

Duba da irin wannan yanayi na sanyi da muke ciki lokacine da cuttukan dake shafar jijiyoyin kai sako sukafi tsanani... kama daga ciwon hakori, ciwon kunne, ido da sauransu. Zan dau ciwo mai tsanani da takura nai bayaninsa ko da yawa wadanda basu sani ba zasu fahimci yadda abun ke faruwa. Allah sa bayanin ya amfanar amin.

:::::::::::::::::::::::::::●●1●●::::::::::::::::::::::::::::

Ciwon hakori galibi ruɓewar tushen hakorin a tsakaninsa da dasashi ke jawo sa, sakamakon samun kyakkyawan muhallin zama tare da yin kyankyasa da bacteriyar din da ake aka samu cikin baki (sitireftokokus mutan da biridans) galibi... wato rukunin giram fozitib dake da jijiya da saiwoyi. 

Bakteriyas din suna samun wannan kyawun yanayin ne sakamakon sakacin mu wajen tsaftace baki in munsha sinadaran "sugar" da suke samu in munsha zaƙi irinsu; (lemon kwalba kona roba, chocolates, candy, sugar, shayi, alawa dss) ko kuma in munci abinci mai bawa jiki kuzari "carbohydrates" irinsu; (Tuwo, masara, shinkafa, doya, dankali, indomie, taliya dss) 

Wadannan backteriya bayan sun sami wadannan sinadaran sugar da bama tsayawa mu goge bakin da kyau shike basu kuzari da lafiyar sakin sinadaran gubarsu (toxins) a gurin da suka samu suka makale a hakorin takai ga sun haddasa abunda ake kira "PLAQUE KO CARIES" kamar farin kwanso ko kwanso mai duhu baqi.. na kunshin kwayoyin cutar akan hakori... Wanda muke iya gani da ido har wasu kance masa CIN-ZANZANA" 

Zanzanar shine sunan dattin toxins din da bakteriyar ta zuba da yaren hausa... Toh daga nan ne kwayoyin zasu fara nitsawa ahankali suna guiguiyar jikin Enamel wato 6am6arokin hakorin da suka taru akai suna shiga ciki ahankali-ahankali....wanda a wannan ga6ar inda ana goge baki da kyau koda sun fara wannan kokarin shigar inmukai brush toh FLUORIDE din dake jikin makilin zai kashesu, ko ya rage musu karfi inda inmuka kuma yin brush gaba sai su mutu ko suita raguwa ahankali har su qare.

Toh amma karancin tsaftar kesa suci gaba da haƙa... har su fasa ENAMEL su tarar da "DENTIN" wato tuwon hakorin, toh dake kasan dentin kasansa kadan nan jijiyoyin kai sakonni kwakwalwa da jijiyoyin jinin dake ba hakora jini duk suke... toh bakeriyas din suna tarar da nan suka dunguri jijiya suka fara ci toh sannan zamu ankara saboda ZAFI tunda aikin ya tarar da wayarin din kai sakonni🔥. 

A sannan ne mutum zai gane yana da ciwon hakori bayan "the damage already been done" domin ada kila duk mutum bai san da ciwon ba. Ko kuma kila yaga kogo amma baya masa ciwo don haka bai maida hankali ya koma ta kansa ba. Amma yanzu antarar da inda dole yagane bashi da lfy, ba zancen juriya. 

Toh idan duk da haka sun tarar da DENTIN amma maimakon sui kasa su nitsa cikin jijiyoyi sai ya zamto sun dena descending sun koma faďaďa mashigarsu shine sai sui katon kogo amma duk da haka ta waje baza agani ba. Domin wani bun yadda suke ramin su shiga baikai ko tsinin allura ba...

To idan suka fadada kogon ta ciki shine duk randa mutum ya tauna wani abu mai karfi sai yaji hakorin ya ɓungulo ko ya burma domin ta ciki holo ne dama, bakteriyar tuni ta cinye nama naman gurin... ko kuma shine in yaje wajen likitan hakori ana dubawa da andan kankare jikin hakorin sai kaji 6urum ya bude kaji yana ɗoyi😷 saboda abincin da ya shiga ya hadu da toxins din bakteriyar ya kume ciki. Wannan shine Yadda KOGON HAKORI ke faruwa.

:::::::::::::::::::::::::::●●2●●::::::::::::::::::::::::::::

Toh idan kuma sanda bacteria din suka fafe tuwon hakorin suka dunguri jijiyoyin sunyin kasa sun nitsa bayan cinye hakorin to shine sai su tarar da GINGIVA ko Gum din kasa wato can tushen hakorin daga nan saboda babu iska sai toxins din yasa gurin ya kume sai ya fara samar da ruwa wato ABSCESS shine wasu zakaga har ta waje fuskarsu ta kumbura ga matsanancin ciwo. 

Hakan kuma shikesa koya sanyi ko abu mai sanyi ya ratsa ya shiga saboda sun fatattaka jijiyon gun yanzu mutum zaiji zogi ya qaru saboda me? Saboda bakteriyar nason sanyi, tana son loko inda zataci karenta ba babbaka, wannan tasa da sanyi ya shiga gun sai jijiyar takai sako su kuma su yunkura. Shyasa lokacin sanyi abun yafi tsanani.

Toh idan wannan abscess din ya taru dole sai ansha magani bana wasa ba domin ganin ankashesu, inko abscess din da yawa sai anhuda anzuqesa, Idan ba'a zuqe ba to zasuci gaba da rubunya subi jijiyoyin jini su yadu zuwa tushen wani hakorin shima su haddasa masa ciwo ta kasa... kafin ka ankara zasu gamawa da hakoran su zarce cikin kirjinka su haddasa ciwon zuciya.

☆ Kwarai kuwa yana daga complication din ciwon hakori kwayoyin cutar subi jijiyoyin jini su hadda abunda muke kira ENDOCARDITIS ciwon mayanin zuciya wanda barazana ne ga rayuwa. Tunda kai tsaye daga hakorin suka sauko wuya zuciya zasu fara tararawa shyasa ake mutuwa dalilin ciwon hakori in akai wasa. 

Wannan kusancin na hokari dakuma kwakwalwa shikesa wasu har ciwon kunne da kasa hadiyar abinci suke fuskanta domin wayarin din duk daya ne.

Wannan bakteriya din da akuke rainawa kamar yadda nace intai abscess ta nutsa take shafar sauran hakora zuwa zuciya shyasa ake camfa wai cewa inde aka cire hakori sau 1 toh anta cirewa kenan, ko kuwa duk saura sai sun harbu.... duk karyane. Babu alakar cire hakori da cutar cancer ko kuwa cewa sai anta cire hakori. Inde kaga ancire hakori kuma wani ma ya dau ciwo to alama ce ta dama wannan hakori na kusa infection din yakai garesa shima.

Dubu nawa aka cirewa hakorin kuma suke lafiya har yau. Inkaga cancer dama kana da kwayoyin cancer cell din ne sai wannan ya zamo sababin bayyanarta. Haka inkaji wani hakorin ya kamu to HEMATOGENOUS SPREAD ne na kwayoyin bakteriyar zuwa wani hakorin.

:::::::::::::::::::::::::::●●3●●::::::::::::::::::::::::::::

Toh idan kun fahimci bayanin sama na abunda ka iya faruwa sanadiyyar ciwon hakori kurum, toh shyasa ayanzu don gudun kar hakorin kusa su kamu suma ko kuma ganin ga kogo koda babu ruwa atushen hakorin.... yasa ba'a gaggawar cire hakori yanzu dole sai anwa mutum PROPHYLAXIS wato anbashi magani yasha matsayin rigakafi na sati 1 ko 2 kafin ai aikin cire hakori.

Saboda ta yiwu kwayoyin cutar basu yadu zuwa ga wani hakorin ba amma akokarin cirewar in aka bude jijiyar jini sai sui masa subi su riski daya hakorin shyasa yanzu ake prophylaxis, kuma galibi sai anyi hoto angani koda ta waje babu alamar hakorin yana ruwa...

Don haka kada wanda ya yadda yaje za'a cire masa hakori kai tsaye kurum akace ya kwanta acire ya yadda. Kace kaji likita yace akwai bukatar rogakafi don gujewa complication don haka ka nemi awanke gun kurum akuma baka maganin rage zogi, sannan sai abaka prophylactic antibiotics kaje kasha idan ka shanye ka dawo acire! Sau tari kafin sannan ma zakaji ya dena ciwo to sai kazo acire hankali kwance. Ai dama kuskurene ma cire hakori sanda yake tsaka da ciwo, ba ayi sam... inde ba hatsari akai ba. In accident ne wannan ana iya ciresa nan take inya karye.

Wato inde ba accident neba ya zamto hakori ko mukamiki ya karye. Inde don kwayar cuta ce ake tsammani toh dole saida prophylaxis. Inma dentist ne kai nasan kasan hanka don haka don Allah ka dena gaggawar cire hakori sai kaba mutum prophylaxis din (AMOXICILLIN) na sati 2 ya gama tukun, adena kallon abunda za asamu kurum.

Haka kuma baya ga wadancan bakteriya din kala biyu dana kama sunansu ana iya samun wata daban musamman daga ciwon makoshi ko kuma mura wato sinus infection. Shyasa dole sai likita ya nutsu ya kuma yi tambayoyi mahimmai ka bashi amsa domin gano inda abun ya somo da kuma maganin da ya dace da kwayar cutar da yake hararowa... shyasa wani maganin bayayi domin kai kana zaton ga irin kwayar cutar ya dace ace ta mutu zuwa yanzu, amma ashe mara lafiyar ne makaryaci, bai fadi gsky a ainishin tambayoyin da likitan yai masa ba.

Shiyasa ko anan facebook har gobe in mutum na tambayesa na fahimci yana mun karya bana kuma kara saurarsa, ko kuma nace ma ga magani kayi amma bayan ka fara samun sauki kasa wasa... toh nan ma koni na haifeka na barka kenan saide kaga wani likitan. 

Shiyasa zakuga galibi likita baya duba yan uwansa na jini saide emergency inta taso, ko matarsa saide taga wani likitan, kamar yadda shima inbashi lfy saide yaga likita bazai sha magani daka ba... saboda susan abun ba wasa bane, aje attachment da sanayya gefe ake ai bayani tamkar ba asan juna ba. Babu wani likita dazaije yana yaďa sirrinka, domin ba abunda bai gani ba ballantana kai tunanin wani abu daban akanka.

Don haka aguji yin karya ga likitoci kanku zaku cutar.. kamar yadda bazakaso ace likita yai banza dakai ba toh kaima ka bayyana masa dukkan abunda kasani, kai har wanda bai tambaya ba inkasan fadarsa zai iya yin amfani.

:::::::::::::::::::::::::::●●4●●::::::::::::::::::::::::::::

𝐀𝐋𝐀𝐌𝐎𝐌𝐈𝐍 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐇𝐀𝐊𝐎𝐑𝐈

Wadannan duk abayyane suke sun kuma hada da: kumburi, yawan dalalar ko taruwar miyau, jin zogi wanda ke kuɗa har kunne ma ake jin ciwon, haka jin zogin ciwon har wuya, wahalar hadiyar abinci, zafi yayin tauna, zafin yayin waige, ko hakori yake ruwa, nauyin numfashi, da warin numfashi... duk ciwon hakori na haddasa wannan. 

Haka sensitivity wato inkasa abu mai sanyi zakaji ya dau kuɗa, ko kuma inka bude iska ta shiga da kaluluwa a kasan mukamiki.

Ciwon hakori tare da zazza6i lokaci guda yana nuna yanzu haka kwayoyin cutar suna kan aikinsu ma, kamar kurace ke cin barewa da ranta batare data kashe ba.. shyasa bazaka daure azabar ba. 

Haka jin kaluluwa a mukamiki na sanar da likita yiwuwar kwayoyin cutar sun shiga jijiyoyin jini dole yaima systemic treatment wato kada tunanin magani ya tsaya ga hakori kurum duk sauran sassan jiki ta shafesu... domin gudun abunda kwayoyin cutar zasu iyayi. Rashin sanin hakan kunga ai illah ne, shyasa aiki sai mai shi, inkaga case yafi karfinka matsayin karamin jami'in lafiya maza tura mutum ga manyan likitoci a asibitin gaba.

:::::::::::::::::::::::::::●●5●●::::::::::::::::::::::::::::

𝐌𝐄𝐊𝐄 𝐍𝐔𝐍𝐀 𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌 𝐙𝐀𝐈 𝐈𝐘𝐀 𝐇𝐀𝐃𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍

■ Karancin tsaftar baki da hakora wato "poor dental & oral hygiene" gaskiya shine kan gaba. Kamar yadda nasha fada kurum kurkure baki bashine tsafta ba, hatta yin brush fa kwai yadda akeyi sai ankoya. Sannan bayan angoge sai ankoyi sa zare ana sakuce space din tsakanin hakora, shyasa ynxu duk sabon gidan brushi ake saka wata yar karamar roba mai kamar igiyar robe ta sakuce tsakanin hakori... saboda cire abincin da ya makale wanda inba haka kwayoyin cuta sun sami mazauni.

Haka koda an iya brush to yinsa sau 1 ayini yai kadan ya samar da tsaro ga hakora.

■ Yawan shan zaƙi, kamar yadda na fada asama: su soft drinks, cokes, maltinas, chocolate, alawa, mazarkwaila, tea, rake, da duk wani abu me zaki. Mutum mai ta'ammali dasu tunma bamai tauna sweets ba zai iya wayar gari da kogon hakori wato cavities. Shyasa ko yara aka fiye basu kayan zaqi batare da kamasu awanke musu baki ba za aji suma bakinsu na ďoyi ko cin zanza.

■ Bushewar baki kila sanadiyyar wani magani da aka rubutawa mutum yake sha, ko kuwa barinsa abushe ya zamto mutum baya shan ruwa akai akai, musamman a tsoffi wannan yafi.

Amma de adunkule gaskiya ciwon hakori karan cin tsaftar baki ne. Don haka dole mutum ya lura inyanason cetonsu.

:::::::::::::::::::::::::::●●6●●::::::::::::::::::::::::::::

𝐌𝐀𝐆𝐀𝐍𝐈𝐍 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍

▪︎ Idan akwai zazza6i, za aba mutum maganin zazza6i wato Antipyretics musammsn fitacce wato: Patacetamol.

▪︎ Idan akwai zogi za'a ba mutum maganin zogi wato anti inflammatory gasunan birjik irinsu: Aspirin, cafenol, feldin, diclofenac, ibuprofen, Novalgin, mefenemic da sauransu. 

Amma de asani rukunin Anti inf. suna kunshe da caffeine don haka gamai ulcer ya kwan da sanin zasu iya tayar da ita koma susa mutum inyai amai yaga jini.... saide ciwon hakori alokacin ya danne azabar ulcer dinne. Wato benefits outweighs risk, amma de likitan da kagani shi yasan plan din da ya dace dakai.

Shin za'a iya hada paracetamol da anti inflammatory musamman in akwai zazza6i amsa eh.

■ Anti biotics; tunda munji bacteria din kai tsaye rukunin maganin da zai kasheta za aba mutum, domin ba duk antibiotic ne zai kasheta ba sai wanda zai iya yunwatar da ita, ya fasa jikinta, ya toshe mata hanyar numfashi ta mutu. Antibiotic ba OTC bane don haka doka ne ambatar sunan antibiotics a post. Sai anje ga likita shine zai duba abunda ya dace da mutum.

■ Neurogesic ko opiods rukunin magunguna masu karfi idan duk wadancan na rage zogin basui aiki ba shine likita ke badasu.. wasu kuma na shafawane ta waje ko fesawa acikin hakorin.

■ Sai kuma in kogo ne yai zurfi toh ana iya cikesa.

■ Idan kogon yai zurfi sosai kuma ya zamto duk an cinyesa toh anan ko an cikesa idan likitan hakori yaga cikewar na iya sa cigaba da jin zafi toh CIRE hakorin yafi cikon. inajin inda ake samun sa6anin shawara kenan wasu ke cewa bayan an musu ciko zafi ya rikayi har saida aka cire hakorin.... dama yai mutuwar da ciresa shine abunyi ba ciko ba.

■ Kurkure baki da ruwan dumi me gishiri agida na taimakawa wajen rage kwayoyin cutar da kuma zogi. Duk sanda akaci wani abu koda sau nawa ne toh da an gama kar azauna, maza asami ruwan dumi akurkure... hakan koda da kogo zai hana kumewa da kumburin gurin.

■ Rage surutu musamman a irin wannan lokaci na sanyi na rage zogi da azaba. Gami da cin abu me ruwa ruwa.

■ A kuma yi hakuri da kwanciya a siminti mai sanyi, ko cikin Ac ko shan drinks masu sanyi da kankara irinsu yoghurts.

■ Sannan baya ga hakorin in likita ya lura da wata matsalar to nan ma yana iya karawa da magungunan da suka dace walau supplements irinsu vitamin c & b- complex, antideppressants ko steroids

■ Matukar ba acike kogon nan ba zaka iya shekara 10 kana yi domin bacteria din taita dawowa kenan tunda magani kurum kakesha ba'a kiyayewa. Idan duk anyi anyi yaki dena ciwo toh ko babu kogo kaje kaga likitan hakori ku tattauna yiwuwar cire kurum. Amma de kar a manta a kar6i prophylaxis na Amoxicillin na tsawon kwana 14 kafin acire tunma ba inyana ruwa ba.

☆ Kar a manta shan magani zogi baya maganin ciwon hakori saide adena jin zafi na dan wani lokaci amma zai dawo. Dole ahada da maganin da zai kashe giram neegetib da fozitib baki daya.
:::::::::::::::::::::::::::●●7●●::::::::::::::::::::::::::::

𝐌𝐀𝐓𝐀𝐊𝐀𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐈𝐘𝐀

1. Lura da tsaftar hakora shine mahimmi. Don haka inkana kokonto game da yadda ake brush ka daure ka ware lokaci minti 5 kacal ya isa ka bude YOUTUBE kai saearching video akan How to properly brush your teeth. 

2. Bayan ka iya ko ka koya toh Mafi karancin shine ka goge baki sau 2 arana, mafi inganci sau 4 ko duk bayan gama cin abinci.

3. Yayin goge baki in angoga makilin to ba nan da nan ake kurkurewa ba, dole ajira minti 2 zuwa 5 abari fluorides din makilin din yai aikin kashe kwayoyin cutar inba haka ba koda angoga brushi yadda ya dace baza akashe komi ba, kuma hakan bazai hana hakora ciwo ba.

4. Ake amfani da dental floss ko interdental cleaner ana tsefewa ko sakace tsakanin hakori. Saboda wannan ma mahimmi ne, galibi ta inda bakteriya din ke fara samun mazauni kenan

5. Kada abubuwa masu suga suke zamtowa a abincinka na karin kumallo da kuma na karshe aanda daga shi sai bacci. Akuma rage cin zaki ko tauna abubuwa masu zaki ko sha... ko don gudun ciwon suga.

6. Shi kansa brush akwai bukatar koda sati sati ake tsomashi aruwan dumi yadan dahu saboda bakteria din. Sannan kusani brush na expire a wata 3 ne inde kullum ana amfani dashi. Don haka duk wata 3 zuwa 4 ake canza sabo. Wasu sai subar brush ya shekara ma.... habaa kuskure ne.

■ Sannan arika zuwa wankin wankin hakora haka kurum koda basa ciwo akalla duk wata 6 hakan zaisa agani matsala da wuri in akwai. In babu kuma zaisa karin lafiya bama ta baki ba har idanu da kwakwalwa da kunnuwa.

Kuyi hakuri naci lokacinku da yawa wajen karatu, fatana Allah sa kun ilmantu.

::::::::::::::::::::::::::::●●●●::::::::::::::::::::::::::::
𝐈𝐛𝐫𝐚𝐡𝐢𝐦 𝐘. 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟

Post a Comment

0 Comments