Amfanin Albasa a jikin dan adam:





Albasa na da tarin alfanu a cikin jikin dan adam, sannan kuma an dade ana amfani da albasa wajen magani cututtuka da dama.


Baya ga haka albasa na karawa abinci dandano da kamshi mai dadi, wadda ake ganin yana daga cikin muhimman sinadarai na yin girki.

Don haka muka kawo maku wasu daga cikin alfanun da albasa ked a shi a jikin dan adam.


Ga su kamar haka:

1. Albasa na taimakawa sosai wajen maganin sanyi, sai daimutane da dama basu san cewa wannan sinadari na maganin ciwon tarin fuka da jiri ba.

2. Cin albasa cikin abinci na taimakawa wajen wanke jinin jikin dan adam ta yadda zai kore duk wani dauda dake tattare da jinin.

3. Ana amfani da albasa wajen gyaran fuska sakamakon sinadarin ‘carotene’ da yake tattare da shi.

4. Albasa na taimakawa wajen kare jikin dan adam daga kamuwa da cuta sannan yana warkar da cuta na ciki da wajen jikin bil’adama idan ana ta’ammali da cin sa sosai.


5. Albasa na taimakawa garkuwar jikin namiji ta yadda zai samu Karin kuzari musamman ta bangaren auratayya.


Idan muka dauki ALBASA kadai irin wannan tamu ta Qasar hausa wato RED ONION zamu ga cewa tana Qunshe da Manyan fa'idodi wadanda zasu magance mana wasu daga cikin manyan cutukan da muke fama dasu. Kuma Allah yayi haka ne domin tausayawa garemu.

Albasa tana Qunshe da Sinadarai masu yawa. Irin su Protien, Calcium, Vitamin A, Vitamin B, Vitamin C, Vitamin E, Da kuma wani Sinadarin mai suna Allicin.

Shi wannan ALLICIN din shi ke haddasa idanun mutum yake hawaye, aduk lokacin da ake yanka albasa.

Fresh Albasa (wato danya wacce ba'a dade da cirota ba) tana Kashewa Bacteria, tana maganin Hypertension, Tarin Qwatai, tarin Mura, har ma da ciwon Qoda. etc.

ALBASA tana maganin Shock, Suma, Farfadiya, Ciwon Zuciya, Ciwon Ciki, Ciwon Sugar, Asthma, Gastric Ulcer, da sauransu.

Musamman ma idan an gaurayata da tafarnuwa.

★ Mutumin da ya fadi ya suma, idan aka samu albasa aka fere aka sanya masa akofar hancinsa guda, Insha Allahu wannan Qamshin albasan zai Wartsakar da hanyoyin numfashinsa kuma zai farfado..

★ Don haka ne ake so Majinyatan da suke fama da Matsalar HEART ATTACK su rika yawan cin 'Danyar Albasa acikin abincinsu na yau da kullum.

★ ALBASA tana maganin ARTERIOSCLERIOSIS (wato daskarewa ko Qekashewar Manyan jijiyoyin cikin zuciyar Dan Adam, da manyan hanyoyin jinin da suka Turowa jini da kuma janyoshi daga zuciyar Dan Adam).

★ Don haka tana magance BLOOD PRESSURE kuma tana Qara taimakawa wajen blood circulation (zagayawar jini ajikin Dan Adam).

★ MASU CUTAR DIABETES: Su samu Lansur mai kyau, awankeshi sosai. Sannan ayanyankashi, Asamu garin Qarago (kuli-kuli) cokali 3 tare da Garin hulba cokali guda da rabi.
Barbada Wannan garin, sannan asamu Qatuwar Albasa ('Danya) ayanka aciki.

Insha Allahu wannan abincin idan kana ci kamar sau 2 asati guda, zai zabge maka Sugar wanda ke cikin jininka, kuma zai kore maka Cholestrol daga jikinka.

★ Wanda yake fama da ZAZZABI, ko Mura, ko ciwon makogoro (makoshi) Ya samu zuma rabin kofi ya yanka Qatuwar albasa mai kyau aciki, Sannan ya cinye tare da zuman
Insha Allahu zai samu lafiya da gaggawa.

★ Hakanan mai fama da Ulcer, ko jin zafi alokacin fitsari, shima idan yaci wannan hadin zai samu waraka sosai.

★ Idan mutum yana fama da ciwon goshi ko ciwon kai na gefe daya dinnan, asamo albasa akirba ta tare da tafarnuwa sannan amanna masa akan goshinsa ko daidai wajen ciwon kan..

★ Wanda zuma ta harbeshi, ko cinnaka ya cije shi, ko kunama ta harbeshi, idan aka Manna masa irin wancan hadin sannan aka daure wajen kamar bandeji, shima zai samu waraka da izinin Allah.

★ Wanda yake fama da habo (zubar jini daga hanci) Idan aka sanya masa dakakkiyar albasa yana shaQar warinta insha Allah jinin zai tsaya.

★ Wanda yake fama da matsalar INDIGESTION (rashin narkewar abinci) shima idan yaci danyar albasa zai samu waraka da izinin Allah.

Domin albasa tana taimakawa jikin Dan Adam wajen samar da Sinadaran da suke narkar da abinci.

★ Wanda wuta ta konashi, idan aka kirba albasa aka manna masa awajen, zai ji zafi sosai. Amma kuma wajen zai bushe da wuri kuma zai warke cikin kankanin lokaci.

★ Cin danyar Albasa kullum yakan zama riga kafi ga mata. Saboda breast cancer (Sankaran mama) da colon cancer da kuma sauran cutukan da suka shafi mahaifan mace (diseases of the womb).

Nan zamu tsaya amma zamu ci gaba Insha Allahu.

Post a Comment

0 Comments