ALAMOMIN GANE MASOYIYA/YI TA GASKIYA.




Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

🌹 ki dauka kamar nake ake magana sai ki duba ki gani.

A lokacin da kake ‘ko’karin gano matsayinka a zuciyar budurwarka shin tana son ka ko akasin haka da akwai bu’katar ka nazarci wasu abubuwa wad’anda wasu sun kasance waiwaye ne wasu kuma suna kan faruwa.

🌹 FARKON HA’DUWAR KU.

🌹 YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA. 🌹

  🌹 FARKON HA’DUWAR KU.

A yayin gabatar da soyayyarka gare ta ka yi amfani da salo ne mai karsashi wato sai da ka gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka sannan ka bayyana a gareta da lamari na soyayya?

Furta kalaman amince wa na soyayya ga wanda suke so abu ne da mata suke jin kunyar furta wa a karon farko ga samarin na su, sai dai duk da haka zata ke nuna maka alamun tana son ka kuma zata ke nuna maka wasu alamomi da suke nuni da SO.

Salon da kake bi wajen gudanar da soyayyar ta ku shi ne sikelin auna ci-gaba ko ci-bayan soyayyar ta ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya sai ta samu wani da ya fika iya kalaman soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da dai duk wani salo mai burge wa to babu shakka ko kafi ‘karuna dukiya zai iya d’auke hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da kai dan kud’inka. A saboda haka akwai bu’katar ka kasance mai sabunta salonka na soyayya tun daga kan kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da sauran su lokaci bayan lokaci.

A dukkan lokacin da ka bu’kaci mace ta baka amsar amince wa tana son ka sai ka ga ta yi murmushi ko ta kasa furta hakan a karo na farko to hakan yana daga cikin alamu na SO domin kuwa wanda ake so ake jin kunya.

Karda ka damu da sai ta furta maka kalmar tana son ka kai dai lura da wad’annan abubuwa kamar haka;

🌹 Sau nawa kake kira kafin ta amsa? Idan har da so zata amsa a kira na farko idan kuma bata amsa ba zata amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da zaka gamsu na dalilin.

Post a Comment

0 Comments