ABINCI WANDA ZAI TAIMAKA WAJEN KUZARI YAYIN SADUWAR AURE:



Ba wani abu ya sanya mu rubutu a wannan bangaren ba, sai irin koken da muke ji daga gurin ma'auratan da matsala rashin sha'awa ko kuzarin ke ciwa tuwo a kwarya.

Allah kuma ya hore abinci kala kala da kuma kala kalar kayan itatuwa wanda muke amfani dasu yau da gobe ma bamu san amfaninsu ba.

abinci kala-kala amma da yawanmu ba mu san yadda za mu ci gajiyar su ba, wajen inganta lafiyarmu. Wannnan yasa muka ga ya dace a kawo muku wannan MANHAJA.

1-KANKANA -WATER MELON
A wani sabon babi na masu binciken lafiyar dan adam an sake gano cewa Kankana -watermelon-

Manazarta sun yi bayaanin ta yadda kankana ke kara kuzari ga namiji, saboda wasu muhimman sanadaran da ta ke kunshe da su, harma wasu sukan misalta ta da irin magungunan jima'i da wasu ke sha.

2-YAJI-PEEPER
Masana kiwon lafiya jikin dan-adam da jima'i ba. Yadda al'amarin yake yayin da sha'awar mutum ta motsa, hanyoyin jini da ke jikin al'aurarsa sukan bude sai jini ya kwarara, hakan ya ke sanya al'aurar ta sa yin karfi har ya samu damar gabatar da jima'i ba tare da matsala ba.

Da irin wannan aiki a jikin dan-adam. Amma ba ana nufin mutum ya debi yaji ya sha ba, a'a zai hada shine da abinci. Haka nan kuma ana fadakar da mutane wajen takaita amfani da shi,musamman ga wadanda idan sun ci da yawa zai haifar musu da wata matsalar.

3- CITTA-GINGER
Ita ma citta tana aiki ne kwatankwacin na yaji,amman de ba ainihin zallar yajin ba,to amma Kamar yadda yaji ke taimakawa wajen kwararar jini zuwa ga al'aura namiji, haka ita ma ta ke yi. Sai dai kari akan na barkono ita tana kara lafiyar hanyoyin jinin.

Sannan ai dinga shan lemon ciitar idan an samu damar yin haka a kalla a wata sau 2-3 sau biyu zuwa..

4- YAYAN KABEWA-PUMPUKIN SEEDS
To har illa yau suma yayan kabewa suma suna taka rawa ta mussamman ta yanda ya dace,kuma suna bada gudunmawa ga Mace da Namiji.
Ba shakka yayan kabewa na kunshe da sanadarai da ke kara sha'awa da kuma kuzari ga namiji.

5- AYABA-BANANA
Manyan Masana lafiyar gaba sun gano cewa itama ayaba tana kunshe da sinadarin kamar irinsu potassium, hakan ya sa masanan suka bayyana yadda ta ke karawa namiji kuzari, musamman idan ya ci mintuna kadan kamar minti 35haka kafin saduwa da iyali.

To tabbas zata bada gudunmawa tamussanman.
 
6-DANKALIN TURAWA -POTTATOES
DANKALIN HAUSA-SWEET POTATOES
To zaka iya amfani da kowanne kalar dankali ko namu na hausa ko kuma dankalin turawa-duk kusan amfanin su daya.

Dankali ko na gargajiya ko na turawa shima yana kunshe da sinadari potassium da ke inganta karfin mazakutar namiji, hakan kuma na inganta saduwa tsakanin ma'aurata.

7- GYADA-GROUNDNUT
Ta wannan bangare kuma itama gyada tana taka rawar gani na mussan a wannan bangare sannan kuma tana dauke da wani sinadari ta ke kunshe da shi da ake kiran sa amino acid L-arginine da turanci, shi wannan sinadari na taimakawa wajen dadewar gaban namiji a mike.

8- TAFARNUWA-GARLIC
Ta wannan fuska ma manazarta sun samo sakamakon binciken alfanun tafarnuwa da amfanin da tafarnuwar take a wajen daban daban ,don gudanar da magungunan matsalolin jiki daban-daban. Har zuwa wannan zamani da masana suka gudanar da bincike na zamani don tabbatar da irin alfanunta ga lafiyar dan-adam.

 Binciken zamanin ya tabbatar da cewa ita tafarnuwa na gyara hanyoyin jini, kuma mun bayyana a sama yadda gudanuwar jini ke da alaka da mikewar gaban namiji. Hakanan tana gyara zuciya wadda itama an san aikinta na wajen tunkuda jini cikin jiki. Don haka wannan na bayuwa zuwa ga karfin al'aura yayin jima'i.

9- KWAII-EGG
Wannan bama sai an fada ba kowa yasan ansha fadar fai'idar kwaii da kuma illahirin dukkan sinadarai masu gina jiki da yake dauke dasu dama sauransu wanda bazamu iya kawo su ba a cikin kankanin lokaci ; Game da jima'i kuwa akwai sinadaran B6 da B5. Bincike ya nuna wadannan sinadarai suna kawar da damuwa, su kuma inganta sha'awa jima'i ga namiji.

 SHAWARA
Fadakarwa: Anan fa ba ana nufin cewa sai an ci ko anyi amfani da dukkan wadannan abinci-kayan marmari da muka ambata ko muka kawo muku ba, a sama ba ne don samun fa'ida a'a za'a iya jarraba wasu daga ciki, kuma ana son yawaita cin su ne in banda ayaba, kankana, kwai musamman danye, da ake son aci lokaci kadan kafin saduwa da iyali,ko kuma a duk lokacin da ake da damaryin hakan..


Post a Comment

0 Comments