AMFANIN GANYAN MANGURO:




Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al’ummar musamman a wannan zamani. Ire-iren wannan sunadarai sun hada da:
- Alkaloids
- Phenols
- Flavonoids
- Saponins
- Tannins
- Calcium
- Magnesium
- Potassium
- Phosphorus
- Sodium
- Copper
- Zinc
- Cadmium
- Ascorbic acid
- Riboflavin
- Niacin
- Thiamine

A sakamakon wannan arziki na sinadarai da Allah yayiwa ganyen mangwaro Yana maganin wadannan cututtukan: 

1- Ciwon Suga

Ganyen mangoro yana daidai ta suga, sabida yana dauke da sinadarai masu saka jiki ya saki insulin.

Ana iya jika ganyen magwaro a cikin ruwa ya kwana sai ayi amafani da shi yana taimaka wajen daidai ya suga.

Haka Kuma za'a iya barin sa ya bushe sannan a maida shi gari adinga amfani dashi domin daidai ta suga.

2- Hawan Jini

Kasancewar ganyar mangiro yana dauke da sinadaran vitamin hakan zaisa ya kona cholesterol mara amfani a jikin mutum, sannan ya daidai ta jinin mutum.

3. Matsalarar Koda

Ana dafa ganyan mangoro kamar shayi a dinga sha da safe a matsayin abincin farko yana kawar da matsalar Koda, kuma yana narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka.

4- Matsalar Kirji ( Respiratory Track Infection)

Ana iya dafa ganyan mangoro kamar shayi sannan a saka zuma a ciki ana amfani da shi ya saukake matsalar tari da rike kirji.

5- Cutar Atini

Akan kwankwadi garin ganyen Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini.

Post a Comment

0 Comments