Hanyoyi 60 Da Zaka Dawwamar Da Soyayyar Matarka
1. Ka zamo mai tausasa zance a gareta, kar ka zamo mai yawan fada.
2. Idan ka shiga gida kace ‘Assalamu Alaikum’, sallam tana korar Shedan daga gida
3. Annabi SAW yace mata kamar kayan qarau ne saboda haka kula dasu sosai, ka tuna akwai alkhairi a cikinsu saboda haka sai a tarairayesu.
4. Idan zaka bata shawara ko zaka yi mata fada ya zamo a cikin sirri, wato alokacin da kuke ku kadai, kada ya zamo a cikin mutane dan yin hakan muzantawa ne.
5. Ka zama mai kyautatawa matarka, hakan yana qara soyayya
6. Idan tazo zata zauna ka tashi ka bata wurin zamanka, hakan zai tausasa zuciyarta.
7. Ka guji yin fushi ta hanyar riqe al’wala a koda yaushe. Annabin Rahma SAW yace idan kayi fushi to idan a tsaye kake sai ka zauna, idan a zaune kake sai ka kwanta.
8. Ka rinqa yin ado kana sa turare saboda ita.
9. Karka zamo mai tauri, Annabi SAW yace : ‘Nine mafi kyautatawa zuwa ga iyalina’, idan kayi tauri da yawa baza ka samu kusanci zuwa ga Allah ba, haka kuma baza ka zamo namiji jarumi ba.
10. Ka dinga sauraron duk abinda matarka zata gaya maka koda kana ganin abin bashi da muhimmanci, hakan zai sa ta san ka damu da ita.
11. Ka kaucewa cin musu da matarka, yana kawo rabuwar kai.
12. Annabi SAW yace ku kira matanku da sunaye masu dadi, sunan da suke so suji ka kira su dashi.
13. Ka riqa yi mata tsarabar bazata, idan tana sha’awar wani abin marmari sai ka sayo mata ba tare da ta sani ba.
14. Ka kula da harshenka zuwa gareta, wato ka guji abubuwan da zasu sa ta fushi.
15. Mutum tara yake bai cika goma ba, kayi haquri da duk wani aibun da take dashi sai Allah SWT ya sa albarka a cikin auren naka.
16. Ka dinga nuna mata yabo da godiya idan tayi maka abu mai kyau.
17. Ka dinga taimaka mata wajen ganin ta kula da dangantakar ‘yan’uwanta da iyayenta.
18. Ka yawaita janta da hira akan abinda take so.
19. Idan kaga ‘yan’uwanta suna kusa, ka dinga yabonta, kana kambamata, kana tabbatar musu da kirkinta da kyautatawarta.
20. Ku dinga yiwa junanku kyaututtuka. Manzon Allah SAW yace kyauta tana qara soyayya.
21. Idan kayi mata laifi sai ka samu wani abu ka kyautata mata dashi dan ya goge laifin.
22. Ka rinqa kyautata zato a gareta, banda zargi!
23. Karka dinga kulawa da qananan laifukanta, kayi kamar baka gani/ji ba. Yana daga cikin ‘dabi’un Sayyidina Aliyyu (RA).
24. Ka nin-ninka haqurinka da ita musamman a lokacin da take jinin al’ada.
25. Ka ringa sauraron zuwan kishinta, kuma ka ringa yabon kishin nata, ko manta Manzon Allah SAW suna kishi!
26. Ka zamo mai qasqantar da kai, idan ka zamo mai tunani to ka tuna cewa tana kula da ‘ya’yanka, itace mai kula da gida!
27. Karka dauki abokanka sama da matarka!
28. Ka ringa taimaka mata da ayyukan gida. Manzon Allah SAW ya kasance yana taimakon matansa.
29. Ka taimaka mata wajen girmama iyayenka, baza ka iya takura mata taso su ba amma zaka iya taimaka mata dan ta cimma hakan.
30. Ka dinga nuna mata cewa itace irin matar da kake ta addu’ar ka samu.
31. Karinga tunawa da matarka a cikin addu’o’inka, hakan zai qara qarfin soyayyar taku.
32. Kada ka dinga tunawa da baya, babu abinda hakan zai jawo sai damuwa, abinda ya riga ya wuce a barwa Allah.
33. Karka taba nuna mata cewa taimaka mata kake idan kana mata wani abin kamar sayan abincin gida, saboda a zahirin gaskiya mu ‘yan aikatarwa ne kawai, Allah shine yake azurtawa da ciyarwa. Wannan kuma wata hanya ce ta qasqantar da kai ga Allah SWT da kuma gode masa.
34. Ka gane cewa Shaidan maqiyinka ne amma ba matarka ba, wani lokaci idan mata da miji suna magana idan suka samu sabani sai Shaidan ya shiga tsakani. Kayi iya qoqarinka wajen ganin Shaidan bai shiga tsakaninka da matarka ba.
35. Ka ringa bata abinci a baki, Annabin tsira SAW ya koya mana hakan, abincin ba wai iya cikinta zai tafi ba idan ka bata a baki, har zuwa cikin zuciyarta.
36. Ka kare matarka daga duk wani sharri ta hanyar yi mata addu’o’in neman tsari.
37. Ka zamo mai yawan yi mata murmushi.
38. Ka guji duk abinda bata so ko mai qanqantarsa, idan baka kula ba ta haka ne zai girma har ya zama babba.
39. Ka guji yin fushi da fada a gareta, yin hakan yana rage shaquwa.
40. Ka dinga yin maraba da shawarta.
41. Ka taimaka mata wajen samun nasara a harkokinta na rayuwa.
42. Kullum ka zamo mai qara kusantuwa zuwa gareta.
43. Ka taimaka mata wajen kula da yara. Wasu mazan suna ganin kamar ba aikin su bane kula da yara, basu san cewa yin hakan ne ma zai sa su qara kima da daraja a idon matan da yaran ba.
44. Ka ringa yi mata dadin baki da magana mai taushi.
45. Ka ringa cin abinci tare da ita.
46. Duk lokacin da zaka yi tafiya ka sanar da ita, haka kuma ka gaya mata rana da lokacin da zaka dawo.
47. Kada ka fita daga gida a lokacin da kuka samu sabani.
48. Gida yana da sirri kala-kala, idan ka zamo mai fadan sirrin gidanka a cikin mutane to kana yi wa kanka zaqon qasa ne. Sirrin gida ya tsaya a cikin gida.
49. Ku dinga qarfafawa junanku wajen yin ibada, ku dinga shirya zuwa Hajji ko Umrah a lokacin da kowa bai takura ba (misali a lokacin da bata da ciki kuma bata shayarwa) idan Allah ya baku iko.
50. Ka kula da haqqoqinta na aure
51. Allah SWT yace : « ku zauna da matanku cikin kyautatawa », ka dinga riritata kamar qwai.
52. Idan aka zo kwanciyar aure kada kayi mata ‘hawan qawara’, kuyi wasan tayar da sha’awa tukuna.
53. Idan kun samu sabani da matarka, kada ka gayawa kowa, idan kayi haka kamar kabar ciwo ne a bude quda ya hau.
54. Ka nunawa matarka cewa ka damu da lafiyarta. Lafiyar matarka lafiyarka ce. Idan ka kula da lafiyarta hakan ya nuna kana sonta.
55. Karka dinga tunanin ko yaushe kana da gaskiya, mutum tara yake bai cika goma ba.
56. Ka ringa sanar da ita lokacin da kake cikin matsala, farin ciki ko damuwa.
57. Ka dinga yafe mata idan tayi ba dai dai ba.
58. Kake yawan tuna cewa kaine bango wajen jinginarta a lokutan wahala ko qa-qa nakayi
59. Ka karbi matarka da duk halin da take tashi, Mazon Allah SAW yace an hallicci mata ne daga qashin qirji tanqwararre, idan kayi qoqarin ka tayar dashi zai karye!
60. Ka zamo mai kyakykyawan zato ga matarka a koda yaushe, Allah yana kula da niyyarka zuwa gareta a koda yaushe. Allah madaukaki yace:
“Kuma daga ayoyinsa ne cewa ya halitta muku matanku daga gareku, kuma ya sanya qauna da tausayi a tsakaninku, haqiqa a cikin wannan akwai ayoyi ga masu zurfin tunani” (Q. Rum 21)
Ya Allah ka bamu abokan zama nagari, masu tsoronka da yi maka da’a, kuma masu kyawun gani.
Hikimomi da dabarun da maigida zai bi ya kyautata wa matarsa
Babu macen da ba ta son mijinta ya rika ji da ita, yana nuna mata soyayya da girmamawa. Yin haka na kara wa mace jin ta fi kowace mace ko jin ta a saman duniya, sannan duk yarintar mace ko tsufanta tana son mijinta ya rika daukarta a matsayin ’yar karamar yarinya, wadda na taba bayani a kan hakan. Ma’ana ya rika kula da ita kamar yadda zai kula da karamar yarinya, ya rika tunawa da kuruciyarta da ya sani a da kafin ya aure ta.
Saboda haka idan ba ka yin haka, to daga yau ka fara, don matarka ta rika jin ita ma ta kai mace, ta samu farin ciki da jin dadin zaman aure. Na tabbata yin hakan na bayar da kwanciyar hankali a cikin gida, sannan yana kara dankon soyayya sosai.
Ka rika kula da irin sabon kayan da take sa wa ko wani sabon abu da ta canja, kamar yin kitso, kunshi da kwalliya sai ka yaba da nuna burgewa a tare da kai. Duk wani sabon canji da ka gani yana da kyau ka san da shi, idan na yabawa ne, ka yaba, idan kuma na magana ne ka yi. Wannan shi ne zai kara tabbatar mata da cewa kana damuwa da ita.
Kalmar yarinta kada ta rabu da bakinka, kamar Bebita, ka rika sa wa tana jin a kullum ita ’yar karamar yarinya ce a wurinka. Wani lokacin ma ka kira ta da sunan da ka san babanta ko babarta suke kiran ta da shi a lokacin da take karamar yarinya, sannan ka fada mata kalaman yabawa masu dadi da cewa tana da kyan tsari.
Sai kira in ka fita ofis, ka kira matarka duk lokacin da ka kai ofis. Sai ka fada mata cewa: “Na kira ne don in tabbatar da jin lafiyarki.” Yin hakan na sa ta san cewa tana da muhimmancin gaske a wurinka sosai.
Wata rana ka ba ta hutun shiga kicin, kamar ranar da babu aiki, sai ka shiga ka dafa abincin da za ku ci ko in ba zai yiwu ba sai ka fitar da iyalinka wani wurin birgewar da za su dade suna tunawa. Zuwa sayayya tare ko zuwa wurin hutu da shakatawa, ka rika kulawa da ita kamar kwanan nan ka hadu da ita, wato kamar wata sabuwar budurwarka.
Kulawa ta musamman, idan tana son yin magana da kai, ka juya ka saurare ta da kyau. In kana karatun jarida ko kallon talabijin sai ka rufe. Haka in an bugo waya kuna cikin tattaunawa, kar ka dauka ko kuma ka kashe kafin ku fara tattaunawa. Ka saurare ta da kunnen basira kamar yadda kake yi da in ka je zance. Sannan ka rika nuna alamun kana ji da kyau ta alamun gyada kai, murmishi ko amsawa. Sauraren abin da mace ta fada na daya daga cikin abin da ke sa wa ta kara girmama ka.
Ka matso da ita kusa da kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da take fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sa wa ta dan huce ko ta samu sauki. Ka sanya ta ji kamar ’yar yarinya karama a kirjinka. Ka bar ta har ta yi barci daga nan ne za ka gane irin baiwar da Allah Ya yi mata da kyanta da kai kanka baiwar da Allah Ya ba ka.
Zama a gida ranar da babu aiki don kawai ka kasance tare da ita, sannan ta san kana tare da ita ne ba don kamai ba sai dan kana son ka zauna da ita. Ka yi hira, wasanni, maganganun da za su sa ta ji dadin wannan kasancewar da ka yi da ita, tun da na sha ganin matan da ba su son mijinsu yana gida sai in lokacin da zai yi barci.
Yana da kyau wata rana ma ka kulle ta a daki, don kar yara su dame ta sannan kar ka bar su su shiga har na kamar tsawon awa shida, kawai don kana son ta yi barci ta huta. Sai kai ka kula da yara na dan wannan lokacin, ka fahimtar da su cewa innarsu na bukatar hutu, bari ita ma ta dan ji dadin rayuwarta. Sai ka yi girki ka kai mata daki ta ci gaba da hutawarta, babu abin da yake sa a ji dadin soyayya face irin wadannan abubuwan. Na san wani zai ce shi yaushe yake da lokacin hakan, ko ya ce in ya yi haka ai ya bayar da kansa ga matarsa, za ta raina shi. Wallahi babu maganar raini, tun da wanda aka yi duniyar ma dominsa na tabbata kowa ya sami labarin irin was an da yake da iyalinsa. Saboda haka ka zama miji nagari.
Ka matso da ita kusa da kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da take fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sa wa ta dan huce ko ta samu sauki.
SIRRIN MAZA
☏+2348037538596
Sirrin rike miji
Hakika namiji yana da wani sirrin Wanda ba kowacce mace ta San wadannan sirrin ba Sai wacce Allah ya sanar da ita, shi namiji ya kasance Mai tsanani son karairaya, rangwada, kissa,shagwaba, da kalaman soyayya, duk macen data San wadannan kuma take aikatasu hakika zata zama tauraruwa a zuciyar mijinta.
Babu ko shakka wadannan kam Na Daga cikin abubuwa mafi muhimmanci dake taka muhimmiyar rawa wajen sace zuciyar namiji ,ya kasance kin tanadi wani suna Na musamman da Zaki dinga kiran mijinki dashi kamar:
● sweety
● honey
● darling
● Abin kaunata
● farin cikin rai Na.
Magana ta gaskiya a wannan fannin a nan ne aka yiwa matan hausawa nisa , don da yawa sune basu dauki hakan a wani Abu Mai muhimmanci dake Iya jefa tsantsar sonki a zuciyar mijinki ba.
Dole a matsayin ki Na macen da ke son ta mallaki mijinta saifa ta dage wajen Iya kalaman soyayya don sune masu kwantarwa da namiji hankali koda kuwa an bata masa rai KO hankalinsa ya tashi.
Sannnan yana Daga cikin namiji ki Iya gabatar da zahirin soyayya, hakika tsakaninki da mijinki bafa jin kunya, ki Saki jikinki ki nuna masa soyayya, domin duk wani hade-hade da manne-manne da zakiyi idan Har baki Iya kalaman soyayya ba da ita kanta soyayyar to gaskiya da sauranki Dan Neman Karin bayani.
☏+2348037538596
・ sirrin rike miji
0 Comments