Yadda Ake Mayar Da Mata ’Yanlele.
☏+2348037538596
@sirrinrikemiji
Babu macen da ba ta son mijin ta ya rinka ji da ita, yana nuna mata soyayya da girmamawa. Yin haka na kara wa mace jin ta fi kowace mace ko jin ta a saman duniya, sannan duk yarintar mace ko tsufanta tana son mijinta ya rinka daukarta a matsayin ‘yar karamar yarinya wadda na taba bayani a kan hakan. Ma’ana ya rinka kula da ita kamar yadda zai kula da karamar yarinya, ya rinka tunawa da kuriciyarta da ya sani a da kafin ya aureta.
Saboda haka idan ba ka yin haka to daga yau ka fara don matarka ta rinka jin ita ma ta kai mace, ta samu farin ciki da jin dadin zaman aure. Na tabbata yin hakan na bayar da kwanciyar hankali a cikin gida, sannan na kara dankon soyayya sosai.
Rinka kula da irin sabon kayan da take sawa ko wani sabon abu da ta canja, kamar yin kitso, kunshi da kwalliya sai ka yaba da nuna birgewa a tare da kai. Duk wani sabon canji da ka gani yana da kyau ka san da shi, in na yabawa ne ka yaba in kuma na magana ne ka yi wannan shine zai kara tabbatar mata da kana damuwa da ita.
Kalmar yarinta kada ya rabu da bakin ka, kamar Bebita, ka rinka sawa tana jin a kullum ita ‘yar karamar yarinya ce a gurinka.
Wani lokacin ma ka kirata da sunan da kasan babanta ko babarta suke kiranta da shi a lokacin da take karamar yarinya, sannan ka fada mata kalaman yabawa masu dadi da cewa tana da kyaun tsari.
Sai kira in ka fita office, ka kira matarka duk lokacin da ka kai office sai ka fada mata na kira ne don in tabbatar da jin lafiyar ki. Yin hakan nasa ta san tana da muhimmancin gaske a wurinka sosai.
Wata rana ka bata hutun shiga kitchen kamar ranar da babu aiki, sai ka shiga ka dafa abincin da za ku ci ko in ba zai yiwu ba sai ka fitar da iyalinka wani wurin birgewar da za su dade suna tunawa. Zuwa sayayya tare ko zuwa wurin hutu da shakatawa, ka rinka kukwa da ita kamar kwanan nan ka hadu da ita wato kamar wata sabuwar budurwarka.
Kulawa ta musamman idan tana son yin magana da kai, ka juya ka saurareta da kyau in kana karatun jarida ko kallon talabijin sai ka rufe haka in an bugo waya kuna cikin tattaunawa kar ka dauka ko kuma ka kashe kafin ku fara tattaunawa, ka saurare ta da kunnen basira kamar yadda ka ke yi da in ka je zance. Sannan ka rinka nuna alamun kana ji da kyau ta alamun gida kai, murmishi ko amsawa. Sauraren abin da mace ka fada na daya daga cikin abin da ke sawa ta kara girmama ka.
Ka matso da ita kusa da kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da take fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sawa ta dan huce ko ta samu sauki. Ka sa ta ji kamar ‘yar yarinya karama a kirjin ka. Ka bar ta har ta yi barci daga nan ne za ka gane irin baiwar da Allah ya yi mata da kyaun ta da kai kan ka baiwar da Allah ya baka.
Zama a gida ranar da babu aiki don kawai ka kasance tare da ita, sannan ta san kana tare da ita ne ba don kamai ba sai dan kana son ka zauna da ita, ka yi hira, wasanni, maganganun da za su sa ta ji dadin wannan kasancewar da kayi da ita, tunda nasha ganin matan dabasa son mijin su yana gida sai in lokacin da zai yi barci.
Yana da kyau wata rana ma ka kulleta a daki, don kar yara su dame ta sannan kar ka bar su su shiga har na kamar tsawon awa shida kawai don kana son ta yi barci ta huta, sai kai ka kula da yara na dan wannan lokacin, ka fahimtar da su cewa babar su na bukatar hutu bari ita ma ta dan ji dadin rayuwarta. Sai ka yi girki ka kai mata daki taci gaba da hutawar ta, babu abin da yake sa aji dadin soyayya face irin wadan nan abubuwan. Na san wani zai ce shi yaushe yake da lokacin hakan ko ya ce in ya yi haka ai ya bayar da kansa ga matar sa za ta raina shi. Wallahi babu maganar raini tunda wanda a kayi duniyar ma dominsa na tabbata kowa ya sami labarin irin wasan da yake da iyalin sa. Saboda haka ka zama miji nagari.
Bayan ka san ta sha gajiyar hayaniyar yara da aiki kitchen da daddare, sai ka sa ta kwanta don ka yi mata kyakkyawar tausa tun daga yatsu har zuwa kai, na tabbata za a ba ka kyautar da ba’a taba yi ma ba in dai har a ka ji dadin wannan tausa.
Sai bayan cin abincin dare, in an gama cin abincin dare da yara sai ka juya ka kalli yara ka yabi girkinta, sannan ka ce yaran duk su tashi su tafa wa babarsu, kuma su gode mata su gaya mata ‘Umma abincin ki ya yi dadi, gaskiya kin iya girki babu kamar yake.’ Sannan ka sa kowa ya rungume ta suna masu gode mata. Yana da kayu ka rinka yin haka lokaci lokaci.
Abin birgewa ne yadda wasu samarin suke kula da ‘yan matan su kafin aure, in aka lura da yadda wasu mazan suke yi da matan su na gida, ina nufin yadda wasu mazan ba su kula da matan su in suka kawo su gida ba tare da rashin sanin daraja ba ko daukakawa ba. Ya kamata a samu canji na sanin darajarta, girmamawa, so da kauna, rinka fada mata ina kaunar ki ina sonki, ina ganin girman ki da daukar ki da muhimmanci.
Kuma ba fada kawai a baki ba, nuna mata ta fahimta, ta yadda za ka fahimtar da ita din kuma ta gane shine. Ka bar yin komai hankalin ka ya dawo kanta gaba daya ka kula da ita a matsayin ta na sarauniya, macen da ka damu da ita kamar lokacin da take sabuwar budurwar ka. Lallaba ta kamar kwai za ta zamo maka abin alfahari da daidato a tare da kai da samun soyayya tagari irin wacce ka ke sha’awa.
Ka zama mai yi mata kyauta kowane karshen wata, kai inda hali ma ko wane karshen sati, Zai iya kasancewa kuma sai zagayowar watan haihuwar ta. Ita soyayya tana son abubuwan da za su ringa kara mata zaki ko dadi da mando, kamar a girka miya ce daga gishiri babu komai yaya miyar nan za ta kasance? Amma idan aka zuba mata magi da daddawa fa da sauran kayan kanshi ai dole ta yi dadi. To itama soyayya haka take tana son ana kara barbada mata kayan dadi da kayan kamshi, yin kyautar nan kuwa na kara sa soyayya ta kara zaki matuka. Ba dole sai babbar kyauta ba tunda daga karami na iya komawa babba wata rana, tasirin kyautar shi ne kara zakin soyayyar,tun daga kan agogo, sarka ne, kayan sawa ne, su man shafawa da turare ko kayan kitchen ne, wata rana ma a hankali har sai a sayi mota da sauransu. Ka tuna fa masoyiyar ka ce sannan abokiya zamanka kuma matarka.
Yawaita fadan dadadan kalamai game da ita a gaban jama’a, yabon ta a gaban jama’a na kara dagata da sa ta jin dadi. Saboda haka ka ringa nuna muhimmancinta da irin yadda ka dauketa da irin jin dadin da ka ke yi na haduwar ka da ita. Kar ka yarda ka kalubalance ta a gaban jama’a ko ka bata ta a gaban su.
ZAMANTAKEWA AURE:
Abinda ake nufi da zamantakewa shine mace ta zama mata ta gari, mutuniyar kirki wacce duk al’umma suka shaideta da mutuntaka a zamanta na aure. Kula da Maigida, yara, iyayen miji da kuma malamanta da ma sauran mutane baki daya. Daga cikin abubuwan da zasu taimakawa mace ta zama ta gari sun hada da :
1. Bin dokokin aure.
2. Bayar da haqqoqin aure.
3. Kyakykyawar mu’amala da miji, ‘ya’ya, iyayen miji, dangin miji da sauran jama’a, mu sani duk wanda ya auri mace to fa ya aureta ne harda danginta, kamar yadda itama ta aure shi ne harda danginsa.
4. Haquri da yawan yafiya tare da kawar da ido akan wadansu abubuwa.
5. Neman shawara daga mutanen kirki, masu hangen nesa da nutsuwa da kuma aiki da shawarar da aka bata.
6. Baiwa Maigida shawara a kebance, ma’ana ba a cikin jama’a ba, kinga ko da bai karbi shawarar ba abin ba zai zamo matsala ba.
7. Rashin saurin fushi da kuma qoqarin kawar da fushi, kamar yadda yake a maganar Mazon Allah S.A.W : Idan kayi fushi idan kana tsaye to ka zauna, idan kuma a zaune kake sai ka kwanta, kuma kayi alwala.
8. Baiwa Maigida cikakken saurare, ki zama mai kyakykyawan saurare.
9. Sallamawa ga shawararsa matuqar bai sabawa Allah da Manzonsa ba, da kuma rashin jayayya da shi, sabanin wasu da qawayensu ne kadai keyi musu jagora da zuga.
10. Kiran Maigida da suna mai dadi ko kuma sunan da yafi so (kamar su sweety, darling, honey, angona, maigidana, nawan, my only one, Sahibina, sirrin zuciyata, hasken idona dss), kamar yadda Manzon Allah S.A.W yake kiran Nana A’isha da Ayish !
11. Yiwa Maigida kyautar bazata, kamar tufafi, abinci, abinsha, ‘greeting card’, turare da kuma yafiya akan laifi mafi girma wanda yake zaton za’ai tashin hankali akai.
12. Ki zama kina kiyaye harshe, tare da lura da abinda zaki fada, domin Manzon Allah S.A.W yace harshe zai jefa mutane a cikin wuta. 13. Yiwa Maigida uziri a inda ya gaza da nuna masa godiya ga duk abinda yayi ko ya kawo.
14. Qarfafa masa gwiwa wajen qulla zumunci da ‘yan uwansa, kamar iyaye dss.
15. Yawaita hira da shi da irin abinda kika san yafi daukar masa hankali ko kuma yafi so.
16. Yabonsa a gaban iyaye, ‘yan uwa tare da jinjina masa
17. Taimaka masa a gurin girmama iyayensa da naki
18. Kyautata zato a gareshi da kuma rashin dogon bincike a gareshi, kamar bincike a wayarsa (handset) da shiga cikin saqonninsa (messages) dss.
19. Karki fifita abokan miji akan miji, ballantana qawayenki!
20. Ki riqa nunawa Maigida cewa yana da hikima da dabara a cikin al’amuransa.
21. Mantawa da abinda ya wuce don baya jawo komai sai bacin rai
22. Tunawa da shi a cikin addu’a
23. Kulawa da ‘ya’yansa wadanda ba ke kika haifesu ba.
24. Ba da kyauta ta mamaki ga iyayensa ko wadanda suke a matsayinsu
25. Kulawa da wurin kwanciyarsa da kuma koyan salo daban-daban na kwanciyar aure, tare da tausaya masa idan kina al’ada, in har kina da abokiyar zama ki bashi damar ya tafi koda bai nema ba, in kuma ke kadai ce to ki bi hanyoyin da zaki kawar masa da sha’awa wadanda shari’a ta yarda da su.
@ SIRRINRIKEMIJI
0 Comments