MAGANIN WARIN HAMMATA GA NAMIJI KO MACE



Tsananin zafin rana da ake samu a lokacin rani yana haifar da gumi, wanda hakan ke haifar da bayyanar wani wari mai banƙyama.

Sau da dama mutanen dake fama da wannan warin yana zamo musu abin kunya, ko a wurin aiki, a cikin ababen hawa na haya, ko a wasu wuraren taruwar mutane daban-dabann.

Domin magance wannan matsalar, zamu gabatar da hanyoyi na dabi'a da za'ayi amfani dasu don kawar da wannan wari.

■ Farin khall tufa (white vinegar) don kawar da mummunan warin jiki:

Ruwan khal yana taimakawa wajen rage pH na jiki, wanda hakan ke hana kwayoyin cutar bacteria yaduwa, saboda ba za su iya rayuwa a cikin yanayi mai acidic ba.

Ana amfani dashi ta hanyar tsoma auduga a cikin ruwan khal daga nan kuma sai a shafa shi a karkashin hammata, ko kuma ana iya diga farin khal a cikin ruwa sai a wanka hammata dashi sosai don samun sakamako mai kyau.

■ Lemon tsami don kawar da warin jiki mara dadi:

Ana shafa lemon tsami kai tsaye a cikin hammata sannan a dauraye shi da ruwan, ko kuma ki zuba wani adadi na ruwan lemun tsami a cikin ruwan wanka zai taimaka miki sosai wajen kawar da warin jiki. 
Ko kuma ki kwaba ruwan lemon tsami da baking soda ki shafa a hammata, daga nan kuma sai kiyi wanka don samun sakamako mai kyau.

■ Man tea tree (tea tree oil) don magance warin jiki:

Man tea tree ana siffanta shi a matsayin mai mai karfin gaske, sannan kuma yana dauke da sinadarin antibacterial wato yana kashe kwayoyin cutar bacteria.

A saboda haka, zamu iya yin amfani dashi a madadin deodorant, ta hanyar zuba shi a cikin ruwa sannan a wanke jiki dashi sau biyu zuwa uku don kawar da warin jiki.

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA,LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

0 Comments