Yadda Zaki Zauna Da Uwar Mijinki Lafiya


Yadda Zaki Zauna Da Uwar Mijinki Lafiya:

#Tsangayarmalamtonga 

Surukai, musamman iyayen maza suna taka rawa wajen inganci auren dansu ko wargaza zaman auren.

Ana samun ma'aurata suna matukar son junansu, basu da wata matsala da junansu amma sai uwar miji ta shiga ta fita har sai ta raba wannan aure.

Ana samun wani lokacin matsalar na bullowa ne daga wajen su matan, wasu lokutan kuma iyayen mazajen nasu ne da kansu suke zama fitinannu ko basa kaunar ita matar dan nasu.

Ga wasu hanyoyin da zaki iya zama da uwar mijinki lafiya.
 
1: Idan kina son zama lafiya da uwar mijinki, to ki guji nunawa kece kike da iko akan mijinki fiye da uwarsa.
Babu abunda yake bakantawa surukai mata haushi irin matar dansu ta nuna uwarsa batada Iko a kansa sai ita.

Don haka koda wasa, ko a gabanta, ko a gaban wasu da zasu iya zuwa su fadamata kada ki kuskura ki nuna ko ki furta wata magana da zai nuna kece kika isa da mijinki amma ba uwarsa ba. Muddin zaki kiyaye hakan to zaki zauna lafiya da mijinki.

2: Akwai matan da suke barin mazansu su rika musu sayayya kayan masu tsada, amma sai su bari a saiwa uwar mijinta masu arha. Muddin uwar miji ta ankara ko aka ankaran da ita zata iya samun matsala da uwar mijinta.

Kada ki bari mijinki ya rika fifitaki fiye da uwarsa. Ki tabbatar duk wasu kaya na jin dadi da zai kawo muku gida ya samo sayawa mahaifiyarsa kamin ku. Da haka ne zaki iya samun zaman lafiya da uwar mijinki.

3: Idan kina son zaman lafiya da uwar mijinki ki rika zama da ita kina neman shawararta.
Koda kuwa kin riga kin yanke shawara akan abun, nuna mata shawaranta kike nema tare da sanya albarkarya akan wannan abun.
Da irin hakan ne zata fahimci kina daukarta a matsayin uwa, ba uwar miji ba. Hakan kuma zai sa ki kara shiga ranta sannu a hankali.

4: Uwar miji tana son ganin jikokinta kusa da ita kuma suna nuna mata kauna.
Wasu matan kan yi kokarin ganin sun nisanta 'ya'yansu da kakansu, wanda hakan ke jawo takun saka tsakaninta da uwar mijinta.
Ki cusawa yaranki kaunar kakarsu. Ki nuna musu mahimmancinta a gunsu. Ki sa su shiga jikinta. Muddin kin samu nasaran yin hakan to kema albarkacinsu zaki samu soyayyar ta.

5: Kada kije kina yin kananan maganganu ko gulma akan uwar mijinki.
Mata ba a rabaku da yawan korafi ko gulma. Wannan gulmar ko da mahaifiyarki kika yi zai iya fitowa fili ta hanyar wasu data sanar dasu abunda kika fadamata akan uwar mijinki.

Don haka muddin kina son zama da uwar mijinki lafiya. Ya kasance kinyi gum da bakinki wajen furta duk wani kalami mara dadi akanta. Wannan zai sa ko tana da wani kulli a ranta bazata samu damar diran miki ba.

Post a Comment

0 Comments