Makarin Matsananciyar Sha’awa ga matasa maza ko mata





Assalamu Alaykum wa rahmatullah, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo…

Daga
Olusegun Mustapha


Assalamu Alaykum wa rahmatullah, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani da zai amsa tambayoyin da da masu karatu matasa suka aiko kan yadda za su magance matsalar matsananciyar sha’awa da ta addabi rayuwarsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Tambaya

Malama Nabila don Allah ki yi man bayani game da mutum mai yawan jin sha’awa kuma ga shi babu yadda za ai gidansu a yi masa aure saboda karatu ga shi kuma yana jin tsoron aikata fasikanci don ya san hukuncin wanda ya yi haka wurin Allah; don Allah wadanne hanyoyi zai bi don magance matsalar? Daga Haidar.

Amsa: Ga hanyoyin da matashi zai bi don yakar matsananciyar sha’awa ya kasance ba ta kai shi ga fada wa cikin halaka ba:

Fahimta Kyakykyawa: Abu na farko na maganin wannan matsala shi ne ta hanyar yi mata cikakkiya kuma kyakykyawar fahimta:

Ø Matsananciyar sha’awa wani yanayi da sha’awar mutum ke yawan motsuwa nan da nan kuma kusan kowane irin lokaci, musamman a lokuttan da ba ya bukatar motsuwarta. Wannan yanayi yana faruwa ga duka masu aure da marasa aure, maza da mata, kuma yana takurawa ga rayuwarsu, sannan yana jefa wasu ga yin zinace-zinace; zinar hannu da kallon fina-finan batsa, wadanda duk wasu muggan ayyuka ne da ba su kawo sauki ga matsalar sai dai su kara ruruta ta, sannan suna kawo bakantar dabi’ar masu aikata haka da raunana masu imaninsu.

Yana da kyau ga mai fama da matsananciyar sha’awa ya fahimci cewa, sha’awa ba komai ba ce illa daya daga cikin al’amuran gudanarwar jikin dan’adam da Allah Ya halitta shi da su. Kamar yadda wani ya fi wani tsawo; wani da saurin fushi wani kuma da sanyin zuciya, to haka sha’awa ta bambanta tsakanin mutane ta fuskoki daban-daban. Kamar yadda mai tsananin fushi Allah Ya hore masa iko da damar dannewa da hadiye fushinsa, to haka ma mai tsananin sha’awa yana da cikakken ikon da zai danne sha’awarsa, ya kasance sai lokacin da ya bukace ta ne kadai za ta yi tasiri a cikin rayuwarsa da harkokinsa na yau da kullum. Ka da mutum ya ce ai ni haka Allah Ya yi ni, don haka ya doge da savon Allah yana cutar kansa, Allah SWT bai halitta varna a cikin ko da daya ne daga cikin halittunSa ba, sai dai shi abin halittan ya jawo wa kansa varna da abin da Allah Ya halitta masa. Mu lura mu gani zuwa ga shukokin da Allah Ya azurta mu da su, kowace shuka Allah Ya aje ta a mafi dacewar waje da yanayinta, kuma Ya hore mata abubuwan da za ta girma ta yadu a wannan wajen. Don haka ko me Allah Ya ba mutum, shi ne daidai abin da zai yi amfani da shi ya girma, ya yadu, ya kuma yi nasara a duniyarsa da lahirarsa. Haka kuma tsananin sha’awar da Allah Ya ba wani na iya zama wata jarabawa ce da Allah Ya yi nufin Ya jarabci bawanSa da ita, in mutum ya yi hakuri ya jure, Allah Zai saka masa da mafi kyawun sakayya.

Ø Kasancewa cikin matsananciyar sha’awa na nufin yawan sinadarin sha’awar da ke cikin jini ya wuce yadda ya kamata. Abubuwa da dama, masu nasaba da juna ne ke haddasa matsananciyar sha’awa ga dan’adam:

1. Akwai wadda ke faruwa a dalilin yanayin halayya da yanayin tunane-tunanen da ke zirga-zirga cikin zuciya da ma’aikatar hankalin mutum, da yanayin dawwamammen tunanin da ke cikin ma’aikatar hankalin dan’adam. dabi’antu da yawan kallon matan da ba muharramai ba, da yawan tunane-tunane na alfasha, da kallon fina-finan batsa, duk ayyuka ne da ke rura wutar sha’awa cikin zuciya da jiki.

2. Haka kuma matsananciyar sha’awa na faruwa a dalilin faruwar rikirkicewa cikin jerin gwanon sinadaran da kwakwalwa ke yawo cikin jini musamman masu nasaba da sha’awa. Duk lokacin da adadin wani sinadari ya daga ko ya kasa adadin daidansa cikin jini, wannan zai haifar da faruwar al’amuran cikin jikin dan’adam sama ko kasa da daidai faruwarsu. Abubuwa da dama na haifar da rikirkicewar sinadarai cikin jini, kadan daga ciki sun hada da mugunyar gajiya (stress) da kuma kasancewa cikin tsananin huzni na iya rikitar da kwakwalwa har ta saki adadin sinadarin da ya wuce daidai cikin jini.

3. Tabbatuwa kodayaushe cikin kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa; na iya sa sinadaran sha’awa su yawaita cikin jini.

4. Wani ciwo ko wata cuta da ke damun daya daga cikin manyan namomin jikin dan’adam masu gudanar da al’amura, na iya haifar da karuwar sinadarin sha’awa cikin jini;

5. Haka nan wasu magungunan warkar da wata cutar na iya yin tasiri ga karuwar sha’awa cikin jiki.

6. Cin kayan dadi masu kara lafiya; yawan motsa jiki da yin ayyukan karfi na kara yawan sinadarin sha’awa (Testosterone) da ke cikin jini.

Hanya ta 7 da matashi zai bi don dakushe kaifin matsananciyar sha’awa: Yana da matukar alfanu ga matashi mai fama da matsananciyar sha’awa ya kasance koda yaushe akwai wani al’amari da ya sa a gabanshi ya ke aiwatarwa, ya tarkato aikin da bai son yi ko wanda yake ganin ya fi karfinsa ya yi ta yi, in kwakwalwarsa ta kasance koda yaushe akwai abinda ke gabanta, a hankali za ta kone kuzarin shaukinta har ya kasance babu kuzarin jin motsuwar sha’awa kuma. Matashi ya kiyayi zama haka nan ba ya yin komai, domin a irin wannan lokacin ne shedan kan lallabo ya tsirar da tunanin sha’awa cikin zuciya, in ko matashi na aiwatar da wani aiki kusan koda yaushe, to ko shedan ya tsirar masa da tunanin sha’awa, to wannan tunanin ba zai yi tasiri ba. Ko kallo ne matashi zai yi, to ya fi masa alheri ya kalli abubuwan karuwar ilimi, ba fina-finan labaran soyayya ba, ko na kide-kide da wake-wake, domin wadannan duk wasu abubuwan ne ma su hassasa ruruwar wutar sha’awa cikin jiki.

Hanya ta 8: Yawan karfi da tsanantuwar sha’awa na iya zama alheri mara iyaka ga mai fama da su in dai ya gano dabarar da zai sarrafa su su haifar da alheri ga rayuwarsa maimakon su yi ta motsowa kodayaushe ba bisa ka’ida ba. Kamar yadda na taba fada a wannan fili, sha’awa ba komai ce illa daya daga cikin shau’ukan dan’adam, kuma duk wani shauki na dan’adam na bukatar kuzari lokacin motsawarsa cikin jiki da zuciya. Sha’awa ta kasance ta fi kowane kuzari karfi a dalilin tana amfani da duka kalar kuzari ukun nan na jikin dan’adam, watau kuzarin aikin karfi, kuzarin ma’aikatar hankali, da kuzarin shau’uka a duk lokacin motsuwarta. 

Binciken masana kimiyya ya tabbatar dukkannin manyan mutane da suka shahara suka yi suna a duniya ta wani fanni, irin su manyan masana kimiyya, kirkira, masana hikimomi, manyan masu mulki, Allah SWT Ya wadatu su da yawan karfin sha’awa da yawan tsanantuwarta, amma sai basu biye ma son zuciyarsu sun konar da wannan dimbin kuzarin a banza ba wajen dulmiya cikin tunane-tunanen alfasha da neman mata, sai dai suka runka karkatar da wannan dimbin kuzarin sha’awarsu wajen aiwatar da muhimman abubuwa wadanda suka kawo ci gaba a rayuwar dan’adam a dalilin haka su kuma suka yi suna duniya ta sansu, ya kasance ana ambaton su har bayan ransu.

 Don haka matashi ko magidanci mai tsananin sha’awa ya kamata ya tashi ya mike kuma ya dage, ya juyar da wannan dimbin zinariyar sha’awar da Allah SWT ya azurta shi da ita zuwa ga wani abin da zai zama abin alfaharin gareshi da duk wani nashi. Mu yi dubi zuwa ga manyan mutanen da suka yi suna da karfin su ba da karfin wasu ba, ko karfin zalunci, inda sun biye ma sha’awar su da son zuciyarsu, lallai da basu kai ga wannan matsayi ba. Ba kuzarin da ya kai kuzarin sha’awa karfi, don haka in ya yi yawa ko in ba a bukatar shi wajen ibadar aure, ana iya juyar da shi a cimma wani tsayayyen buri na rayuwa, maimakon a yi barnarsa wajen bin mata ko a yi asararsa haka nan a banza. Da fatan Allah Ya bada ikon dagewa, amin.


Duk lokacin da sha’awa ta motso ma mai fama da matsananciyar sha’awa, to ya san yadda zai yi ya karkatar da tunanin shi daga wannan sha’awar zuwa wani abin daban. Misali, duk lokacin da igiyar tunanin sha’awa ta bijirowa matashi, sai ya yi sauri ya tsinke ta, ta hanyar saka wani tunanin daban cikin zuciyarsa wanda bai da nasaba da sha’awa, misali, sai mutum ya yi ma kansa wani abun da zai sa dole ma’aikatar hankalin sa ta sakki wancan tunanin ta koma ga abin da ke faruwa a jikin sa a wannan lokacin, misali, mutum na iya sanya robali (rubber band) a hannunsa, sai ya ja shi da karfi ta yadda zata tsalle shi ya ji zafi sosai, ko ya ciji hannunsa, ko dan yatsan sa cizo mai zafi a duk lokacin da irin tunanin nan ya bijiro masa, dole kwakwalwa nan take ta yanke ta bar wancan tunani ta koma ga na jin zafi, domin kwakwalwar dai guda daya ce, zai yi wuya ta saurari abubuwa biyu masu karfi a lokaci daya!
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.

Post a Comment

0 Comments