Amfanin Jirjir (watercress).
■ Jirjir yana taimakawa wajen kula da lafiyar kashi domin yana dauke da sinadarin calcium.
■ Jirjir yana taimakawa wajen bada kariya daga goiter saboda yana dauke da matsakaicin adadin Iodine.
■ Wani binciken masana kimiyya ya tabbatar da cewa man jirjir da man zaitun na taimakawa wajen kawar da kitse a cikin jini yana kuma zama sanadin raguwar duka cholesterol din jiki.
■ Jirjir yana taimakawa wajen magance cututtukan hanji da rashin narkewar abinci da kuma tsabtace jiki daga duk wata guba.
■ Jirjir yana taimakawa wajen ƙarfafa ƙwaƙwalwa da haɓaka ƙarfin basira don samun fahimta da saurin haddace bayanai.
■ Jirjir yana ƙunshe da wasu muhimman vitamin kamar Thiamine, niacin, vitamin B16 da sauran vitamins waɗanda suke kula da lafiyar jiki gaba daya.
■ Yana taimakawa wajen rage kiba.
■ Yana ƙunshe da sinadarai masu mahimmanci ga lafiyar mata masu juna biyu.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
ALLAH YA KARBI IBADUN MU.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments