AMFANIN KANTU WAJEN ƘARA LAFIYA.
Kantu, ana kuma kiransa da Riɗi sannan wasu suna ce masa Simsim.
Kantu na da sinadarai masu muhimmanci wajen kyautata lafiyar mutum da ƙayatar da jikin mutum yai kyau da kuma hana bayyanar tsufa ajikin fata.
Ga wasu daga cikin Amfanin Kantu.
1. Taimakawa narkar da abinci da kuma rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya.
Sinadarin 'fiber' mai yawa da ake samu acikin Kantu ya sa yake taimakawa jiki wajen sauƙin narka da abinci, rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya, hana cutar kansa da kuma 'diabetes type 2'.
2. Cire kitse mara amfani daga jikin mutum.
Da akwai kitse mara amfani wanda idan yai yawa ya ke yiwa zuciya barazana da haifar da wasu cututtuka. 'Lignans' da kuma 'phytosterols' da ke cikin Kantu na taimakawa wajen cire kitse mara amfani daga cikin jiki.
3. Gina jiki.
Kantu na samar da sinadarin 'protein' wanda ke gina jiki.
4. Samar da manyan sinadaran ƙarawa mutum lafiya kamar 'calcium' , 'vitamin E' , 'B vitamins' 'copper', 'zinc', da 'magnesium' waɗanda ke yaƙin wasu cututtuka da kuma ƙarawa jiki lafiya.
5. Sa girman gashi.
Kantu na da matuƙar amfani wajen sa fitowar gashi a jikin mutum idan ana cinsa ko shafa mansa a fata.
6. Kariya daga cutar Kansa (cancer).
Kantu na taimakawa sosai wajen yaƙi da kamuwa da nau'ukan kansa da dama.
7. Taimakawa masu fama da Ciwon suga (diabetes).
Kantu na taimakawa wajen daidaita sikarin da ke cikin jini.
8. Lafiyar ƙasusuwa.
Samun 'calcium' da 'magnesium' a cikin Kantu ya sa ya ke da gudunmawa wajen ƙarawa ƙasusuwan jiki lafiya.
9. Hana lalacewar abinci.
Kantu na ɗauke da sinadaran da ke hana abinci da kayan amfani saurin lalacewa.
10. Narkar da abinci.
'Fiber' da ke cikin Kantu na taimakawa jikin mutum wajen narkar da abinci cikin sauƙi.
11. Lafiyar haƙora.
Kantu na taimakawa wajen ƙarawa haƙora lafiya.
12. Girman nono ga mata.
Haɗawa da Kantu cikin magungunan ƙara girman mama na taimakawa sosai wajen sa shi girma da kyawun fatar jiki.
Amma a kula, cin Kantu mai yawa lokaci guda na iya sa wa ai gudawa.
Idan kana yawan cin Kantu to ya kamata ka dinga wanka akai-akai don ta haka ne zai gyara ma ka fata kullum ka dinga zama sabo amma in ba ka wanka akai-akai to akwai matsala.
In kuna bukatar ku san amfanin wani abinci ko magani sai ku magana a comment, za mu kawo muku insha Allahu.
Daga shafin Bashir Halilu.
0 Comments