Kankana ta fi amfani ne a lokacin da ta nuna sosai don masana sun ce sinadaran nunannar ya fi taruwa sosai musamman beta-carotene dake cunkushe a cikin jan tozon nan wanda ke matukar taimakawa idanu.
Zakin cikinta kuma na ba mutum karfi, tana kuma karawa jiki ruwa.
- Gyaram fatar jiki.
Nunanniyar kankana na taimakawa fata saboda
sinadarin lycopene dinta.
- Ƙarfin maza
Sinadarin arginine dake cikinta na kara yawan
nitric oxide dake karawa namiji karfin gaba.
- Ciwon zuciya da hawan jini.
Nitric oxide da wasu sinadaren kankana na
taimakon masu ciwon zuciya da hawan jini.
- Samun bacci.
Tana haifar da samuwar wadataccen barci.
- Karin jini
Sinadarin vitamin C dinta na taimako wajen
maganin cututtuka da dama.
-Cutar kansa da ciwon Ƙoda
Kankana tana maganin ciwon daji kala-kala, da kuma ciwon koda.
- Kara Karfin jiki
Tana da sinadarai masu kara karfin kashi
(bone) da kuma maganin kumburin jiki musamman gabban jiki (joints).
Daga shafin Bashir Halilu
0 Comments