Zuwaga masu Aure da masu niyyar aure maza da mata.......................................
( kumin afuwa da wasu abunda zan faɗa a ƙasa)
Yana da matuqar kyau da amfani kuna maganin infection kafun kuyi aure ko bayan aure musamman in akwai alamomin su a tattare da ku, domin infection na daga cikin abubuwan dake hana jin dadin aure da haifar da wasu matsaloli musamman ta babin saduwa da ba'a ciki lura ko sani ba balle ayi maganin sa sai bayan aure ayi ta fuskantar matsaloli da dama da zai iya haifar da matsaloli da ya shafi mu'amala da lafiya jiki da zuciya.
A lokacin da zakuje gwaje-gwajen lafiya da ake kafun aure, ya na da kyau kuna sawa a hada muku da wannan test din dan baku damar yin maganin sa kafun ayi auren.
Daga cikin alamomin infection na mata da zaki gane kina da shi shi ne :-
💥 Fitan ruwa mai qauri kuma mai kama da tunbuɗi
💥 Jin raɗaɗi da zafi kamar barkono da ƙaiƙayi a ciki da wajen gaban mace.
💥 Wari ko tsananin qarni a gaban ki
💥 Jin zafi kamar barkono lokacin da miji ke shiga, ko ya yin saduwa ( zafi yana da banbanci da zafin da macen da ta somayi da wacce sabayi ko ta kwana 2 batayi ba, zafi ta dalilin yanayin halittan namiji, ko yanayin yadda namiji ke saduwa da mace, ko dan wani position, zafin sa nada bambanci dana mai infection.
Zafin na mai infection wannan kasancewar infection din yasa mace na yawan qaiqaya wajen, hakan yasa wajen ya ji 'yan raunuka kamar kuraje ko kwarzanewa a bakin shiga da cikin gaban hakan yasa da namiji yasoma qoqarin sa gaban sa zataji wannan zafin sosai tamkar barkono aka zuba mata a wajen, ko in aka sa lubricant taji zauuu a wajen na zafi kamar a ciwo aka samata)
💥 Daukewa ko gushewar ruwan ni'ima
💥 Gushewa ko daukewar sha'awa duka
💥 Bushewan gaba kafun da lokacin saduwa ( ko ana ganin wannan ruwa mai dauke da tunbuɗi )
💥 Fitan ruwa mai wari kore ko yellow.
💥 Qananan ƙuraje masu kai kayi da zafi
💥 Yayyankewan lebban gaban mace.
💥 Jin zafi lokacin fitsari
💥 Yawan discharge mai kama da tunbuɗi, ko kore ko yellow ruwa ( discharge)
Yana da kyau da muhimmanci...............
🩷 kije asibiti a gwadaki dan asan irin nau'in infection da kike dashi sannan matakin da ya kai a jikin ki.
🩷 Amfani da ruwan dumi da gishiri wajen tsarki ( yana rage infection ko ya kashe shi in baiyi tsanani ba)
🩷 Kwana ba pant ko a sa wadda yake sake ba matsetse ba
🩷 Amfani da cotton pants da kiyaye amfani da silk ko polyester.
🩷Chanza pad a kai a kai lokacin al'ada
🩷 Kiyaye amfani da turare, sabulu, yin hayakin tsuguno da sa maganin mata a gaban ki.
🩷 Kiyaye amfani da kowani bandaki
🩷 Bama wajen daman shan iska da dare, amma a kiyaye barin iska ya shiga dan yakan kawo tusan gaban mace musamman na lokacin saduwa ( akwai wadda dalilin rashin kula da kai bayan haihuwa ake samu)
🩷 Kiyaye shan shuga da kayan zaƙi musamman in kina da infection ( yeast infection yana qaruwa in ya samu sugar a jikin mace ko kikayi inserting abun da ke dauke da zaki kamar zuma etc.)
🩷 Amfani da gishiri a bandakin da mutane da yawa ke amfani dashi.
🩷 kiyaye hada tsarkin gaba da baya lokacin tsarki
🩷 Goge wajen da towel, tsumma ko zani da kika ajiye musamman dan wannan, ko amfani da cotton pant dan yayi absorbing ruwan da kikayi tsarki.
🩷 Kiyaye amfani da bandakun kowa da kowa ( public toilet)
🩷 Kiyaye amfani da bandakin gidan biki.
🩷 In ba ya zama dole ba ko in fita zakiyi, yana da kyau ki na rage wuni da pant a jiki dan wajen ya samu daman shan iska
🩷 Kiyaye sa yatsa a gaban ki da ba a tsabtace shi ba, yana da kyau da muhimmanci kafun miji ya kusance ki ya kasance farcunsa a yanke suke, sannan kullum ya wanke hannun sa da kyau kafun yayi wasa ko sa yatsa a wajen.
🩷 Tsarki ko sit bath da ganye ko garin ruwan magarya da aka tafasa ya dan huce da amfani da man albabunaj da aka hada da man zaitun kina sawa a ciki dan magano ko rage infection da bai yi tsanani ba wato kamar kin soma jin alamamun sa da warkar da kuraje ko raunin da kika samu sanadin yawan ƙaiƙayi ko saduwa ( WANNAN RIGA KAFI NE BA MAGANI BA)
A TABBATA ANJE ASIBITI DAN SANIN MATAKIN DA YA KAI DA MAGANIN DA YA DACE DASHI.
✍️ Fatimah Chikaire
0 Comments