Yadda Za’a Magance Ƙyasbi Ko Kurajen Fuska Cikin Sauki:


Yadda Za’a Magance Ƙyasbi Ko Kurajen Fuska Cikin Sauki:


Mene ne ciwon kyasbi? Ya kuma ake magance ciwon ta hanyar amfani da magungunan gargajiya a gida?

Ciwon kyasbi, ciwo ne da ya shafi fatar jikin mutum. Sannan kyasbi ba kasafai mutane ke warkewa ba idan sun kamu shi.

A yau zamu bayyanawa masu karatu wasu hanyoyi ko magungunan gargajiya hudu da zasu taimakawa masu dauke da wannan cutar ta kyasbi ko kurajen fuska.

Domin magance matsalolin da suka shafi fata, wadanda suka hada Kyasbi, Maƙyaro da Pimples, wadanda anyi-anyi abin yaci tura, to kun zo wurin da ya dace matukar da gaske kuke wajen son kawar da ciwon na kyasbi da sauran su.

Zamu lissafa abubuwan da ake bukata domin maganin kyasbi a ƙasa;

1. Man Zaitun; (Olive Oil).

2. Man Kwakwa, (Coconut Oil).

3. Aloe Vera.

4. Ma’u Khal, (Khal Water).

Yadda za’a hada wadannan abubuwa;


: Man Zaitun da Man Kwakwa
Bayan kun kammala duk wadancan abubuwan da muka ambata a sama, sai a dauki wannan Aloe Vera a saka ta cikin wani abin daka mai tsabta sai a dan daka ta, ko kuma a saɓa.

Lokacin da ake dakawa ko saɓa Aloe Vera din sai a rika zuba Ruwan Khal kadan-kadan, amma kada a saka ruwan sosai ta yanda zata kwabe tayi ruwa.

Idan aka gama wancan matakin na farko, sai juye ta cikin wani wuri mai tsafta, sai a zuba man zaitun da man kwakwa a ciki a juya sosai.

Ana bukatar a bayan an juya su, sai a kai hadin ga rana mai dan zafi na kamar tsawon awa daya, domin yayi dan ɗumi.

Daga karshe za’a samu mataci wanda za’a tace mayukan domin a cire itatuwan Aloe Vera, sannan sai a rika safa wannan hadin safe da dare idan za’a shiga barci.

Inshaa Allah, idan mutum ya hada wadannan abubuwa dai-dai kamar yanda aka zayyana su anan zai yiwa Allah godiya, kuma ya yiwa Arewa Times Hausa addu’a

Ku turawa yan uwa da abokan arziki wannan post…..

Post a Comment

0 Comments