MUHIMMANCI UWA (MOTHER) ARAYUWA


"Rayuwar Matasa a Yau

1. # Mahaifiyace zata dauke cikinka/ki har na
tsawon watanni tara (9) ciwo kan ciwo ba tare
da tace a zubar ba.

2. #Mahaifiya ce zata kasance babu ci, babu
sha, ga karancin bacci bisa nauyin dauke da
kai/ke.

3. #Mahaifiya ce bayan ta haife ka/ki zata
dauki dukkan lokutanta akan ka/ki domin kula
da kai/ke.

4. #Mahaifiya ce ba zata iya cin # Abinciba
sai taga kai/ke kaci, haka zalika ba zata iya
# Bacciba sai taga kayi/kinyi.

5. #Mahaifiya ce duk tsananin rashin lafiyar
dake damunta tana dauke da kai/ke, kuma
tana rarrashin ka/ki a duk lokacin da ka/kike
kuka komai tsawon lokaci.

6. #Mahaifiya ce ta koyar da kai/ ke yadda
ake tafiya, ake cin abinci, ake magana da
kuma zamantakewa.

7. #Mahaifiya ce duk tsanin rashin lafiyan da
yake damunka/ki tana tare da kai/ke ba tare
da gajiya da kai/ke ba, kuma duk kazantar
cuta bata guje ka/ki ba.

8. #Mahaifiya ce ke girka maka/miki duk
kalar abincin da ka/kike so.

9. # Maiahifiyace take siya maka duk abinda
ke/kike so, a lokacin kuruciyar ka/ki kai
harma da wayonka/ki.

10. #Mahaifiya tana sonka/ki fiye da
matarka/mijinki, kuma # Sona hakika wanda
arziki ko talauci bai isa ya taka rawa tsakanin
ku ba.

YA-ALLAH KA JIKAN MAHAIFAN MU, KA SA
ALJANNAR FIDDAUSI CE MAKOMAR SU.
WANDA SUKE RAYE KUMA ALLAH KASA
SUKACI DA IMANI DAMA MU BAKI DAYA."


Share This 

Post a Comment

0 Comments