Yadda Za’a Yi Maganin Ciwon Kai Mai Tsanani A Gida:
Mene ne ke kawo ciwon kai? Kuma ta yaya za’a magance matsanancin ciwon da magungunan gargajiya?
Ciwon kai koyaushe ana rarraba shi azaman na wanda aka saba gani ko wanda ba kasafai yake faruwa. Babban ciwon kai shine ciwon kai wanda ba wani yanayi ko rashin lafiya da ya haifar dashi ba.
Akwai nau’ikan ciwon kai da yawa, amma akwai nau’ikan guda huɗu: sinus, tension, migraine, da cluster.
Abubuwan da ake bukata domin hafa wadannan magungunan da kuma yadda za’a shirya maganin;
(1). Danyan citta cokali daya. Idan kuma busassace karamin cokali.
(2). Iklilil jabal, wato Wanda a harshen turance ake Kira da (Rosemary).
(3). Lavender, wanda a Kira da harshen larabci cewa (Kazama).
(4). Yansun.
Yadda zaka hada shine:- Zaka zuba karamin cokali na sauran maganin amma banda danyar citta, zaka zuba cokali daya ne ita, amma kada amanta, abaya munce idan busassace karamin cokali, ko rabin cokali ya isa.
Zaka tafasa ruwa sai kazuba ruwan dumi akai, amma wanda aka dafa sosai, bayan anzuba sai karufe kabar shi, bayan mintina kadan sai katace karika shan kadan lokaci bayan lokaci. Inshaa Allah akarshe zakaga sakamakon mai kyau.
Baya wadancan abubuwan da muka zayyana a sama, za’a iya samun ingantaccen man tafarnuwa, wanda aka tabbatar da sahihancin shi.
Shi wannan man tafarnuwar za’a rika shafa shi a goshi idan za’a shiga barci.
0 Comments