ABINCIN MASU CIWON SUGAR [DIABETICS DIETS]
______________________________________
Ina fatan masu wannan larura harma wandanda basu da ita ko wanda take jiransu agaba yan Borderline zasu kara kiyayewa don kauracewa hatsarin da za'a iya tsintar kai ciki a dalilin saka ci da larurar.
Masu wayau ciki in nine zan sami littafi ne na kwafe wadannan abincin daga baya sai in zauna na tsarawa kaina Timetable na abinci domin samun sauki tunawa.
Don Allah wanda yake da mata wacce ke fama da wannan larurar ya taimaka ya bata hadin kai. Inyaji abunda take bukata ya karfafeta ya taimaka ya sayamata. Karkace saide inta mutu in bazataci abunda kasa ta ta girka maka ba. Kasani kaima Allah na iya jarabtarka.... karka zama mugu
Inhar aka kiyaye cimakar nan insha Allah duk wani complications ana iya kauce masa kuma mutum zai rayu kamar kowa.
Sannan Babban abinda nake son kusa aranku shine me ciwon suga baa so yake cin koma menene yana koshi dam.... koda cikin abinci irin nasa. Domin yin hakan zai wahal dashi kuma zata kaisa ga zuwa cin abunda ba'a yarje ba.
GA JERIN ABINCIN DA ZA'A HAƘURA KO A KIYAYE CINSU A RAYUWA GA MASU CIWON
1. Banda cin Farar Shinkafa
2. Banda cin taliya walau yar hausa ko spaghetti,
3. Banda cin Macaroni
4. Banda shan Yoghurts/Ice creams
5. Banda duk wata alewa ko nau'in kayan zaqi
6. Banda cin Abu mai kitse ko maiko (harda chocolates)
7. Banda cin Couscous (kus-kus)
8. Banda cin Bredi da duk wani abincin da akai da fulawa
9. Banda shan Coffee
10. Banda cin Soyayyen nama
11. Banda cin Jan nama (sa')
12. Banda shan Lemuka su fanta, coke, pepsi, mirinda, 7up, maltina, lacasera da sauransu
13. Banda shan Tea me sugar (akwai lipton na masu suga daban)
14. Banda cin dabino tare da shan zuma
15. Banda shan miyar Egusi
16. Banda shan Rake
17. Banda cin dankalin hausa.
18. Banda cin Ayaba.
19. Banda cin doya ko sakwara
20. Banda cin hanji ko tumbi cikin kayan cikin sa'.
21. Banda cin garin kwaki,
22. Banda cin Teba
23. Banda cin su Egg roll, da meat pie
24. Banda shan duk wani fruits ko juice na roba
24. Banda cin shawarwa
25. Banda rolgo
26. Banda shan maganin gargajiya kowanne iri.
27. Banda shan sprite
28. Banda shan abarba.
29. Banda Shan melon
30. Banda cin su doughnut,
31. Banda cin Cincin
32. Banda Fanke
33. Banda cin wainar flour (kalalla6a)
34. Banda cin tuwon masara (sosai da sosai) ake take ciki kuma kullum....banda yin hakan. Saide kadan shima sai in sugar ansan anyi control dinta sosai
35. Banda shan kankana akai akai kuma kadan zaa sha in bukata ta taso kuma sai in anyi control din sugar akalla kasa ko daidai 7mmol
36. Banda cin dambun shinkafa
37. Banda cin funkasau din fulawa
38. Banda cin Tsire (Naman sa)
39. Banda cin Balangu (Naman sa) saboda kidney
40. Banda dambun nama
41. Banda wainar shinkafa
42. Banda Alkubus din fulawa
43. Banda Sinasir
44. Banda Semovita (saide kadan bakuma kullum ba) shima kuma sai anyi control din sugar da kyau
45. Banda cin madarar i'loka
46. Banda cin indomie❌
47. Banda toyayyen kwai
48. Banda Shan lemun abarba
49. Banda cin Spring rolls
50. Banda cin Bread rolls.
51. Banda cin Pancake
🌱Fatan an fahimta!
❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌
ABUNDA MAI CIWON SUGAR ZAI IYA CI
Karfin abincin yanzu zaifi a ganyayyaki da fruits, sanan akwai wanda ba fruits bane toh amma fa daidai misali za'a ci ba bude ciki za'AI ba har sai anji ankoshi.
Shyasa zakuga na nuna ba kullum ba. Infact in sugar dinka ta haura (8mmol) toh karka ci koda kaji nace aci daidai misali.
1. Ku dage da motsa jiki, saboda karkui nauyin Koda (kidney) za ta samu karin wahala.
2. Kui hakuri da duk abun zaqi kamar yadda nace abaya.
Saboda zaku iya tambayata to ai shinkafa da taliya dasu indomie dana hana ba kayan zaqi bane?
Amsa Eh abaki ba kayan zaki bane amma dukkansu Carbohydrates ne kuzari suke samarwa ajika.... zarar akaci jiki na gama niqasu ruwan suga suke komawa wato GLUCOSE ku kuma larurarku babu sinadarin dazai saisaita sugar wato INSULIN shyasa dole ku hakura. Inba haka ba sugar zatai sama sannan ragowar zata juye zuwa kitse ta kwanta kasan fatarku koya aka sami rauni toh daga irin haka sanadiyyar kaiwa ga yanke kafa ke farawa. Abincinku yanzu zaifi ga Fiber wato (dusa-dusa) irinsu Alkama....
3. Don haka zaku iya cin Bredin Alkama...... domin a biredi akwai na alkama musamman don masu sugar dama akeyi babu zaqi aciki kuma yana da dadi. Marasa ciwon suga ma wasu sunfi sonshi
4. Zaku iya shan lemon 6awo saboda vitamin c ne shi kuma zai wanke kodar sannan duk inda rauni yake zai saurin hadewa
5. Zaku iya shan tumatir duk sanda kuka samu koda kwaya 1 zuwa 2 ko3 ne saboda shima vitamin c ne. Ko kui jajjagen miyarsa
6. Ku rika shan ruwa sosai da sosai. Koda bakwajin kishi yadda fitsarinku zai karu.... kodarku ta kara washewa taji dadin tace jini.
7. Ku rikacin kabeji..... kwarai da gaske hasali ma kodarku shi take so saboda yana wanke dattine dama (antioxidants).
8. Rika amfani da Olive oil ana digashi a abinci inda hali yana da mahimmanci sosai.
9. Zaku iya cin Kifi kowanne iri
10. Zaku iya shan Oat meal. Ku sayo ku aje ku rika damawa koda cokali 4 inkukasha zai saisaita maiko ajikinku kuma kodarki shi takeso, sannan bazaki ke yawan jin yunwa ba.
11. Dafaffen kwai babu damuwa amma karya wuce 2 ayini.
12. Amfani da Tafarnuwa a abinci ko a rika hadiya akai akai zai taimakawa jikin yasa pancreas ta saki insulin din da ya samu.
13. Dafaffen naman kaji. Amma banda fatar bayan...saboda fatar bayan kunshe take da cholesterol
14. Dafaffiyar Gyada, ko wacce ba'a sa gishiri ba.
15. A rage shan gishiri ko magi saboda hawan jini.
16. Za'a iya cin Salads
17. Broccoli
18. Za'a iya dafa Brown Rice aci saboda tafi Fiber akan kowacce irin shinkafa
19. Albasa
20. Taliya Pasta wacce take ta alkama zallah
21. Miyar kubewa
22. Za'a iya shan Cashew
23. Apple cider vinegar
24. Abincin Gero (walau tuwo ko kunu) amma anso kar a surfa shi
25. Abincin dawa (Tuwo) (Amma daidai misali) saboda dawa ba Carbohydrates bace zallah akwai fiber. Amma ba kullum ba.
26. Zaku iya shan Miyar kuka
27. Zaku iya cin kwakwa (ko shan ruwan kwakwar)
28. Low diary fat milk. ( misali; Three crown, ko nonon shanu)
29. Zaku iya yin Miyar wake (Ama wanda Uric acid level dinsa yai high to sai yai hakuri har ya sauko)
30. Zaku iya cin Awara wacce babu gishiri sosai.
31. Zaku iya shan Yaji (pepper) (banda gishiri sosai)
32. Kunun tsamiya... banda suga. Musamman na gero ko dawa.
33. Bitter leaf soup
34. Miyar alayyahu.
35. Amala ta garin danyar plantain bata garin doya ko alabo ba
36. Alala (moimoi)
37. Zaku iya cin hanta.
38. Zaku iya cin Ganda (cow skin)
39. Walahan (cocoyam)
40. Dankalin turawa
41. Guava
42. Oha soup
43. Miyar gyada.
44. Apple za'a iya ci
45. Koko wanda ba sugar...
46. Naman akuya
47. Wajen girki ai amfani da zallar original mangyada, Canola Oil ko Pomace Olive oil.
48. Banda maganin gargajiya
49. Aya (kananun)
50. Yalo
51. Kunun alkama
52. Fankasau din alkama
53. Zobo banda sugar
54. Zaku iya sayo sugar masu diabetes (Natural Stevia ) kuke amfani da ita.
55. Shrimps
56. Okporoko stock fish
57. Tomatoes stew
58. Afang soup
59. Gugguru mara suga (popcorn)
Karku manta da nace ba'a sakin ciki aci akoshi. Raba ciki uku za'ai : kaso daya ruwa, kaso daya hakuri, kaso daya Abinci.
Don haka ko bakunci mutum yaje kar yaji nauyin cewa baya cin duk abunda ya sa6a dana mai ciwon suga.
0 Comments