AMFANIN KUKA A JIKIN DAN ADAM


AMFANIN KUKA A JIKIN DAN ADAM 

GARIN KUKA YA KUNSHI ABUBUWA MASU GINA JIKI KAMAR.

1, Calories: 50
2, Protein: 1 gram
3, Carbohydrates: 16 grams
5, Fiber: 9 grams
6, Vitamin C: Kashi 58%
9, Iron: 9% na RDI
10, Potassium: 9% na RDI
11, Magnesium: 8% na RDI
12, Calcium: 7% na RDI

Kuka bishiya ce mai asali da ake samu a nahiyar Afirka da kuma wani yanki na kasashen Larabawa.

A al'adance bishiyar kuka tana da matsayi da muhimmanci ga abinci da magungunan mutanen Afirka.

Kuka tana kunshe da muhimman sinadarai masu gina jiki kuma masu inganta lafiya, kamar yadda mujallar lafiya ta Healthline ta bayyana a wani bincikenta game da amfanin kuka ga lafiyar dan Adam.

Tun daga daga ganyen kuka da ɓawon da ƴaƴan kuka dukkaninsu suna da sinadarai masu amfani sosai a jikin mutum.

Mujallar ta ce kuka tana ƙunshe da kusan dukkanin sinadaran da jikin mutum yake buƙata - Kuka na da sinadarin Calcium da ke taimakawa wajen ƙwarin kashi da hakori da sinadarin magnesium wanda yake daidaita jini.

Kuka tana da sinadarin iron wanda yake kare jiki daga kamuwa da cutar rashin jini, haka kuma kuka tana da sinadarin potasium da ke saita jini.

Sannan uwa uba sinadarin Vitamin C ya fi yawa a kuka wanda ke yaƙi da cututtuka.

Sauran sinadaran da ke cikin kuka sun haɗa da sinadarin cabohydate da protien da vitamin D da kuma sinadarin fibre da ke sa abinci saurin narke wa a jiki.

Babban sinadarin da ke cikin kuka.

Bincike ya nuna kuka tana samar da kusan rabin sinadarin Vitamin C da jikin mutum da ya haura shekara 18 ke buƙata.

Wani binciken masana ya gano cewa kuka ta fi lemun zaƙi sinadarin vitamin C da Ninki 10, haka ma lemun tsami.

Mujallar lafiya ta Healthline ta ce kuka tana dauke da kashi 58 na Vitamin C da mutum yake buƙata a rana.

zaren kuka ya fi yawan sinadarin Vitamin C, ana amfani da shi ga masu kansa.

Amfanin Vitamin C ga jikin ɗan Adam ya haɗa da:

Vitamin C sinadari ne da ke kare ƙwayoyin halitta da kiyaye su cikin ƙoshin lafiya.

Yana ƙara lafiyar fata da hanyoyin jini da lafiyar ƙashi da kuma ɓargo

Vitamin C na taimakawa wajen saurin warkewar ciwo.

Masana sun ce ga ƙa'ida ƴan shekara tsakanin 19 zuwa 64 suna buƙatar 40mg na vitamin C a rana.

Kuma an fi samun sinadarin vitamin C a abincin da mutane suke ci kuma ana buƙatar sinadarin a kullum.

Miyar kuka ta fi alayyahu da kuɓewa amfani a jiki

Miyar Kuka - ta fi dukkanin sauran gayyakin da Hausawa ke miya da su amfani ga jiki saboda yawan sinadaran da ta ke dauke da ita cewar masana.


kuka ta fi alayyahu da kuɓewa cikin ire-iren gayayyaki da ƴaƴan ita ce da Hausawa ke yin miya da su a abinci.

Yadda mutanen ƙauye ke yawan shan kuka yana ƙara masu lafiya, "shi ya sa yawancin cutukan da ake yi a gari da wuya a same su ƙauye."

kuka tana warkar da cututtuka da dama, kuma mutane ba su san amfanin kuka ba ne ya sa suke gujewa amfani da garinta ko ganyenta musamman a abinci.

Maganin da kuka ta ke yi

1, Kuka tana maganin zazzabin maleriya
2, kuka tana maganin tarin fuka TB
3, Tana kara ingana garkuwar jiki
4, Kuka tana ƙara jini a jiki
5, Kuka tana maganin gudawa
6, Kuka tana maganin hakori
7, Kuka tana maganin ulsa
8, Kuka tana rage ƙiba

Baya ga waɗannan, idan ana shan kuka ba zai sa mutum ya samu kumburin ciki ba saboda rashin narkewar abinci sakamakon sinadarin fibre da ke cikinta.

Haka kuma ga wadanda ke son rage tumbi ana iya shan ganyen kuka domin yana narkar da kitse.

kuka tana maganin ciwon ulsa - "ga mai ulsa zai kaɗa ganyen kuka a ruwa a sha, cikin lokaci kaɗan zai samu saukin ulsa." In sha Allah 

Kuka tana ƙara ni'ima ga mata da Kuzari ga maza

Masana sun ce saboda tasirin kuka wajen inganta ruwan jikin mutum, tana kuma tasiri wajen ƙara ni'ima ga mata.

Yadda ya kamata mata su yi amfani da kuma za a samu sassaƙin kuka a wanke sosai sai dinga sha 


kuka tana kara wa maza karfin jiki da kuzari. Haka kuma mazan da ke son jikinsu ya buɗe kuka tana taimakawa saboda sinadaran da ke cikinta.

Yadda ya kamata a yi amfani da kuka

Kamar yadda muka yi bayani tun a farko cewa kuka tana da matsayi musamman a abincin Hausawa.

Hausawa suna yin miya da ganyen kuka. Ana busar da ganyen kuka a niƙe a tankaɗe a yi miya domin cin tuwon dawa ko masara ko shinkafa ko alkama. Haka kuma Hausawa sukan yi amfani da kuka wajen yin Ɗanwake

Amma masana sun ce ɗanyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kuka da ake miya da shi.

Yadda ake busar da kuka yana kashe wasu sinadaran da ke ƙunshe a cikinta - saboda rana da aka shanya kukar tana kone sinadarai da dama.

ɗanyen ganyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kuka ƙarin lafiya da sinadarai a cikin miya.

Sannan ba a son idan za a yi miyan kuka a bari ta sha wuta sosai domin yawan dafuwa zai rage yawan sinadaran da ke cikin kuka, 

Shin ko kuka na da wata illa?

Masana na ganin duk da ba a zurfafa bincike ba kan kuka, kamar yadda ake buƙatar binciken sosai game da bishiyar mai matukar muhimmanci ga lafiya, amma zuwa yanzu babu wata babbar illa a kuka.

Sai dai duk lokacin da mutum ya fahimci wata matsala bayan amfani da ganye ko garin kuka an fi son a ziyarci likita musamman mata masu juna biyu da shayarwa.

Haka kuma kamar yadda aka yi bayani cewa kuka tana da sinadarin Vitamin C sosai, amfani da ita da yawa yana iya haifar da ciwon ciki ko gudawa idan har mutum ya yi amfani da adadin kuka da ya wuce kima.

Masana sun yi gargadi cewa kada mutane don sun ji an ce kuka tana da sinadarai sosai ga lafiyar jiki su dinga sha da yawa. Domin sha da yawa zai iya yin illa ga masu cutar ulsa.

Masana kuma sun ƙaryata iƙirarin da wasu ke yi musamman a tsakanin Hausawa cewa yawan shan miyar kuka yana toshe basira.

"Kuka sai dai ta ƙara basira saboda sinadaran da ta ke ƙunshe da su, kawai camfi ne

DON ALLAH KUYI SHARING ZUWA WASU GROUPS

ISLAMIC MEDICINE CENTER.

Post a Comment

0 Comments