Yanda Ake Rijista a Binance Daga Farko zuwa Karshe (Hausa)


Mutum ze iya kasancewa bako a Binance, amma Binance baze taba kasancewa bako a garesa ba saboda Binance ya riga yayi nisan gaske sosai da sosai a yaduwa ko ina da ko ina a fadin duniya. Binance a halin yanzu ya kasance mafi girma da inganci a cikin gidauniyar siya da siyarwa na Cryptocurrency a dunia baki daya tare da samar da masu aiki dashi abubuwa masu inganci da fa’ida a garesu.

A wannan rubutun, zan yi magana akan:

- Menene Binance?
- Me yasa zan fara amfani da Binance?

- Mataki-mataki kan yanda zaku fara aiki da Binance (Registration)

Menene Binance?

Binance sanannen gidauniya ne na siya da siyarwa na cryptocurrency a duniya a wajen girman kasuwa da kuma yawan ‘yan kasuwa (Binance shine mafi girma da inganci a halin yanzu)
Anyi rijistan Binance a Cayman Islands, North America. An kir-kira Binance ne a 2017; wanda ya kir-kira Binance kuma shine Changpeng Zhao, shahararren masanin na’urar gidauniyar kasuwancin yanar gizo wanda a baya ya kir-kira wata ingantacciyar gidauniyar kasuwancin yanar gizo da duniya ta yaba da ita sosai da sosai.

Haka zalika Binance ta kasance gidauniyar kasuwancin Crypto a yanar gizo da ta kunshi crypto kala-kala, daban-daban masu inganci da nagarta. Binance tana baiwa masu amfani da shi Wallet daban da zasu dinga aje dukiyar su cikin kakkauran tsaro domin kwanciyar hankalin su.

Binance na samarda masu amfani da shi hanyoyi daban-daban na samun kudi cikin sauqi da kuma amin ci. Misali daga cikin su shine trading da staking.

Binance nada nashi Blockchain token na kansu me suna Binance Coin (BNB).

Me Yasa Zan Amfani da Binance?

Dalilin da yasa ya kamata ku fara amfani da Binance nada yawan gasket, Wanda dalilan ne suka sa gidauniyar Binance ta kasance mafi girma da inganci a duniya., Cikin sauqi, ga kadan daga cikin su:

- Binance ta kasance gidauniyar siya da siyarwa na crypto ne mafi karancin charges, 0.10% fee a spot trading, 4.5% a siyayya da Debit card da kuma free charges a siya ko siyarda Bitcoin.

- Binance na samarda ‘yan kasuwanta na duniya baki daya da cryptocurrency kala-kala, daban-daban har sama da dari bakwai (700) da zasu iya kasuwancin su cikin sauqi da aminci.

- Binance ne gidauniyar cryptocurrency mafi tsaro, tsaro mafi inganci. Dukiyarku zata sama kulawa sosai da sosai fiye da yanda zata zauna a aljihun ku.

- Binance Keda hanyoyin siya da siyarwa na cryptocurrency da dama wanda mutum ze siya coins kuma ya siyar cikin sauqi da aminci Kaman Binance P2P trading, Binance Pay, Crypto Deposit da withdrawal ta crypto network da dai sauransu.

- Binance na bama masu amfani da shi dama su juya crypto daga wani crypto zuwa wani crypto kyauta. Misali, Kaman ka juya Bitcoin zuwa BUSD.

- Binance na bama masu amfani da shi dama su siya katin waya daga gidauniyar Binance zuwa layin salular su kai tsaye ba tare da bata lokachi ba.

Wannan ba kwata-kwata amfanin Binance kenan ba a takaice, sedai kadan daga cikin amfanin Binance. Iya zurfin amfaninka da Binance, iya sanin amfanin sa da kai.

Mataki-Mataki Akan Yanda Zaku Fara Aiki da Binance (Registration)
A matsayin sabon shiga a Binance, cikin sauqi kabi wadannan matakan daya bayan daya domin yin rijista. Domin fara rijista kuma, danna nan.

Matakai:

Bayan ka bude link din, zaka ga “sign up with phone or Email”, a nan kana da daman zabi ko kayi rijista da phone number ko kuma da email address. Dannan nan in baka fara ba ka fara yanzu. Lura da wannan hoton.

Hoto daga Mai Rubutu


2. Zaba daga cikin phone number ko email address wanda zaku bude Binance account dashi se ku cika Kaman yanda kuke gani a wannan hoton. Kada ku manta ku zaba password me karfi Kaman yanda kuka ga mun gwada a wannan hoton. Daga nan se ka yarda da tsare-tsaren Binance sannan ka cigaba. Referral ID 75142476



3. A nan za’a bukaceku da ku tabbatar da cewa kai/ke mutum ne ba robot ba. Cikin sauki kawai kaja wannan zanen zuwa cikin inuwar sa Kaman yanda kuke gani a wannan hoton


Hoto daga Mai Rubutu

4. A nan za’a turo maka confirmation code me 6 digits ta phone number ko email da kukayi amfani dashi wajen fara rijista. Dakko code din kusa shi a gidan sa sannan ku cigaba Kaman dai yanda kuke gani a hotonnan. Idan aka sama matsalar rashin samun code din to ku sake danna “Get code” ko “Resend code”. Idan kuma har yanzu beyi ba to ku gwada goge wasu messages din a inbox dinku domin wani lokachin yana cika kuma cikan sa kan iya hana mutum samun sabon sako (message).


Hoto daga Mai Rubutu

5. Daga nan ka isa samun Binance account dinka. Sedai bazaka iya fara amfani dashi yanda ya kamata har se ka/kin yi KYC verification. Domin yin verification, kawai ku dannan “Verify” Kaman yanda kuke gani a hotonnan


Hoto daga Mai Rubutu

6. Zaba kasar da kake (Country)


Hoto daga Mai Rubutu
7. Ku cika cikakken suna a nan tamkar yanda yake a banki ko National ID card. Duk wanda kayi amfani dashi to dashi zakayi identity verification. A tabbatar da First name, last name, middle name (idan akwai. Idan kuma babu to se a barshi kawai) da kuma date of birth daidai da na banki ko National ID card.


Hoto daga Mai Rubutu

8. Saka address da sunan city ko state da kuma postal code (ku duba postal code dinku a Google in baku sani ba; tabbas zaku samu). Misali 730123.


Hoto daga Mai Rubutu

9. A nan za’a bukace ka da ka tabbatar da identity dinka. Zaba BVN (mafi sauri kenan) ko NIN. Nafi ganin saurin BVN. Kada ku damu ko kadan; Binance basa bari wani ya sama information dinku ko kadan. A tabbata an zaba kasa (county) kafin a cigaba


Hoto daga Mai Rubutu
10. Saka BVN dinka a nan (kar kuji koamai)


Hoto daga Mai Rubutu

11. Wannan shine mataki na karshe da za’a dauki fuskarka. Kaman yanda ka gani a wannan hoton. Kabi umarnin da screen ya baka. Idan ka shirya se ka dannan “continue”.


Hoto daga Mai Rubutu

Idan kuma ba’a baka daman yin Facial verification ba, kada ka/ki damu. Kawai shiga application din kiyi login da details din da kukayi rijista. Asa confirmation code se a cigaba.
Kuna shiga application din zasu kaiku dakansu zuwa wajen da zaku Karasa verification din. Duba login a nan Kaman yanda hotonnan ya nuna.


Hoto daga Mai Rubutu
Wannan rubutun ze iya zuwa, kawai danna “Okay” domin karasa verification din.


Hoto daga Mai Rubutu
Idan kuma be kaiku ba, to dannan nan Kaman yanda ka gani a wannan hoton sannan a dannan “unverified” se a cigaba

Hoto daga Mai Rubutu
12. Dannan start Verification domin karasawa


Hoto daga Mai Rubutu
13. Saka fuskarka ko fuskarki a daidai wannan hoton (a tabbata akwai isashshen haske) sannan abi umarnin da screen yake badawa. Ayi kaman yanda wannan cartoon din yayi. Ko bude baki ko girgiza kai a hankali; duk yanda yayi ko yace ayi, hakan za ayi. Daga nan an gama.

Hoto daga Mai Rubutu
Wannan shine mataki na karshe. Daga nan se a jira zuwa minti biyar, za’a sama message na “verification successful” ko “Verification Unsuccessful”. Idan ka wuce successfully, zaka iya fara aiki da account dinka kamar kowa.

Wannan shine karshen rubutuna a nan, zuwa yanzu, na tabbata cewa kun san:

- Menene Binance?

- Me yasa zan fara amfani da Binance?

- Mataki-mataki kan yanda zaku fara aiki da Binance (Registration)

Da fatan zakuyi nasara a harkar cryptocurrency sannan kuma kun shiga Binance da sa’a.

Idan baka fara rijista ba, to dannan nan domin fara rijista. Idan kukayi rijista ta link dina to ina muku albishir da samun bonus har $300 domin biyan charges din trading sannan zaku sama amfani daban-daban a gaba. Godia.
 The Binancian


Post a Comment

0 Comments