NAMIJI MAI NEMAN MATA: Abubuwan Da Ke Sa Namiji Fadawa Neman Mata:


NAMIJI MAI NEMAN MATA: Abubuwan Da Ke Sa Namiji Fadawa Neman Mata:


1. Wasu mazan suna fadawa neman mata ne saboda sun auri ballagaza shashashar mace, wacce bata iya zaman aure ba, wacce bata iya kissa da tarairaya ba. Wacce bata san me rayuwar aure ya kunsa ba. Ita dai kawai gatanan ne.

Babu kwalliya wa maigida, babu shafa turaruka masu kamshi da gyara fata, bata shafa mai wanda zai sa fatar ta tayi laushi, bata gyara gashin kanta, bata iya kwanciyar aure ba, bata iya shagwaba mai fisgar hankali ba, bata iya nuna kauna da soyayya ga miji ba.

Bata iya zama tayi masahira domin ya nishadantu ba.

Bata iya magana ba, bata iya kallo ba. Ita dai gata nan ne kawai. Toh kun ga mijinta baya samun abin da ya kamata ya samu a wurinta, mai yayi saura? Sai yaje ya fara biye-biyen mata idan bayi da TSORON ALLAH. Kin ga kina daya daga cikin mutanen da suka bashi gudunmuwa wurin jefashi cikin wannan musiba ta neman mata.

2. Wani kuma yana fadawa neman mata ne saboda mabukaci ne dayawa, ita kuma matar bata iya jure masa, har ya kai ga duk lokacin da zai nemeta sai anyi rigima, toh a nan idan mijinki ya bukaci kara aure, kada ki hana shi, idan kuma kika yi masifa kika tayar masa da hankali toh zai kuwa fada neman mata, kina zaune zai kawo miki tsarabar HIV/AIDS har cikin dakinki. Don haka ki kyale shi yayi aurensa don wani baya iya hakuri da mace daya.

3. Wata kuma ta iya kwalliya da kissa, da tarairaiya, da abinci, da tsabta, ta iya kwanciya da komai, amma mijinta kuma manemin mata ne, to irin wainnan sai ace jarabawace, domin irin wainnan mazan ko mata dari za’a tara musu to ba zai hana idan sun ga wata su nema ba. Domin su basu dauki aure a bakin komai ba. Ki dagye sosai da rokon Allah, sannan kada ki fasa abin da kike masa na kyautatawa, ki cigaba, da izinin Allah zai dai na wata rana.

Sannan ki rinka kokarin nuna masa illan yin hakan, misali: Kice wane Idan ni kadai bana isan kane to ni babu damuwa ka karo wata, saboda ina ji maka tsoron cuta, kuma ina jiye maka tsoron kada abin da kayi ma ‘ya’yan wasu ayi ma naka.

Magana zaki yi masa cikin nutsuwa da ladabi, a kuma lokacin da kika ga ya cancanta. Ki rinka yi masa magana cikin nutsuwa da sanyin murya. Kada ki nuna masa kina fushi, kada ki nuna bacin rai. In ma zaki yi kada ya wuce kina magana kina zubar masa da kwallah na nuna bakin ciki da damuwa. Idan kina masa haka, kuma kina ribanya abubuwan da kike masa na kyautatawa. Da izinin Allah zai dai na.

Sannan Addu’a, shi zaki dagye da yi, babu dare babu rana, In Allah yarda za a wayi gari ya dai na ya dawo gareki.

Maza kuji tsoron Allah ku dai na shiga hurumin da ba naku ba, zina haramunce har ranar alkiyama, ka tausayawa kanka da matar ka, sannan ka tausayawa zuri’arka, kada su taso a neme su, a lalata maka rayuwarsu. Na tabbatar ba zaka so ba.

Allah ya kubutar da maza masu fama da wannan matsala.

 Sadeeya Lawal Abubakar.

Post a Comment

0 Comments