#tsangayarnalam
SHARE 🥇
Sau tari, maza magidanta sukan yi wasu abubuwan da matansu suka tsana ko suke ƙi a yayin da suke gudanar da jima'i dasu, sai dai kuma kadan ne daga cikin matan sukan iya fitowa fili su nunawa mazajen nasu rashin
jin dadinsu ga irin wadannan dabi'on ko Halayen.
Ire-ire waɗannan halayen na wasu mazan yakan kuntatawa mata, hakan kuma yakan yi sanadiyar rashin samar masu da gamsuwa a lokuta da dama yayi gudanar da
jima'i da mazajensu.
Ga jerin wasu abubuwan 10 da mata suka tsana kamin, lokaci da kuma bayan kammala jima'i.
1-Rashin Tsafta- Wasu mazan basu iya tsaftace jikinsu kamin su Tinkari matansu da jima'i. Ana samun wasu mazanma a lokacin da suka shiga wankasu na jima'i, basa kula da mahimman wuraren da ya kamata su tsaftacesu da kyau ganin mahimmancin su a lokacin gudanar da jima'i.
Wurare irin su baki, hamata, matsaimatsi, da kuma 'ya'yan marina, wurarene da mata suke matukar son ji da ganinsu a tsaftace a duk lokacin da mazansu suka tinkaro su a jima'ince. Don haka rashin
tsaftacesu, yakan hana mace samun jindadi kamin da kuma lokacin gudanar da jima'i.
2-Wasanni Motsa Sha'awa- Wasu mazan sam basu da al'adar motsawa matansu sha'awarsu ta jima'i ta hanyar wasannin motsa sha'awa, yadda
zai sa mace sha'awarta ya motsu sosai ta kuma ji ta kamu da bukatar mijinta. Mata da dama sun koka ta yadda mazansu da sun tashi gudana da jima'i dasu sai dai kawai su musu hawan kawara ba tare da motsa musu sha'awa ba, wanda hakan yasa mata da suke fuskantar irin wannan matsalar suke tsanar yin jima'i a lokuta da dama.
Mata suna sha'awar ayi musu wasanni da dama kamin a soma gudanar da jima'i dasu.
3-Rashin Maida Hankali- Mata sun tsani a lokacin da za a soma ko ake jima'i dasu hankalin namiji ya koma wani wajen. Mace na bukatar ganin mijinta ya tattara hankalinsa gaba daya a kanta kamin, lokacin ko bayan kammala jima'i da ita. Don haka ne mata suka tsani namiji yana amsa waya ko kallon talabijin, ko kuma yin wani batun da bashi da
alaka da abunda suke gudanarwa a wannan lokacin. Dole muddin namiji yana son ganin ya gamsar da matarsa, to ya maida hankalinsa gaba daya a kanta a yayin da yake tare da ita.
4-Lokacin Yin Jima'i- Kashi 80 cikin 100 na mata sunfi sha'awar a yi jima'i dasu ne a lokacin da suke da sha'awar yi ba a lokacin da basu da sha'awa ba. Mata sun tsani namiji ya tilastasu yin jima'i ba tare da sune da bukatar shi ba a wannan lokacin. Don haka yana da kyau maza suyi la'akari da lokacin da mace take sha'awar yin jima'i da kanta, domin ta hakan ne maigida zai iya samun biyan bukatar da za'a
sakar masa jiki sosai. Saboda a akwai wasu lokutan da mace batada sha'awar jima'i a rayuwanta.
5-Yanayin Kwanciya- Duk mace tana son mijinta ya saduda ita da yanayin da yafi mata dadi da kuma saukin gamsar da it. Mata sun tsani mazajensu su kwanta dasu a yanayin da basu jin dadinsa wanda ko yanayin dake wahalar dasu, hakan yake sa mace ta tsani gudanar da jima'i ko kuma ta kasa samun gamsuwa. Don haka yana da kyau maza su kula kuma suyi la'akari da yanayin kwanciyar da mace ta tsana da kuma wanda tafi sha'awa a yayin jima'i.
6- Sauke nauyinka a kanta- Maza musamman masu nauyin jiki, sukan cutar da matansu a lokacin da suka sauke nauyinsu akansu a yayin gudanar da jima'i. hakan na hana macen ta samu sararin gudanar da jikinta yadda
take bukata, wanda yanayin yana matukar cutar da ita. Don haka mazan da suke da girman jiki kuma suke saduwa ta yanayin kwanciyar rigingine, dole ne su kaucewa sauke nauyinsu akan ruwan cikin matansu.
7- Saurin Zuwan kai- Dukkannin mata sun tsani mazansu suyi zuwan kai da wuri a yayin gudanar da jima'i, wanda hakan yana matukar cutar da mace a rauyuwar, don haka wasu matan suka gwammace zama da rashin jima'i maimakon yin jima'in da namiji mai saurin zuwa ba zai gamsar da su ba. Dole ne maza masu irin wannan matsalar suyi kokarin samo maganinsa ko kuma su koyi yadda namiji zai iya jima'i ba tare da yayi zuwan kai da wuri ba.
8- Yin Shuru- Mata suna son jin namiji yana sumbatu a lokacin da yake saduwa dasu, yana basu wani labarin da bashi ne ba, yana kiran sunanta tare da kambama ta da furta mata kalamai na soyayya da zuga irin ni'imar ta da Allah yayi mata. Amma ba yayi gum da bakinsa kamar yana cin kashi ba.
9- Zarewa Bayan Gamsuwa- Wasu mazan tsabar rashin imani suna gamsuwa zasu zare azzakarinsu cikin mace ba tare da ita ta samu gamsuwa ba. Wannan ɗabi'ar babban illa ne ga duk wata mace. Dole ne namiji ya tabbatar da cewa kamin ya cire azzakarin sa a farjin matarsa da sunan ya kammala jima'i to ya tabbatar ita ma ta samu gamsuwa.
10-Runguma Bayan Kammala Jima'i - Akwai wasu mazan da zaran sun biya bukatarsu kawai sai su tashi su bar mace a kwance ita kadai. Wannan ba daidai bane. Duk mace nason bayan kammala jima’i da mijinta ya rungume ta yana shafa ta yana mata kalamai na soyayya tare da yi mata godiya ganin yadda ta biya masa bukatarsa ta hanyar halas. Hakan ya kamata miji ya yiwa matarsa har sai barci ya dauke su tana jin dumin jikinsa amma ba yayi wuf ya tashi daga kammala jima'i ba.
Wadannan sune wasu daga cikin abubuwan da mata suka tsana a lokutan jima'i. Da fatan maza magidanta zasu gyara.
A darasi na gaba zamu kawo abubuwan da maza suma suka tsana a lokacin jima'i da suka kamata mata su ki yaye su.
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
Message Sirrin rike miji on WhatsApp. https://wa.me/2348066627317
https://t.me/sirrinrikemij
EMAIL:
sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: +2348037538596
https://www.tiktok.com/@sirrin_rike_miji?_t=8dJpiRCaT7W&_r=1
0 Comments